← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce"To ai haƙuri za ki yi, wanda ya tashi nema ai ba ya duba nisa Maryam, ni ma zan yi kewarki kuma na akwai masu tafiya su yi wata bakwai, ko shekara bakwai, to ina laifi don na yi kwana bakwai?"

Ta ce"Haka ne, shi kenan Allah Ya kai ka lafiya, ya dawo mini da kai lafiya, Allah Ya ba da abin da aka je nema".

Ya ce"Amin mace ta gari, ko kefa! Amma da kin tsaya kina wani tantama? Gobe da yamma za mu tafi, saboda haka yau kam duk rowarki sai kin bar min daren nan duka, kya dinga tunawa da ni ko?"

Ta ce"Kai ai aikinka kenan, na rasa me kake ji, ni dama tun can babu wannan abun a aure da na ji daÉ—ina" Ta juya kai gefe

Ya ce"Maryam kenan, ke dai na rasa irin tunaninki wallahi, nan gaba za ki saba dai, ina ga sai kin haihu ko?" Ba ta ce komai ba, ta tashi ta kwashe kwanukan da suka ci abinci. Kafin ya shigo É—aki ta yi luf kamar mai bacci, saboda fargabar furucinsa ta kasa baccin ma, ya yi abin da zai yi ya kwanta, yana kai hannu jikinta, ta ce"Na fa fara bacci, ga ciwon kai".

Ya matsa gefe, don dama ba wai buƙatarta yake yi ba, kawai dai don ta sake yarda da tafiyar tashi ce, shi da zai je ya ɓarje guminsa a gidan Hajiya har ya tsaya ana kace-nace da shi? Daga haka ya juya ya fara baccinsa hankali kwance, har zumuɗin zuwan goben yake yi.

Washegari bai fita aiki ba, da kanta ta haÉ—a masa kaya a jaka, har ta ce ya siyo fulawa ta yi masa cincin ya ce a'a ta bar shi, tun da kanta yana ciwo, tun azhar Hajiya ta yi masa tex É—in tana ta jira, ya ce mata sai da yamma, ana idar da sallar la'asar ya É—auki jaka yana yi wa Maryam marayan kallo saboda yaudara, sai ya ga ta tashi ta saka hijjabi, ya ce"A ina zuwa kuma?"

Ta ce"Ai ya kamata na raka ka tasha ko?"

Ya ce"Haba Maryam wace tasha kuma? Mu da za mu haɗa da yawanmu a ƙasan layi sannan mu ɗunguma zuwa tasha, kuma tsakani da Allah sai a ce ni ne kaɗai matata ta rako ni?"

Ta ce"To mene ne idan ma an faÉ—a?"

Ya ce"A'a wallahi ni dai ina kishin a gane mini kyakkyawar matata, duk sallamar da za mu yi mu yi ta a iya zaure, kwana bakwai ne fa, kamar yau ne, yi haƙuri kin ji?"

Haka dai ya lallaɓata ya tafi, bai samu nutsuwa ba sai da ya gan shi a gidan Hajiya, sosai take farin ciki da zuwansa, jinta take tamkar wacce ta yi sabon aure, ɗakin mijinta ta buɗe ta kai kayansa ciki, ta faɗa masa nan ne masaukinsa, tun kafin ya zo ta sallami ƴar aikinta, ta ce mata tafiya za ta yi, sai bayan sati ɗaya idan ta dawo za ta neme ta, saboda haka da kanta ta yi masa girki sakwara da haɗaɗɗiyar miyar da ta zuba yajin maza a ciki ta yi lafiyayyen kunun aya shi ma ta watsa masa ƙwayoyi, Aliyyu ya kwashi abinci ya yi wanka, suka fara shagalinsu, bayan ya kashe wayarsa.

Bai kunnata ba sai washegari shi ma sai azhar, don sosai ya kwashi ramuwar bacci da safe, ya kira Maryam suka gaisa yake faÉ—a mata yanzun nan suka sauka, ta ce"Alhamdulillah! Tafiya ta yi kyau, ina ta tunani wayarka na kikkira a kashe ashe sai yanzu kuka je, amma dai da nisa".

Ya ce"Ke dai bari Love, kwana muka yi a hanya, ana sharara gudu, sai yanzu muka isa".

Ta ce"Ma sha Allah! Da daddare za mu yi chart".

Hajiya dake zaune tana jin duk wayar tasu, ta kaɗa masa ɗan yatsa alamar a'a, tana maƙe kafaɗa kamar yarinya. Ya ce"Ai Maryam chart dai yau ba zai yiwu ba, jiya fa ban yi bacci ba, yanzu caji zan bada wayata, a kaimu mu ga yanayin aikin, sai mu ci abinci a kaimu masauki, kin ga ina yin wanka sai bacci, tun da gobe sassafe za mu tafi wurin aikin".

Cike da tausayawa ta ce"To Allah Ya tsare ku, Ya ba da sa'a Love ka kula da kanka sosai don Allah, ban da kai wa dare a waje ka ga dai ba ka san kowa ba".

Ya ce"Haba ina ma na ga wannan damar? Mu da za mu wuni aiki, ai ina dawowa sai bacci, ke ma sai dai ki yi haƙuri ba za mu dinga doguwar waya ba".

Daga haka suka yi sallama, ya kalli Hajiya yana washe baki, ta juya kai ta ce"Ina kishi da wannan matar taka gaskiya".

Ya ce"A haba Hajiya, ai kin wuce ki yi kishi da Maryam".

Ta ce"Ba ni labarinta, tana sonka sosai ko?"

Kamar ta yi masa allurar tonon silili haka ya ɓarke ya fara ba ta labarin Maryam, hatta gidan iyayenta da yadda suka fara soyayya zuwa aurensu, da sana'ar da take yi, duk sai da ya faɗa mata, sannan daga baya ta nemi sanin unguwar da yake haya, ya kwatanta mata tsaf.

Haka rayuwa take gudana tsakanin Hajiya da Aliyyunta, suna ɓarje soyayya, Ali sai dai a ci a sha a kwanta a yi bacci, daga shi sai gajeren wando za ka gan shi a falo yana kallon TV, AC tana ratsa shi, ya shiga kitchen ya yi ciye-ciyensa son ransa, kullum ya ji alert ɗin dubu goma.

Kwanansa biyar a gidan, Hajiya ta ce masa za ta je unguwa, tun da ya zo bai ga ta fita ba sai yau, tana yin baƙi, idan za su zo sai dai ta ya shige ɗakinsa ya yi kwanciyarsa. Kai tsaye Hajiya ta bi kwatancen da ya yi mata, ta je har gidan Maryam, a buɗe ta tarar da gidan, ta yi sallama ta shiga, ta tarar da mata guda biyu suna fira, wanda kwarjinin Hajiyar ya sa suka yi zaton wata babbar baƙuwa ta yi, suka yi wa Maryam sallama suka tafi, Maryam ta tashi tana yi mata sannu da zuwa, Hajiya ta ja kujera ƴar tsuguno ta zauna ta ce"Yawwa Maryam, dama kitso na zo ko zan samu?"

Ta ce"Za ki samu, bari na ɗakko tabarma". Ta shiga ɗaki, Hajiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo, ta fito ta shimfiɗa hannunta riƙe da kibiya ta ce"Bisimillah".

Hajiya ta zauna a tabarma, Maryam ta fara yi mata kitso, tana ji ta É—akko wayarta ta yi kira, ta ji tana cewa"Ali na samu gidan Maryam É—in, ga shi nan ma har ta fara yi mini kitson". Can kuma ta ce"A babu komai wallahi, tana da kirki, bari dai idan na zo gidan ma yi magana".

Maryam ta É—an yi mamaki jin irin sunan mijinta kuma da alama mai sunan ne ya kwatanta mata har ta zo kitson, ba ta kawo komai ba har ta gama yi mata, Hajiya ta É—auki dubu biyu ta bata, Maryam ta ce"Ai baiwar Allah bai kai haka ba, ungo kuÉ—inki har dubu biyu?"

Hajiya ta ce"Haba ai yiwa kaine, ke da Ali ai duk É—aya kuke a wajena".

Cak Maryam ta tsaya ta ce"Wai wane Alin?"

Ta ce"Ba sunan mijinki Ali ba, wanda ya yi miki ƙaryar ya tafi Enugu aikin kamfani? To idan ya dawo ki faɗa masa Hajiya Zuwaira tana gaishe shi".

Daga haka ta fice tana murmushi, ta bar Maryam wacce mamaki ya daskarar da ita.

Shi kuwa Ali yana falo ya yi ɗai-ɗai yana kallo a TV, lokaci-lokaci yana damƙar dambun nama yana ci, ya ga an buɗe ƙofa, da sauri ya miƙe tsaye ganin wani mutumi ne ya shigo ba Hajiya ba, kallon-kallo suka shiga yi da mutum, kafin Ali ya kwasa a guje ya yi hanyar ɗakinsa, mutumin ya bi sa ya guje yana cewa"Waye kai!?" Ali ya murɗa key zuciyarsa tana bugawa da mugun ƙarfi, ga shi ya bar wayarsa a falo.

GIDAN SADIQ

Yau ta kasance Asabar Yusra tana gida, don haka Kursum ba za ta zo ba, bayan ta gama duk ayyukan gida ta kwanta tana bacci, har ta makara sai da aka fara kiraye-kirayen sallah ta farka, ta fito ta ɗora girki, tana gamawa ta zubawa yara, suna yin cokali ɗaya suka kalli juna, Afna ta ce"Ni dai Momy na ƙoshi"

Fanan kuma ta ce"Momy me yasa abincin Anti Kursum ya fi yin daÉ—i?"

Da mamaki Yusra take kallonsu, ta ja abincin ta yi cokali É—aya ta ji babu wata matsala, ta ce"Ita na Anti Kursum ba irin wannan ba ne?"

Afna ta ce"Nata ya fi daÉ—i, kuma da wuri take gama yi mana, ta ba mu a baki".

Yusra kanta ya kulle tana kallon abincin ta ce"Mene ne bambancinsu?"

"Yara ma suka gane ballantana ke? Haba Yusra yanzu za ki ce duk tsawon lokacin nan ba ki gane canjin É—anÉ—anon abinci da aka samu ba a gidan nan sanadin Kursum?" Sadiq ya faÉ—a wanda ba su san da shigowarsa ba

Cak ta tsaya tana kallonsa da auna maganganunsa, ya ce"Wannan ba wani abun mamaki ba ne, kin san an ce dama kowa da irin hannunsa, ni ɗakko min abincina na koma, yunwa ce ta dawo da ni, Kursum kafin sha biyu take kai min abincina har na saba da ci da wuri, ke kuwa sai ƙarfe biyu, duk yunwa ta gama cinye mutum".

Ai Yusra ji ta yi kamar an zare mata laka saboda tsananin mamaki, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ga ya shiga kitchen ya ɗakko abincin ya zauna zai fara ci, ta tashi ta je ta tankwaɓe cokalin hannunsa abincin da ya ɗibo ya zube, ya ɗago yana yi mata kallon mamaki, ta ce"Abincin da babu daɗi za ka ci? Ai sai ka jira Kursum ɗin ta dafa maka! Wai da gaske ni kake faɗawa wata ta fi ni iya girki?"
Chapter 13 · 0% Book details