← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baaba ta koma ɗaki tana tsaki, wuf Haruna ya fito ya yi zaure da sauri, sannan Zainab ɗin ta fito, ta tarar da Baaba tana kokowa da wayar, don ba ta iya ɗagawa ba, ta karɓi wayarta Baaba ta koma banɗaki tana mita, ita kuma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, sosai take son Haruna don haka dole ta san yadda za su ɓullowa lamarin nan, ta riga ta saba da maza yanzu jinta take tamkar a keje, don tun da suka dawo gidan nan ba ta haɗu da wani namijin ba, kuma a satin da za su dawo ɗin aka cire mata cikin da wani saurayinta ya yi mata, dalilin hakan ne ma kakar tata ta ce a bata Zainab ɗin su bar unguwar, saboda kowa ya ji zancen zubar da cikin nata, ta san idan Zainab ta ci gaba da zama a unguwar ba lallai ƴan ba ni na iya su barta ta yi aure ba.

Shi kuwa Haruna sai da ya ji Baaba ta shiga banɗaki, sannan ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, tashin Halima ya yi ya ragewa kansa zafi, saboda Zainab ta gama kunna shi, daga nan bacci mai cike da nutsuwa ya kwashe shi, saɓanin Zainab.

GIDAN SADIQ

Washegari da damuwa Yusra ta tashi, idan ta tuna maganarsu ta jiya sai gabanta ya faɗi, sosai ta shiga tsoron kar Sadiq ya ƙara aure, tana da kishi sosai, ba ta jin za ta iya raba mijinta da wata macen, a yadda take ji indai ta tabbata Sadiq zai ƙara aure ita za ta iya haƙura da aurensa bakiɗaya ma, ta je ta yi wani auren ta rayu ko da babu ƴaƴanta a kusa da ita, muddin za ta rayu babu kishiya kuma ba za a hana ta aikinta ba ta amince, a sanyaye take yin komai har ta kammala abun karyawa ta kai dining ta jera, sai da ta yi wanka sannan ta tashi yaran daga bacci, kasancewar yau Asabar ce babu makarantar boko, ta yi musu wanka, da suka ƙaraso dining ɗin shi Sadiq har ya gama cin nashi abincin ya tashi, yana kallonta ya san tana cikin damuwa, sai ya ɗauka ko yanayi ne jikin da jini, tun da ya tashi ba su haɗu ba sai yanzu, don tana idar da sallah kafin ya dawo daga masallaci ta koma ɗakin yaranta ta kwanta.

"Zan fita, me za a kawo?" Ya tambaye ta yana yi mata kallon tsaf.

Hankalinta a kan abincin da take zubawa ta ce"Ba sai ka aiko komai ba, yau ina gida me za a dafa maka?"

Yana tafiya ya ce"Ki dafa zaɓinki kawai ya yi". Ya fita yana mamakin sauyinta, ko a dawo lafiya ba ta ce masa ba, ballantana ta raka shi, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin kau da abun.

Da rana bayan ta gama komai yara sun tafi islamiyya, ta kwanta tana ta tunanin wannan maganar tasa da take neman tarwatsa mata farin ciki, idan ta tuna za su rabu sai idonta ya ciko da ƙwalla, kanta ya kulle ta rasa abun yi, saboda haka ta kira Sister Sumayya a waya, babbar ƙawarta tun ƙuruciya, kuma abokiyar aikinta a yanzu, ba sa ɓoyewa juna sirri damuwar ɗaya ta ɗayar ce, bayan sun gaisa Sumayya ta ce"Sister na ji kamar akwai damuwa a muryarki, ba ki da lafiya ko daga bacci kika tashi?"

Yusra ta sauke ajiyar zuciya ta kwashe duk abin da yake damunta ta faÉ—a mata.

Sumayya ta yi murmushi ta ce"Haba ƙawata, ke daga wannan kawai sai ki yi zargin Sadiq zai iya ƙara aure?"

Yusra ta ce"Kamar ba ki san butulcin namiji ba?"

"Butulci?" Sumayya ta tambaya da mamaki, sannan ta É—ora da faÉ—in"Don zai yi abin da Allah Ya halatta masa sai ki kira shi da butulu? Haba Yusra ki dawo cikin hayyacinki...".

Ta katse ta da faɗin"Wallahi Sumayya ba zan zauna da kishiya ba, don haka zan ba shi zaɓi, ko ya sake ni ko ya manta da ana ƙara aure a duniya".

Cike da mamaki Sumayya ta ce"Da gaske duk son da kike yi wa Sadiq za ki iya rabuwa da shi saboda zai ƙara aure?"

Yusra ta ce"Ƙwarai kuwa, wannan abu ne mai sauƙi a wajena, saboda na tsani kishiya".

Sumayya ta yi makirin murmushi mai É—auke da manufofi da dama, wannan wata dama ce da ta jima tana neman hanyar samunta, domin kuwa ko maye ya manta uwar É—iya ba za ta manta, amma za ta biyo mata ta bayan gida, kuma daki-daki har ta cim ma burinta.

"Sister ya zan yi? Duk na damu". Yusra ta faÉ—a kamar za ta yi kuka.

Sumayya ta ce"Dole cikin uku a yi ɗaya, ko dai ki haƙura da aikinki kamar yadda yake so, ko kuma ki samo ƴar aiki wacce za ta dinga zama tana yi miki aikin gida, idan kina aikin kwana ta kwana da yara ko kuma ki haƙura ya ƙara auren".

Yusra ta yi shiru na sakanni tana nazari, sannan ta ce"Ba zan iya ajiye aikina ba fa, zan gwada yi masa zancen Æ´ar aikin dai ko zai amince".

Sumayya ta ce"Idan ya amince sai ki yi min magana, zan samo miki mai hankali da nutsuwa, kin dai ƙi kishiyar ko? Ni ba ga shi ita ce take kula da ƴaƴan ba idan ba na nan?"

Yusra ta taɓe baki ta ce"Zuciyarmu ba iri ɗaya ba ce Sister". Daga haka suka ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama, da wannan matsayar ta samu sauƙin damuwar da take ji.

Da daddare bayan sun gama cin abinci, yana lura da yanayinta na rashin sakewa da shi har yanzu, amma ya share, sai da ta gama jujjuya maganar tana tunanin karɓuwarta a wajensa sannan ta ce"Masoyi ina da magana mai muhimmanci".

Ya ce"Ina sauraronki".

Ta gyara zama ta kama hannunsa tana wasa da shi, ta ce"Na san ba na sauke duka nauyin da ya rataya a wuyana ta ɓangaren kula da gidan nan, ni ma ba na son zaman yara a maƙota, ga shi kai ma ana katse maka kasuwa, da safe a katse maka bacci ka tashi ka shirya su, su tafi makaanta..."

"Ai duk na san wannan Yusra, ki tafi gaɓa ta gaba" Ya katse ta da faɗin hakan.

Ta ce"Dama tunani na yi, na ce me zai hana na samo mana Æ´ar aiki, sai ta dinga kula da gidan idan ba na nan ko?"

Ya yi shiru yana nazari, saboda bai taɓa zaton jin haka daga bakinta ba.

"Ka amince na samo?" Ta tambaye shi jin ya yi shiru.

Ya girgiza kai ya ce"Yusra ba na son ƴan aikin nan, kuma ma gidan nan bai yi girman da za a buƙaci ƴar aiki ba, indai don kula da yara ne, zan duba yiwuwar duk ranar da kike yin aikin kwana a kai su gidanmu su kwana a can, ni kuma zan kula da kaina, sai ki taya ni addu'ar Allah Ya ba ni ikon riƙe kaina, idan kuma na ga hakan duka bai yi daidai ba to ina ba ki haƙuri, don gaskiya zan iya ƙara aure..."

"Wai da gaske?" Ta katse shi da tambaya, idanuwanta sun kawo ruwa, ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.

Ta ce"Sadiq ka san zan iya haƙura da aurenka saboda kishiya?"

Ya yi guntun murmushi ya ce"Ban sani ba, kamar yadda ke ma na tabbata ba ki san zan iya ƙara aure saboda na tsare mutuncina da tarbiyyar yarana ba ko?"

Tashi ta yi za ta bar wurin, ya ruƙo hannunta, ta fizge hawaye suna sakko mata, ta shige ɗaki ta kwanta, tana kuka mai cin rai.

ALI

Bayan sallar isha'i yana shirye-shiryen komawa gida kwatsam sai ga Reza ta zo har majalisarsu, ya haÉ—e rai duk da yana É—an fargaba saboda ya san ba ta da kirki, gefe ya ja ta don kar ta yi masa tonon silili a cikin mutane, ya ce"Haba Reza don Allah ki sakar min mara na yi fitsari!".

Ta ce"Kai dalla can, ni harkar arziƙi ce na zo maka da ita, kana so na ka biya ni kuɗin?"

Ya ce"Wallahi ina so, rashin kuÉ—in ne kawai, idan akwai ai ba zan bari ki yi ta bibiyata haka ba".

Ta ce"To albishirinka".

"Goro!" Ya faɗa cikin ƙosawa.

Ta dafa kafaɗarsa ta ce"A daren nan za ka iya biyana cikin daɗin rai, wataƙil ma ka samu jari sanadin hakan".

Ali ya ce"Don Allah Reza ta fi kai tsaye, sai kwana kike sha".

Ta ce"Wallahi wata ƙawata ce take neman mai ɗauke mata kewa, ta kira ni ta ce na lalubo mata mai jini a jika, za ta ba shi dubu biyar, sai na ga tun da kana ta ƙoƙarin biyana awon shinkafa ya hana me zai hana ka je kawai, ka ga sai na riƙe kuɗin da za ta ba ka, ka biya ni kenan?"

Ali ya É—an sosa kai yana tunani, yana son zuwa yana fargabar kar ya daÉ—e ya shiga komar Maryam, amma wannan wata babbar dama ce, ko babu komai zai sauke duka kewar dake tattare da shi, sannan ya huta da nacin Reza na neman biyan bashinta, ya sauke numfashi ya ce"Ina ne gidan?"

"Biyo ni!" Ta faÉ—a tana wucewa gaba, ya kai wa abokinsa Hamza mukullin babur É—insa yana faÉ—a masa yana zuwa,ya bi ta a baya zungui-zungui, suka shiga adaidaita sahu suka É—auki hanya.

Suna fara tafiya sai ga kiran Maryam ya shigo wayarsa, ya ƙi ɗauka don bai san me zai ce mata ba. A ƙofar wani babban gida suka tsaya, suka fito ta ɗauki waya ta yi kira, babu jimawa wata babbar mace ta fito ta ba wa Reza kuɗi idonta a kaina, sannan muka shiga Reza ta koma, sai ƙarewa gidan kallo nake, wanda nake mamakin a ce mace ce ita kaɗai take rayuwa a cikinsa, haka dai nake biye da ita har cikin babban falon da ya ji kayan more rayuwa, sanyin Ac sai ratsa ni yake yi, babu wani tsayawa bayani ta nemi gudanar da abin da ya kawo ni kai tsaye, ni kuwa ban yi ƙasa a gwiwa ba wurin faranta mata, har ban san tsawon lokacin da na ɗauka ba.
Chapter 5 · 0% Book details