← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe shayi ya dafa musu da ɗumamen tuwo, ya yi musu wanka ya shirya su suka tafi makaranta, shi ma ya tafi shago. Tana dawowa ta gyara gida, ta sha sauran shayin da biredi, ta yi wanka ta zauna har za ta kira wayarsa ta fasa, don kar ma ya ce zai zo, ta yi kwanciyarta, da wuri ta yi girki, ta zuba na yara ta kai musu maƙota, sannan ta zuba na shi ta bawa yaro ya kai masa, ta zuba nata a kula ta tafi kemis, daga nan ta wuce asibiti.

Yau dab da magriba ta dawo, kusan lokaci ɗaya da yaranta, ta shiga ta taho da su, suna ta farin cikin yau Momynsu tana gida, sosai suke kewarta idan tana yin aikin kwana, don ma wani lokacin tana zuwa har islamiyyar ta gansu, cike da farin ciki suke ta ba ta labarin makaranta, su suka zaɓi abincin da za a dafa, ta ɗora, suka yi sallah tare, sannan ta yi musu wanka, tana taya su home work har ta gama girkin, suka ci a faranti ɗaya cike da ƙauna irin ta uwa da ƴaƴanta, bayan sun gama ta ba su wayarta suna ta kallon bidiyoyin yara na ilimi har suka yi bacci, ta gyara shimfiɗa ta kwantar da su, sannan ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci.

Tana kwance tana ɗan taɓa chatting ya dawo, wajen tara da rabi, ta je ta karɓi ledar hannunsa tana yi masa murmushi mai cike da ƙauna, ta kai kitchen ta taho da abincinsa, kafin ta fito har ya shiga wanka, a bakin gado ta zauna ta ɗauki wayarsa da ke ajiye, wacce ta san babu ruwan shi da saka cord, ta duba call long ta yi murmushi ganin duk amintattun kira ne babu na zargi, haka ma massages, shi babu ruwansa da chart, babu ma App ɗin whatsApp a wayar, sai facebook da yake da tsirarun abokai, wannan tana yawan dubawa ta wayarta don ta ga abokansa, tun da nan ma bai wani saka tsaro ba.

Tana ajiye wayar yana fitowa daga banɗakin, ta sakar masa murmushi, ya yi mata murmushin gefen baki, jikinta ya ɗan yi sanyi, don ba haka suka saba ba, a hankali ta ƙarasa inda yake tsaye a gaban sif yana duba kayan da zai saka, gabansa ta je ta tsaya ta riƙe duka hannuwansa daga ɗaukar kayan, ta shiga jikinsa ta kwanta, ya shafa kanta bai ce komai ba, ta ce"Na ga kamar kana cikin damuwa".

Kai tsaye ya ce"Ai ke ce".

Ta ce"To ka yi haƙuri, yanzu ba ga ni ba?"

Ya ja hannunta zuwa gadon, tana ta narke masa, har suka samu nutsuwa cike da ƙaunar juna, sun yi wanka sun fito suna cin abinci ta lura da yadda har lokacin ba ya cikin shauki kamar da, ta tattara hankalinta gare shi ta ce"Masoyi akwai abin da yake damunka bayan kewata, don Allah kar ka ɓoye mini".

Ya yi saurin girgiza kai, ya ce"Babu komai Masoyiya yanayi ne kawai, kwana biyu kamar zan yi zazzaɓi, kuma kewarki ce take haddasa mini irin hakan, ina da mata amma na kwana da kewa kamar mara gata...".

Ta katse shi a shagwaɓe ta ce"Don Allah kar ka ce haka, yanzu ba ga shi kewa ta tafi ba?"

Ya ce"Amma haka zan rayu ba kodayaushe zan samu kulawarki ba?"

Ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, yanayi ne ya zo da haka".

Ya ce"Amma idan na ce miki yanayi ya saka ni son ƙara aure za ki fahimta?"

"Sadiq! Aure za ka yi?" Ta tambaye shi a tsorace

Ya girgiza kai ya ce"Sam, kawai tambayarki na yi".

Jiki a sanyaye ta ce"Wannan bai kai dalilin ƙara aure ba, kuma ma na ga..."

"Ya isa, gwada ki na yi fa" Ya katse ta.

Ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi ba don ta yarda da cewar gwajin ba ne, da wannan tunanin ta kwana a ranta.

GIDAN HARUNA

Kasuwa Haruna ya nufa kai tsaye, don yaron shago ne, kasancewar babban shago ne ana biyansa daidai gwargwado, sai dai wannan halayyar tasa da ta zame masa katankatana ita ce take lamushe duk wani abu da zai samu, duk a zatonsa idan ya yi aure shi kenan matsala ta mutu, da farko kamar gaske sai daga baya ya ji ya rage samun nutsuwa da Halima, sannan ma sam ba ta da wayewa ta wannan fannin, ta ƙi sakin jiki da shi, su na bazan sun fi ta iya komai da yake so, shi yasa ya fi samun nutsuwa da su. A duk inda ɗan bariki ya haɗu da ɗan'uwansa ba ya ɓuya, don haka tun a satin farko da su Zainab suka tare a gidan ya gane ita ma ƴar hannu ce, kamar da wasa wataran zai shiga wanka tana zaune ya tsaya yana kallonta, sai ya ga ta ɗage masa gira tana kashe ido, ya yi murmushin jin daɗi don tun a ranar farko da ya fara ganinta ya kwaɗaita da ita, bayan an kwana biyu yana ƙofar gida ta zo za ta shiga kawai ta shafa bayansa za ta shige, ya taso da sauri yana miƙa mata wayarsa, ta saka masa lambarta, kuma tana shiga gida ya kira ta, su ka yi ta waya kamar sun saba, daga nan suka fara chart na musayar kalaman banza don kar ta san kar babu wani abun ɓata lokaci, sautari idan zai shigo gida yakan taho mata da leda tsire ko balangu ko dangin kayan sanyi, kafin ya ƙaraso sai ya yi mata waya ta same shi a zaure, ya lalube jikinta ta karɓi leda ta shige gida, sannan shi ma ya shiga kamar ba a yi komai ba, duk ranar da bai taho mata da komai ba ba ya faɗa mata ga shi nan zai shigo, ita kuma da safe sai ta daidaici fitarsa sun haɗu a zaure, don tana da mugun son banza, irin matan nan ne ma su yi wa maza kankat idan suka shiga komarsu.

Yau ma hakan ce ta faru, ya samu alheri a kasuwa babu laifi, don haka ya ƙunso mata balangu mai zafi da yogurt, ya sayi taliya leda uku, sabulun wanka da omon wanki, don ya ragewa Halima.

A zaure ya tsaya ya kira ta ba ta É—aga ba, don lokacin tana tsakar gida wayar tana É—aki, tana ganinsa ta taho da sauri za ta rungume shi, ya kauce yana kallon É—akinsa ya ce"Haba Zee mene ne haka?"

"Naki yana zaure" Ya faÉ—a yana saurin shigewa É—aki.

Ita kuma ta je ta ɗakko ledar ta shiga ɗaki, ta baje ledar cike da zumuɗi, Baaba ta ƙure ta da kallo ta ce"Ke Zainab a ina kike samo balangun nan ne?"

Ta haÉ—e gira ta ce"Haba Baaba ai kin san saurayina ne yake kawo min".

Baaba ta ce"To me yasa ba kwa zancen ne sai dai ki leƙa ki karɓo ya tafi?"

Ta ce"Aiki ne yake yi masa yawa wallahi, kuma shi dayake aure ne a gabansa ba ya son ma dogon zance, sai ya ce duk ƙarya ce ake shararawa".

Baaba ta sauke ajiyar zuciya tana karɓar balangun da Zainab ta ɗibar mata ta ce"Ni dai don Allah ki kama kanki Zainab, kin ga dai amana na karɓa, ki taimake ni na aurar da ke kar ki sake jajibo mana wani abun kunyar a nan, na bar waccen unguwar saboda ke, nan dai kin ga mu baƙi ne babu wanda ya san tabonki ballantana ki rasa miji, ki nutsu don Allah kin ji?"

Ta ce"In sha Allah Baaba ba zan ba ki kunya ba".
[2/17, 10:29 AM] Sadiya abdulrazak: PAGE 3

Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

GIDAN HARUNA

Halima ta tashi daga ƴar kwanciyar da ta yi a sallaya bayan idar da sallar isha'i, idonta fal bacci, saboda gajiyar da take kai wa dare da ita dalilin kujiba-kujibar da take wuni tana yi na sana'o'inta, ta yi murmushi tana yi wa mijinta sannu da zuwa, Haruna ya zauna yana amsawa, ya bata ledar hannunsa, da dubu ɗaya, ta karɓa tana yi masa godiya, sannan ta kawo masa abinci ta shige ɗaki ta kwanta, kafin ya gama har ta yi bacci. Ya ɗauki wayarsa ya kira Zainab suka yi fira, don ya san Halima tana da nauyin bacci ba za ta farka nan kusa ba. Can wajen ƙarfe goma har ya kwanta, Zainab ta kira shi ta ce ya kunna data, jansa ta dinga yi da maganganun banza, har ta tabbatar ta tada masa hankali sannan ta roƙe shi kan ya zo ya taya ta wanka, da farin ciki ya tashi tsam ya fice daga ɗakin, duk da yana fargaba, a tsakar gida suka yi kiciɓus suka yi wa juna murmushi ta cikin duhun, tana shiga banɗaki ya mara mata baya, ba su daɗe da shiga ba suka ji muryar Baaba tana cewa"Da mutum?"

Lokaci ɗaya ƙirjinsu ya buga, suka fara muzurai, jin ana ƙoƙarin buɗe ƙyauren Zainab ta yi saurin cewa"Da mutum, ina ciki Baaba".

A hankali ya ce"Yanzu ya za mu yi kenan?"

Ta ce"Idan ta gaji za ta koma".

Ya ce"Ta ya za ta koma tana buƙatar shiga banɗaki, kema wallahi kin fiya jaraba, ga shi za ki tona mana asiri".

Ta ce"Tsautsayi ne, wallahi na gaji da marmarinka..."

"Ni uwar me kike yi ne Zainab?" Baaba ta faÉ—a a fusace.

Ta ce"Ina masai kuma yanzu na shiga".

Suka É—auki lokaci a haka kowa tsuru-tsuru musamman Haruna, sai Zainab ta tuna da ai da waya a hannunsa, da sauri ta ce"Ka kira lambata wayar tana É—aki".

Yana kira, ta É—aga murya ta ce"Baaba ga wayata can tana ringing don Allah ki É—aga kawo ne".

Baaba da fitsari ya matse ta, a fusace ta ce"Ke buhun ubanki, wai kwana za ki yi a banÉ—akin?"

Ta ce"Don Allah Baab, kuÉ—i ya ce zai turo, kin san kuma ba ya kira biyu, don Allah je ki kar ta katse kafin na fito".
Chapter 4 · 0% Book details