← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga gidan ta cire hijjabi ta yi gefe da shi, tana ƙarewa ko'ina kallo, mukullan ta fara gwadawa tana buɗe ɗakunan, sai ta lura babu na bedroom ɗin Yusra, ta taɓe baki ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke, ta fito ta share ko'ina ta goge, ta share tsakar gidan har da wanke kayan su Afna duka, sannan ta ɗora girki, a cikin jakarta ta fito da leda mai ɗauke da magi, curry kala biyu da niƙaƙƙen nama soyayye, ta tsara haɗalliyar jollop, sannan ta kunna ɗayan gas ɗin ta ɗora wani girkin, ta saka magi da curryn da ta tarar a gidan, kafin ya dahu ta yi wanka ta ci kwalliyarya ta canza kaya, don da wasu kayan ta taho, tana gamawa ta zuba ta ci ta ƙoshi, ta juye ɗayar tukunyar wacce ta dafa kaɗan don Yusra, ta zuba na Sadiq ta rufe gidan ta tafi kai masa, a lokacin sha biyu saura kwata, tana zuwa ta ga ƙofar shagon a rufe, ta jira har shiru bai dawo ba, ganin har sha biyu ta yi ya sa ta koma gida saboda kar yaran su dawo, babu jimawa kuwa suka dawo, da saurinta ta tare su ta rungume su, suka tsaya suna kallon juna, duk da Momynsu ta faɗa musu ita za su dinga tararwa a gidan, kuma sun ganta ranar da ta zo.

Hannunsu ta ja suka ƙarasa ɗaki, tana cewa "Sannunku ƙawayena kun gaji ko?" Suka gyaɗa mata kai.

Ta cire musu unifom, ta yi musu wanka suna ta bin ta da ido, ta saka musu kaya marasa nauyi, sannan ta zubo musu abinci a faranti ɗaya, ta zauna tana ba su a baki tana yi musu murmushi har suka ƙoshi, sun ci sosai, saboda canjin test ɗin abinci da suka samu, ba irin wanda Yusra ta saba dafawa ba, ta ba su ruwa suka sha, sannan ta ɗakko jakarsu ta taya su home work, suna gamawa ta saka musu unifom ɗin islamiyya ta ɗakko alawowi ta ba su, ta zauna tana musu tatsuniya, har lokacin makaranta ya yi, da yake babu nida da yaran maƙota suke tafiya, ta ce daga yau ita za ta dinga raka su, sai da ta sake gyara fuskarta sannan ta ɗauki abincin babansu suka tafi, ta kai su makarantar ta ƙarasa shagon, wannan karon a buɗe yake, ta tsaya a gefe har mutum biyu da suke ciki suka gama, sannan ta ƙarasa da murmushi ta gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, ta miƙa masa abincin ta ce"Ga shi, ka yi haƙuri na kawo a makare, tun kafin sha biyu na kawo maka, sai na tarar shagon a rufe, na jira wajan minti goma sha biyar sannan na koma saboda su Afna kar su dawo babu kowa".

"Ok, na je kasuwa ne" Ya faÉ—a bayan ya gama jinta.

Har ta juya ta tafi ta dawo ta ce"Kenan kullum daidai wancen lokacin kana kasuwa?"

Ya ce"Ba kullum ba".

Ta ce"Me zai hana ka ba ni lambarka, idan zan zo sai na dinga tambayarka ko kana nan, ko kuma ranar da ba ka nan ka kira ni ka faÉ—a min ko?"

Ya ɗan yi jimm, sai kuma ya ga tana da gaskiya, hakan zai fi mata sauƙi, ya miƙa mata wayarsa ta saka lambar, tana ce masa"Kursum, na san ka manta sunan" Ta ƙarasa da shegen murmushi.

Tana fita ya yi saving lambar, sannan ya É—akko abincin ya fara ci, cokali É—aya ya yi, ya ji girkinta ya bambanta da na Yusra, É—anÉ—anon ba É—aya ba ne, sai ya bar shi a kowa da irin hannunsa, amma abincin ya yi masa daÉ—i, ya cinye tass ya sha ruwa.

Kursum ba ta jima da komawa ba Yusra ta dawo, dama ta wanke fuskarta kafin ta dawo, kuma ta ƙara wanke-wanke ta gyara gidan tsaf har da turaren wuta, Yusra ta ji daɗin yadda ta tarar da gidanta, a ranar farko har ta fara jin daɗin ɗaukar ƴar aiki, yanzu da tuni yadda ta dawo a gajiyen nan aikin gida za ta hau da girki, yanzu kuwa Kursum na tafiya abinci ta zubo ta ci, ta yi wanka ta kwanta ta huta, sai la'asar ta tashi don tafiya kemis.

A shagon shi ta tsaya ta shiga da sallama murmushi É—auke a fuskarta, ya yi mata murmushin shi ma yana amsawa "Kin dawo?" Ya tambaye ta.

Ta ce"Ga ni kuwa, ta kawo maka abinci ko?"

Ya gyaÉ—a mata kai.

Ta ce"Na ga alamar za mu shirya da yarinyar, ba ta da son jiki, har da kayan yara ta wanke, gida fess".

'Kuma ta iya girki' Ya faÉ—a a zuciyarsa. A fili kuma ya ce"Madallah! Kemis za ki je?"

Ta ce"E, zan ɗan leƙa, Nura yana can, da wuri ma zan dawo na yi maka tuwo".

"To na gode, sai na dawo" Ya faÉ—a yana ta kallonta, har ta tafi.

Ana kiran sallar magriba ta koma gida sai da ta ɗakko yaran a maƙota suka shiga tare, ta ɗora tuwo ta yi alwala suna idar da sallah suka fara bata labarin Anti Kursum, kamar yadda ta ce musu sunanta hakan, ta ji daɗi sosai da yaran suka saki jiki da Kursum ɗin, har ta kira Sumayya ta ba ta labari ta sake yi mata godiya sosai, Sumayya ta ce "Babu komai, ai yi wa kai ne"

GIDAN HARUNA

Sosai Haruna ya yi mamakin yadda Zainab ta ƙware, ashe karuwar gida ce zaune, duk da babu wani gyara a jikinta amma salonta ya gigita shi, da ƙyar ya bari ta koma ɗakinsu, don roƙonta ya dinga yi ta kwana a nan ɗin, ta ce ba zai yiwu ba, Baaba tana farkawa fitsarin dare, haka ya kwana ransa fess shi bai ƙi Halima ta yi wata ɗaya a gida ba ma.

Washegari da safe Halima ta kira shi suka gaisa sai ya ji bai kyauta ba, don tun da ya kai ta gidan bai kira ta ba, ya ce"Ki yi haƙuri Halima wayata ce babu kati, shi yasa ban kira ki ba, ya jikin naki?".

Ta ce"Babu komai, jiki Alhamdulillah, yanzu za mu je asibiti da Umma".

Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, da daddare zan zo, Allah Ya sa dai na samu abin da zan siya miki wani abun".

Ta ce"Amin, idan ba ka samu ba ma ka zo, zuwan naka ya fi muhimmanci fiye da abin da za ka kawo, ka ga idan ba ka zo ba Umma ba za ta ji daÉ—i ba".

Ya ce"Zan zo in sha Allah! Na gode Halima Allah Ya ƙara miki lafiya, gaskiya zan yi kewarki kafin ki dawo".

Ta yi murmushi ta ce"In sha Allah ba zan fi kwana uku ba ai".

Gabansa ya faÉ—i, shi da yake fatan ta yi wata É—aya sai ga shi tana zancen kwana uku? Ya ce"Haba Halima lafiyarki tana da muhimmanci a gare ni, saboda haka ki zauna ki warware sosai, babu komai zan jure kewarki".

Ta ce"To, sai dai yadda ta yiwu".

Da daddare da ya dawo daga kasuwa, ya sayi lemo, kankana, madara, milo Æ´an saches, suga biredi da maltina ya haÉ—a da dubu biyu ya kai mata, bayan sun gaisa ta ce"Ga shi ba ni da lambar Zainab ballantana na ji ko tana fita a abincin nata?"

Cikin suɓutar baki ya ce"Ai ina da lambarta".

Da mamaki ta ce"Lambar Zainab ɗin? Yaushe ka karɓa?"

Sai yanzu ya san kwaɓar da ya yi, nan take ya fara in'inar da bai san yana da ita ba.

LITTAFIN WANI AUREN NA KUÆŠI NE A KAN NAIRA 300 KACAL!

2526907490
Aisha AbdulrazaÆ™
Zenith bank

KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[8/19, 5:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

FIRST CLASS WRITERS

PAGE 7

Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

Ya ce"Na yi zaton Salma kika ce ƙanwarki, ban ji sosai ba". Ba ta kawo komai ba a ranta, suka yi sallama ya tafi.

A ranar ma haka Zainab ta je ɗakinsa suka ƙara haɗuwa. Sanda ta kwana uku a gida Baaba ta ce masa ya yi musu kwatance za su je gidan, sai ya kwatanta musu ya kuma ba su lambarta, suka je suka duba ta, Baaba ce take cewa Umman Halima"Tun da jikin nata da sauƙi ai dama komawa ta yi, kin ga Zainab babu abin da ba za ta yi mata ba, ni kuma zan dinga saka ido akanta".

Umma ta ce"Gaskiya ne, mun gode Baaba, to in sha Allah ko gobe sai ta koma, ai jikin nata da sauƙi kam, aman ma ya tsaya".

Sun É—an jima suna fira sannan suka tafi, takaici kamar ya kashe Zainab ganin Baaba ta dage sai Halima ta dawo sai kace ita take aurenta, suna hanya ta ce"Wai ni Baaba me yasa kika damu sai ta koma? Ko mijinta bai damu ba sai ke?"

Baaba ta ce"Kar ki ishe ni da shirmen banza da na wofi, shi mijin nata ne ya faɗa miki bai damu ba?" Daga haka aka yi shiru da zancen, har suka ƙarasa gida Zainab ranta a ɓace.

Ranar ce masa ta yi ba za ta je ɗakinsa ba ma, tun da har ya yarda Halima ta dawo bai damu da ita ba, gara ta yi zamanta, ya dinga rarrashinta ta ƙi sauraronsa.

GIDAN ALI
Chapter 10 · 0% Book details