← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya katse ta da faɗin"Wallahi ba haka ba ne Maryam, wata yarinya ce take ta bi na a kwanakin nan ba na kula ta, to shi ne jiya ta bawa Hamza ya kawo min wannan kayan, kuma na san idan ma ban karɓa ba wallahi ba zai mayar ba, kuma zuwa zai yi ya ce mata na karɓa, shi yasa kawai na karɓa ɗin, to da yake na san ba za ki ji daɗi ba shi ne na ɓoye saboda kar ki gani, amma ba wai manufata na yi miki rowa ba wallahi".

Maryam ta yi murmushin takaici ta ce"To mene ne abun ɓoyewa? Kenan jiyan a wurinta kake har sha ɗaya ko?"

Ya yi saurin girgiza kai ya ce"Wallahi ban taɓa kula ta ba ma, ba faɗa miki ai aiki na tsaya, kuma tun da zai kawo mana matsala na daina, ba ga shi yau na dawo da wuri ba?"

Ta ce"To shi kenan magana ta wuce".

GIDAN SADIQ

Sanda Sadiq ya gama uzurinsa ya je zai kwanta, sai ya same ta zaune a kan gadon, yana shiga ta sakko ta fice daga É—akin, har bacci ya fara fizgarsa ba ta shigo ba, hakan ya sa ya fito don ya lallashe ta, a falo ya tarar da ita kamar yadda ya yi zato, saboda halinta idan suka yi faÉ—a ta ce za ta kwana a falo, zama ya yi a gefen kujerar da take kwance, yana shafa kanta ya ce"Yusra!".

Ta juya masa baya, ya juyo da ita ya ce"Ni fa ban ce miki zan yi wani auren nan kusa ba".

Ta ce"To me yasa ka hana ni samo Æ´ar aikin?"

"To ki samo mai hankali" Ta ji furucinsa a bazata.

"Da gaske?" Ta tambaye shi tana jin daÉ—i sosai.

Ya ce"Da gaske mana, ba shi ne dalilin fushin ba?"

A gabansa ta É—auki waya ta kira Sumayya ta faÉ—a mata ya amince da É—aukar Æ´ar aikin, cikin jin daÉ—i ta ce mata gobe za ta kawo mata ita har gida. Sai ga Yusra ta ware har tana yi masa firar yadda za ta kasance da Æ´ar aikin, suka kwanta tana cike da farin ciki.

Washegari da kuzarinta ta gama komai na gidan, shi kuma ya tafi shago, ƙarfe tara Sumayya ta shigo gidan tare da wata buduruwa, Yusra ta tare su da murna, suka gaisa tana kallon yarinyar da take a nutse daga gani ba ta da hayaniya, Sumayya ta ce"To ga Kursum nan na kawo miki, ban fiya yabon wani ba, amma ina da tabbacin za ki ji daɗin zama da ita, ba ta da gandar aiki, kuma tana da hankali".

Yusra ta ce"Ai na lura da hakan, ke dai Allah Ya saka ƙawata".

Sumayya ta ce"To ya kika tsara yanayin aikin, a nan za ta zauna duka ko zuwa za ta dinga yi tana tafiya?"

Yusra ta ce"Idan ta gama aikinta za ta jira na dawo gidan sannan na tafi, ranar da nake aikin kwana kuma za ta kwana a nan, ta kula da yaran ko dan saboda tashin sassafe ta shirya su su tafi makaranta".

Nan Sumayya ta faɗa mata unguwar da gidan su Kursum yake, sannan ta ɗora da faɗin"Kursum ki yi abin da ya kawo ki shi kaɗai, ki kular mata da yaranta ki rungume su hannu biyu-biyu, sannan idan za ki yi girki ban da almubazzaranci, magana ta ƙarshe babu ruwanki da mijinta! Gaisuwa ce kaɗai za ta haɗa ku, idan kin yi girki ki ajiye a dining, yana dawowa ki shige ɗakin yara a nan za ki na kwana, kar ki sake ki fito babu hijjabi ko mayafi idan yana gida, kin dai ji ko!?" Ta ƙarasa tana ƙanƙance ido alamar gargaɗi sosai.

Kursum ta ce"In sha Allah zan kiyaye komai".

Yusra cikin jin daɗi ta ce"Na gode sosai ƙawata".

Sannan ta ce"Yau babu aikin komai, tun da ina gida, sai dai gobe ki zo da safe, zan bar miki mukulli a wurin mijina, sai ki dinga zuwa kina karɓa a shagon, kin ga gobe aikin safe zan yi, to kafin ki zo mun fita dukanmu, idan kin karɓo mukulli sai ki yi wanke-wanke ki gyara ko'ina, kafin sha biyu ki yi girki idan yara sun dawo su ci ki shirya su su tafi islamiyya, shi ma ki zuba ki kai masa nasa, sai ki zauna a gidan, wajan ƙarfe uku zan dawo kin ga sai ki tafi ko?"

Kursum ta jinjina kai ta ce"In sha Allah babu matsala".

Suka yi mata sallama suka tafi, a hanya Sumayya ta ce"Don Allah Kursum kar ki ba ni kunya, na faɗa miki kuɗin da zan biya ki idan aikin nan ya yi kyau, ki kwantar mata da kai, shi kuma ki san ta inda za ki ɓullo masa".

Kursum ta yi murmushi ta ce"Ni fa dama can yana burge ni wallahi, ballantana kuma za mu rayu a inuwa ɗaya? Hmm Allah Ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi ɓarna".

Sumayya ta ce"Allah Ya shi miki albarka Kursum, idan komai ya tafi daidai, wallahi sai na yi wata shida muna raba daidan albashina da ke".

Kursum ta kwashe da dariya cike da farin ciki, ta ce"Riba biyu inji sauro".
[2/17, 10:30 AM] Sadiya abdulrazak: PAGE 5

Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

GIDAN HARUNA

A ranar tun tsakar dare zazzaɓi ya rufe Halima, dama tun da rana take ciwon kai, ta kasa bacci, sai gabannin asuba ya ɗauke ta, amma da alarm ɗinta ya buga haka ta daure ta tashi ta yi sallah, sai dai ta kasa komai ta kwanta a sallayar tana ta rawar sanyi, yayinda Haruna yake ta baccinsa bai san halin da take ciki ba. Zainab ganin har bakwai ta wuce Halima ba ta fito ba, ya sa ta ƙarasa ƙofar ɗakinta tana sallama, ta amsa mata da ƙyar tana tashi zaune ta ce"Zainab".

Zainab ta buÉ—e labulen, ta ce"Halima yau lafiya kuwa ba ki fito ba?"

Halima ta ce"Wallahi ba ni da lafiya, zazzaɓi da ciwon kai tun jiya, yau ba zan iya ba ma".

Zainab ta ce"Ai kuwa babu daÉ—i a zo nema a ga ba ki yi ba, yau É—aya da sai na yi miki".

Halima ta ce"Za ki iya kuwa Zainab? Kar ki wahalar da kanki".

Ta ce"Haba wace wahala, ɗakko min kayan, bari na haɗa wuta". Ta fita tana kunna mangal, ita kuma Halima ta tashi ta ɗakko mata kayan wainar, Zainab ta dawo hannunta ɗauke da kofin kunu ta miƙa mata, har da paracitamol ta ce ta sha kafin a kaita asibiti, ta yi mata godiya, ita kuma ta koma ta fara aikinta.

Wajan ƙarfe tara Haruna ya tashi daga bacci, turus ya yi ganinta kwance a daidai wannan lokacin, ya fice don shiga banɗaki, sai dai ya tsaya ganin Zainab a bakin murhu tana ta fifita wutar wake da shinkafa, don har an fita da waina, jikinta ne ya ba ta ana kallonta, ta ɗago ta kalle shi, ta yi masa farr da ido, ƙasa-ƙasa ya ce"Ke dai kina son wahalar da kanki, ki yi ta taya matar nan aiki".

A hankali ta ƙaraso kusa da shi ta ce"Kai ka tattarata ka kai ta gida ta yi jinya, ka ga mun samu ɗaki kafin ta dawo".

Zai yi magana kenan Baaba ta fito daga ɗaki don ta duba jikin Halima, suka waske ya wuce banɗaki, a ransa yana ta tunanin maganar Zainab, domin tabbas shawararta abar dubawa ce, saboda haka yana komawa ɗaki ya tambayi Halima kwanciyar me take yi, ta faɗa masa yanayin jikinta, ya ce"Allah Ya sawaƙe, to ina abun karyawata?"

Ta ce"Ban fita ba fa yau kwata-kwata".

Ya ce"Kuma don ba ki da lafiya ba zan ci abinci ba kenan?"

Takaici ya kamata, tana tabbatarwa kanta lallai Haruna ba miji ba ne, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ji muryarsa ya ce"Daurewa fa za ki yi ki dafa min taliyar nan".

"To!" Ta amsa tana tashi zaune, ta huta na sakanni sannan ta fita ta kunna mangal ta ɗora. Tana fita ya kira lambar Zainab, tana ɗagawa ya ce"Na koro ta ta min girki, kar ki taya ta, ni abincin ma ban so kika karɓar mata ba, idan ta ji wahala za ta nemi zuwa gidan da kanta". Zainab ta yi dariya suka kashe wayar, tana leƙen Halima ta gefen labule.

Zama ta yi a bakin wutar bayan ta haɗa komai na jollop ta ɗora, ruwan yana tafasa ƙamshin ya daki hancinta, nan take cikinta ya fara rugugi, yawu ya taru a bakinta da gudu ta ƙarasa bakin makwarara ta fara kwara amai babu ƙaƙƙautawa, Zainab ta yi kamar ba ta ji ta ba, haka shi ma Haruna, sai Baaba ce da ta ji abun ya ƙi ƙarewa ta fita tana cewa"Subhallah! Sannu Halima, har da amai?"
Chapter 7 · 0% Book details