← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da gajiyawa ta ce"Oh! Yau fa na zauna sosai a kemis, kuma na je wani gida karɓar haihuwa, sai magriba ma na shiga asibiti a latti".

"Ok sai da safe" Ya faÉ—a yana shirin katse kiran.

Ta ce"Na gode Masoyi".

Ya ajiye wayar yana tunanin kalar rayuwar gidan nasa, da haka bacci ya kwashe shi, yana dawowa daga sallar asuba ya É—ora musu abin karyawa a electric kasancewa akwai nefa, shi ya shirya yaran suka ci abinci ya saka musu wanda za su tafi da shi, ya bar mata nata, ya jira mai mashin ya zo ya tafi da su makaranta, shi ma ya tafi shagonsa na provition da babu nisa da gidansa.

Bakwai da rabi Yusra ta koma gida, don ta tsaya jiran wacce za ta karɓi dutyn safe, saboda tana bawa wata mai naƙuda kulawa sosai, ba ta so ta barta sai ta damƙa ta a hannun wacce ta san za ta kula da ita, duk saurinta ba ta tarar da su a gidan ba, bacci ne fal idonta amma haka ta haƙura tana ajiye jaka ta shiga kitchen ta fara wanke-wanke, sai da ta gyara ko'ina gidan ya dawo hayyacinsa ya ɗauki ƙamshi sannan ta ci abincin da ya ajiye mata, ta yi wanka ta ɗauki waya ta kira shi, "Ina kwana?" Ta gaishe shi bayan ya ɗauki wayar.

"Kin dawo?" Ya tambaya ba tare da ya amsa gaisuwar ba.

Ta ce"Na dawo".

"Ok anjima kaÉ—an zan kawo cefane". Ya faÉ—a yana sauke numfashin da ta san fassarsa.

Ta ce"Ka bar shi, wake da shinkafa zan yi ai, kuma Nura zai zubo gas".

"Zan zo dai" Ya faÉ—a.

Ta ce"Masoyi da ka haƙura dai, wallahi jiya ban samu bacci ba, yanzu ina dawowa na hau kan aikin gida, bacci zan yi kafin na tashi ɗora girkin rana, kaina har ciwo yake".

Yana haɗiye ɓacin ransa ya ce"Amma yau ma fa dutyn dare za ki fita, ba kya tunanin..."

Ta katse shi da faÉ—in"Don Allah Masoyi, gobe ina gida fa".

"Ok" Ya faɗa, yana katse kiran. Ita kuma ta gyara kwanciyarta ta fara bacci hankali kwance. Sai sha biyu ta tashi, ta kira yaronta Nura ya sako mata gas, har ma da cefanen kayan miya, don ba ta son zuwan mijinta shi yasa ta ce masa ba sai ya kawo cefane ba, saboda ta san idan ya zo hana ta bacci kawai zai yi, shi ma ya katsewa kansa kasuwa, a gurguje ta yi shinkafa da miya, tana saukewa ta ɗora tuwon dare don shi a son samunsa kullum ya ci tuwo da daddare, amma ba kullum take samun damar yi masa ba, saboda aiki, ƙarfe ɗaya aka dawo da yaran daga makaranta, suka ci abinci ta yi musu wanka, sai da suka saka unifom ɗin islamiyya sannan ta fito da littafansu suka yi home work, tana sauke tuwo ta yi wanka, ta shirya ta ɗauki abincin Sadiq ta haɗa kansu ta kai su makarantar da babu nisa da gidansu, sannan ta wuce shagonsa don kai masa abincin.

Gefe ta tsaya sai da na ciki suka fita, sannan ta ƙarasa murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ce"Sannu da aiki Masoyi".

Ya yi guntun murmushi yana kallon yadda ta yi kyau tana zuba ƙamshi duk da ba kwalliya ta yi ba ya ce"Na gode". Ta ajiye masa kular tana cewa"Ya kake, komai ƙalau ko?" Ya gyaɗa mata kai yana ta kallonta.

"Kemis?" Ya tambaye ta.

Ta gyaÉ—a kai ta ce"E zan je na É—an zauna, na gama aikin gidan, har tuwo na yi maka".

Ya ce"Kin kyauta kuwa, sai goben". Ta yi murmushi ta fice, yaran sun sani daga islamiyya maƙotansu za su shiga, sai ya dawo bayan sallar isha'i ya ɗakko su, duk da ranar da ba ta nan ne yake katse kasuwar, amma a ƙa'ida goma da rabi yake tashi.

GIDAN HARUNA

Ƙarar alarm ne ya karaɗe ɗakin, hakan ya sa Halima tashi a firgice, ta janyo wayar da ke kusa da ita ta latsa alarm ɗin ya mutu, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci ta miƙe zaune, ta dafe kanta tana jin yadda ya sara mata, tun dare ta kwanta da ciwon kan, ga shi har yanzu bai sauka ba, sakkowa ta yi daga gadon ta fita tayo alwala ta dawo ta canza kaya ta kabbara sallar da ake yi ta asuba, tana lazimi tana gyangyaɗi har bacci mai ɗan nauyi ya kwashe ta daga zaunen, a firgice ta tashi ta ga gari har ya yi haske, ga kukan tsuntsayen da suke faɗa mata lokaci ko da babu agogo, da sauri ta fita ta kunna murhunta na gawayi, sannan ta dawo ɗaki ta fara firfito da kayan sana'arta ta wainar fulawa, wata matashiya ce ta fito daga ɗakin dake kusa da nata tana cewa"Ashe kin fito, yanzu nake cewa yau Halima ta makara".

Halima ta yi murmushi ta ce"Zainab ina kwana? Wallahi yau baccin ya yi mini nauyi ga ciwon kai tun jiya".

Zainab ta ce"Ai ke ce ba kya hutawa Halima, sai ki sha magani kafin ki hau suyar nan".

Jin ba ta bata amsa ba ya sa ta san ba ta da maganin, ta shiga ɗaki ta fito hannunta ɗauke da kofi da kuma maganin, kunun alkama da ta saba damawa ne ta miƙawa Halima tare da maganin, ta karɓa tana godiya, ta kwankwaɗe sannan ta sha maganin, Zainab ta ce"Zauna ya ɗan tsarga miki Halima bari na fifita miki wutar".

Ba don kan ya daina ciwo ba ta tashi ta hau suyar wainar, mutane suna ta shigowa suna siya, yawancinsu ƴan makaranta ne, sai da ta gama tsaf sannan ta saka a farantai biyu ta miƙawa Zainab ta leƙa ɗakin da Zainab ɗin ta fito wanda kakarta ke ciki tana jin radio ta miƙa mata, suna gaisawa.

Ta dafa shayi ta juye a flas ta É—auki wainar da ta zuba a wata Æ´ar kula ta kai É—aki ta ajiye, tana nan zaune a tsakar gida tana wanke-wanke yaron da yake kai mata tallar wainar makaranta ya zo ya É—auka ya tafi, bayan ta share tsakar gida ta shiga É—aki ta auno shinkafar da take dafawa ta siyarwa ta fito ta fara tsince ta, sai da ta gama ta É—ora tukunya ta saka wake, sannan ta koma É—aki ta tarar mijinta ya tashi, ta kalle shi cike da takaici ko sallar asuba bai yi ba, sai yanzu zai yi idan har an yi sa'a yana da niyyar yi a ranar, ta kalli yadda daga tashinsa har ya É—auki waya duk da ta san halayyarsa ce amma tana takaicin abun.

"Ga wainarka da shayi" Ta faÉ—a tana tura kayan gabansa

Ya ce"Ki É—an dafa min taliya da ita zan karya, wannan wainar kuma ki samu leda ki saka min".

Ta ce"Taliya ai ka san ta ƙare".

Ya yi tsaki ya tashi ya fita don yin wanka, daga shi sai gajeren wando, wanda har zuciyarta ba ta son hakan, ko don Zainab da ke zaune a tsakar gidan kullum daidai wannan lokacin, ta yi masa ƙorafi har ta gaji, ta lura abun ya bi jikinsa ne.

Yana gama karyawa ya fara sosa kai, tsaki ya ja fuskarsa ta nuna alamun damuwa, Halima da ta san kwanan zancen ta ce"Lafiya kake tsaki?"

Haruna ya ce"Wallahi Halima jiya zero na shigo gidan nan, wannan shinkafar ma bashi na karɓo ta, kin ga bai kamata yanzu na fita ban bar miki komai ba".

Ta yi guntun murmushi ta ce"Haba kar ka damu, Allah zai rufa asiri, watarana sai labari, ga wannan ka hau babur". Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗari biyu

Ya karɓa ya ce"Na gode, kai ni kam na yi sa'ar mace ta gari, Allah Ya shi miki albarka".

Ta amsa da amin, shi kuma ya fice. Ta yi shiru tana tunanin kalar rayuwar auren da take yi, sam Haruna ba shi da zuciyar nema, dududu wata uku kenan da auren amma kullum a haka ake, dama a wurin da take siyar da abinci suka haɗu har ya aure ta, don haka da ta lura da irin mijin da ƙaddara ta zaɓo mata, sai ta fara sana'o'inta, tun da idan ya kawo abin da za a dafa shi kenan, babu ruwansa da mahaɗi, ita ce gawayi, mai, magi, kayan miya, omo, sabulu da siyan ruwa, sai dai duk ranar da ya samu yana ba ta dubu ɗaya, saboda haka take ƙara dagewa a kan neman na kanta don ta rufawa kanta asiri.

A zaure suka yi kiciɓus da Zainab ta sha gabansa tana cewa"Haruna ni me kake nufi da ni wai? Jiya ko biyar ba ka ba ni ba yau ma..?"

Tana direwa ya ce"Ki yi haƙuri Zee, wallahi jiya ban shigo da komai ba, shi yasa ma kika ga na yi dare, saboda shinkafa ma a tata na ɗiba na saka a leda na ajiye kawai, saboda ta yi zaton da ita na shigo, amma yau dole zan shigo miki da wani abu, ai za mu haɗu ko tawan?"

Ta ruƙo hannunsa ta ce"Ko na karyawa fa ba ni da shi".

Ya sauke numfashi cikin sarewa da halinta, ya ciro É—ari biyun da Halima ta ba shi ya ba ta, ya fice. Ta soke a hularta, ta shigo gidan tana gyara rigarta da ta zame ta don ta É—auki hankalinsa, ta shigo ta fara fifitawa Halima wuta tana É—an É—aga murya ta ce"Halima fito da barkonon na daka miki".

Tana murmushi ta fito da shi, a ranta tana jin daÉ—in irin kirkin Zainab da kakarta wanda yau satinsu uku kenan da tarewa a gidan, amma har sun saba.

08028966015
[8/19, 5:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

FIRST CLASS WRITERS

PAGE 2
Chapter 2 · 0% Book details