← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya yi kwana uku bai je gidan Hajiya ba, duk yadda take kiransa kuwa, saboda ba ya so su sake samun matsala da Maryam kwana kusa, yanzu ana yin sallar magriba yake dawowa gida, kwana uku bai yi zaman majalisarsu ba, sai dai a ganin Maryam an gudu ne ba a tsira ba, tun da kullum sai Hamza ya biyo shi gidan, su zauna a ƙofar gida sai su kai ƙarfe tara, ganin an jera kwana uku a haka ya sa ta fara yi masa ƙorafi, ta ce gaskiya Hamza ya daina zuwa yana hanata fira da mijinta, Ali ya ce shi dai mutum ba zai zo wurinsa ba ya kore shi, watarana Hamza ya zo, Maryam ta tashi ta tare hanya tana haɗe gira, da mamaki Ali ya ce"Maryam mene ne hakan? Ba ni hanya don Allah"

Ta ce"Babu inda za ka fita, ka faɗa masa kana buƙatar ganawa da matarka shi ma ya tafi wurin tasa matar".

Ali ya ce"To ai shi yanzi ya saki matarsa, shiyasa idan ya koma gida da wuri sai daren ya yi masa tsayi, kuma kin ga nine dai abokin, dole wurina zai zo, na ga nan a ƙofar gida ne kina leƙowa ma za ki ganmu".

Ta ce"Idan na ganku zan jiyo irin huÉ—ubar da yake yi maka ne? Wato ya saki matarsa kai ma yana yi maka huÉ—ubar ka saki taka ku zama É—aya ko?"

Ali ya ce"Subhanallah! Haba Maryam wannan wace irin magana ce?"

Ta ce"To ni dai ban amince da wannan sabuwar majalisar ba, saboda haka ka faÉ—a masa ya daina zuwa ba ka so!".

Ali ya ce"Wallahi ba zan iya korar shi ba".

Ta ce"To wannan abokin naka ya zama kishiyata, saboda haka daga yau ka fara raba mana kwana, ranar kwanana ana magriba ka dawo gida, ranar kwanan shi ana magriba za ka dawo ka tarar da tabarma a ƙofar gida, don ba zan iya ba!".

Cikin takaici Ali ya ce"Wai me yasa kike haka ne? GabaÉ—aya kin kanainaye ni, sai ka ce ke ce mijin, na faÉ—a miki shi kaÉ—ai ne a gidan shi ya saki..."

"Ya je ya hau sallaya ya fuskanci alƙibla!" Ta katse shi har da ɗaga murya.

Ya juya zai fita, ta ruƙo rigarsa ta dawo da shi, ya ce"Maryam wai mene haka?"

Ta ce"Da gaske fa nake wallahi, ka bari ni na je na same shi na faɗa masa ina buƙatar mijina a kusa da ni".

Ganin ta shiga ta ɗaki ta ɗakko hijjabi Ali ya ce"Bari na je na faɗa masa". Ya fita, bai jima ba ya dawo yana ɓata rai, har lokacin tana tsaye da hijjabin a hannu, ya ce"To ga ni sai ki kwaɗa ki cinye.

Ta yi dariya ta ce"Ni da ana kwaÉ—on ma ai da tuni na cinyeka na huta da matsalolin da kake tara mini".

Daga haka suka shiga É—aki, har ta kunna kallo ya kashe yana cewa"Wucewa za ki yi mu je mu kwanta, ai tun da kin hana ni fita dole ki rage mini daren".

Nan take fara'arta ta É—auke, ta ce"Ni fa tun rana nake jin kasala da ciwon kai, kitso ma yau mutum É—aya na yi wa".

Ya taɓe baki ya ce"Ai wallahi ko karkarwar zazzaɓi kike sai kin wuce mun tafi ɗaki, ai tun da kika kafa mini doka na yi miki sam'u wa ɗa'a ni ma dole ki bi tawa doka, ni wannan dokar ma ai gana ta kai ni gobarar Titi a Jos, babu zancen cewa kin fara bacci, idan da rabo ma sai ki ga cikin satin nan Allah Ya kawo mana babban rabo, kya samu ɗan tayin fira nan da wata tara ko?"

Ko kallonsa ba ta yi ba, ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, fargaba duk ta addabe ta, sai ta ji da ta sani ma ta bar shi da Hamzan, haka dai ta miƙa kai kamar ta yi kuka don takaici.

Kwana uku suna yin haka, Maryam gabaɗaya dauriyarta ta ƙare, saboda haka ta fara ƙaryar rashin lafiya, kafin ya dawo sai ta shige bargo ta ce zazzaɓi take yi. Ana haka ne kuma Hajiya ta dame shi da kira kan ya kamata ya zo ko awa ɗaya ne, to shi ma ya yi kewarta, kawai yana dannewa ne ganin yanzu yana yi wa Maryam fin ƙarfi, to da ya ga ta narke da zazzaɓin da ya san na ƙarya ne sai ya ƙyale ta, ya yanke shawarar zai je gidan Hajiyar yau.

Yana idar da sallar magriba ya kira Hajiya ya faɗa mata ga shi nan zuwa, ya kama hanya ya tafi, yau ma da kanta ta shigar da shi, kafin su ƙarasa ɗaki yake ƙara kallon gidan, ya ce"Hajiya wai duk girman gidan nan babu mai gadi ne?"

Ta ce"Akwai mai gadi, aikensa nake yi idan zan yi baƙo".

Ya ce"Kenan dai Hajiya akwai wasu baƙin bayan ni".

Ta ruƙo hannunsa a lokacin da suke ƙarasawa ta ce"Wallahi tun ranar da ka fara zuwa har yau na kasa sake kula wani, kai na musamman ne Aliyyu, ni fa da za ka dawo gidan nan da zama gabaɗaya wallahi zan so haka, kana ɗaki kawai a cikin AC, ka zaɓi abin da za a dafa maka ka ci ka kwanta, sannan kullum dubu goma".

Ya yi ƴar dariya ya ce"Kin ga kuwa da har ƙiba fa sai na yi".

Hajiya ta ce"A to! Ka dai duba wannan damar".

Ya sosa kai ya ce"Ai Hajiya matata nake tunani, kin san fa amarya ce ko haihuwar fari ba ta yi ba, kuma wallahi tsaye take a kaina, tana lura da duk wani motsina, shi yasa amma da ni ma zan so hakan wallahi".

Hajiya ta ce"To kai kuwa Aliyyu ya aka yi ka yi sake matarka take juya ka har haka? To me zai hana ka ce mata ka samu aiki a wani garin, sai ka zo mu yi zamanmu, duk kwana biyu ka dinga tura mata kuÉ—i ka kashe bakinta, ko ba zai yiwu ba?"

Aliyyu ya ce"Kuma fa kin kawo shawara Hajiya, zan yi tunani, ke zai yiwu ma in sha Allah!".

Ta ce"Ko kai fa, na gode, sosai nake sonka Aliyyu, ji nake kamar na kashe auren nan na aureka wallahi".

Ya yi murmushi ya ce"Habawa Hajiya wane kare da É—aukar gara? Wani kayan ai sai amale".

Daga haka ta kawo masa abinci ya ci, ya yi wanka, ya fara abin da ya kawo shi, ƙarfe tara ya baro gidan, yana ta sauri saboda Maryam, a hanya ya tsaya ya kira ta, tana ɗagawa ya ce"Maryam ki yi haƙuri ga ni nan zuwa".

Ba ta ce komai ba ta kashe, sai da ya tsaya a hanya ya siya mata kwakwa da dabino sannan ya ƙarasa gidan. Yana zuwa ya ganta fuskar nan kicin-kicin.

Ya yi murmushi ya ce"Hajiya Maryam kenan, uwargidana amaryata, sarautar mata daga ke babu ƙari..."

Ta ɗaga masa hannu ta ce"Don Allah dakata, ya isa haka, na san dai duk siyan baki ne kake yi, babu komai Ali duk yadda ka tsara rayuwarka ka je ka yi ta yi, ni dai Allah Ya sani na yi iya ƙoƙarina don na ga na kula da kai, tun da kana ganin kamar takura ne shi kenan, ka je ka yi".

Ya zauna, ya janyo ta jikinsa, yana cewa"Haba Love, wallahi ba takura ba ne ba, na sani ƙauna ce, kuma ina jin daɗin yadda kike kulawa da ni ɗin wallahi, yanayin aiki ne kawai, ga kwakwa na kawo miki, na san za ta wanke laifina ai ko?"

A zahiri shi take kallo, amma sam ba ta gane inda maganganunsa suka dosa, ta yi nisa a duniyar tunanin da zuciyarta ta ɗarsa mata, dalilin kusancin da suka samu, sakamakon zamanta a cinyarsa, wani kalar ƙamshi ta ji na wata shegiyar humra mai daɗin ƙamshi, kuma ta san Ali idan zai fita da safen nan ba ya wani fesa turare ma, ko ma yau ya fesa ai ba su da irin wannan turaren, kuma ma fa wannan humra ce, kamar ta yi masa magana, sai ta bar shi a kan za ta yi bincike kafin ta tuhume shi.

GIDAN SADIQ

Rayuwar gidan Sadiq ta samu ci gaba a nasu ganin shi da Yusra, yanzu hankalinta ya kwanta sosai, tsakaninta da Kursum sai godiya da fatan alkhairi, idan tana aikin kwana ko fargabar ta bar mijinta da wata a gida ba ta yi, domin ta yarda da su, su biyun, yayinda Kursum matakan da ta tanada don shayar da Yusra maÉ—aci suke ta tafiya hawa-hawa.

A yanzu dai ta riga da ta gama da Sadiq da yaransa wajen girki, ya yarda a kan Kursum ta fi Yusra iya girki, don sosai Sumayya ta kashe kuÉ—in wurin siya mata kayan É—anÉ—anon girki, wanda Yusra duk ba ta san wainar da ake toyawa ba, duk da Æ´aÆ´anta sun sha faÉ—a mata girkin Anti Kursum yana da daÉ—i sosai, ita ba ta kawo komai ba, tun da ba ta ji wani bambanci da nata ba. Abu É—aya ta sani Kursum tana taimakonta.

A ɓangaren Sadiq tsakaninsa da Kursum babu yabo, babu fallasa, kullum za su gaisa tana murmushin da ya gane ɗabi'arta ne, sai dai yadda ba ta gajiya da kwalliya abun yana burge shi, saboda shi mutum ne mai son kwalliya sosai, duk da bai taɓa faɗawa Yusra ba tun da ya lura ita ba ta da ra'ayin wannan zane-zanen, sai kuma tsafta da take da ita sosai abun yake burge shi, uwa-uba kuma yadda take kula masa da ƴaƴa, abun sha'awa, sun shaƙu da yaran sosai ba su da zance sai na Anti Kursum ɗinsu, saboda haka shi ma yanzu aikin Yusra ba sosai yake damun shi ba.

Sai dai wani baƙon lamari da yake faruwa da shi, wanda tun yana damunsa yanzu ya zame masa jiki, ta wani ɓangaren ma abun ɗebe kewa ne a gare shi.
Chapter 11 · 0% Book details