Sashe 6
Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin na fito daga wanka ta kawo min abinci mai rai da lafiya, dama yunwa nake ji, na ci na ƙoshi na kora da lemo mai sanyi, sai a lokacin ta kalle ni ta ce"Ya sunanka?"
"Aliyyu" Na ba ta amsa ina murmushi.
Ita ma murmushin ta yi min ta ce"Gaskiya na ji daÉ—in haÉ—uwarmu, nawa Reza ta ba ka?"
"Dubu biyar" Na ba ta amsa.
Ta ce"Ni zan ƙara maka dubu biyar yanzu, sai dai babu cash a hannuna, kuma ATM ɗina ya samu matsala, ka kwanta ka huta bari na shiga maƙociyata ta ara mini, ko na daɗe kar ka fito".
Ya jinjina mata kai cike da farin ciki, sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga sha É—aya saura mintuna, ga miss call É—in Maryam rututu har da massages, tsoro ya kama shi, gabaÉ—aya hankalinsa ya tashi, Allah Ya taimake shi ba ta daÉ—e ba ta dawo, ta ba shi dubu biyar, sannan ta shiga kitchen ta fito da leda ta ba shi, ta ce"Ga mai adaidaita nan zai kai ka sauke ka, ka ga dare ya fara yi".
Ya ce"Na gode sosai Hajiya". Suka yi musayar lamba, ya fita ya shiga adaidaita sahun yana yi masa kwatance har suka ƙarasa.
A sanyaye ya ƙarasa gidan nashi, yana tura ya ji shi a rufe kamar yadda ya yi zato, ya ciro waya ya kira ta, bugu ɗaya ta ɗauka "Ki zo ki buɗe min, ina ƙofar gida". Ya faɗa da fargaba.
Yana jin motsin buɗewarta, ya mayar da ledar hannunsa bayansa ya ɓoye, tana buɗewa ko kallonsa ba ta yi ba ta juya ta koma, ya rufe gidan ya ajiye ledar a zaure, ya shiga yana karanto la haula wa la ƙuwwata a hankali.
08028966015
[8/19, 5:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
FIRST CLASS WRITERS
PAGE 4
Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅
GIDAN ALI
Ɗakin gado ta shige kamar kububuwa, kafin ya ƙarasa har ta kwanta, ya ƙaraso ya zauna a sanyaye ya ce"Love ba ki san mene ne ya tsayar da ni ba..."
Ta katse shi da faɗin"Babu ruwana da ko mene ne ya tsayar da kai, ka raba dare a waje, ni dai ba zan iya ba, don haka gobe ƙarfe shida a gidanmu za ta yi min in sha Allah!".
"Innalillahi! Haba Maryamata, ai ya kamata ki ji hanzarina, wallahi aiki ne ya sha kaina, ganin ga azumi yana matsowa kuma ban tanadi komai ba, shi yasa na ce bari na dinga ƙara lokacin tashi saboda na linka samun kuɗin, amma tun da hakan bai yi miki ba, shi kenan na haƙura kawai".
Ko juyowa ba ta yi ba, ballantana ta nuna ta san yana yi. Ya zaro dubu biyu yana miƙa mata ya ce"Ga wannan kya sayi hoda".
'Ko uwar hoda ba!' Ta faɗa a zuciyarta, tun da ba ta ga amfanin yin kwalliyarta ba, kafin ta yi wanka yake fita, sai dare ya dawo, da daddaren za ta yi ta zambaɗa hoda kamar wata aljana? Ta yi ƙwafa a bayyane.
Ya tashi a sanyaye ya canza kaya, ya kashe wayarsa ya kwanta, sai kuma ya ba ta tausayi ganin bai ci abinci ba, bai yi wanka ba, duk da gajiya da yunwar da ya kwaso, kuma duka saboda ita yake yi, ya nemo mata abin da za ta ci ta sha da sutura, sai ta ji ba ta kyauta ba, to amma mazan zamanin nan ne sai kana saka ido sosai a kansu, idan ka ce za ka ɗaga musu ƙafa sai su fanɗare maka kana ji kana gani.
"Baka yi wanka ba kuma abincinka yana falo" Ta faÉ—a ba tare da ta juyo ba.
Ya ce"Babu komai, zan kwana a hakan".
Ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta fita, ta ɗauki a bincin ta kai kitchen ta buɗe ta rufe da kwando saboda kar ya lalace, shi kuma yana ta fargabar kada tsautsayi ya sa ta leƙa zaure, wata fitinar ta ɓallo, sai da ta dawo ta kwanta sannan hankalinsa ya kwanta.
Yana lura ta yi bacci ya tashi tsam, ya tafi zaure, ya ɗauki ajiyarsa ya buɗe, snacks ne da dangin kayan zaƙi su alawar madara da chocolate kala-kala, sai robar wani lafiyayyen yougurt, ya zauna a zauren ya buɗe yougurt yana sha, sannan ya kunna data yana duba sakwanni hankali kwance, ya kai minti talatin kafin ya tashi ya tattara sauran kayan, saɗaf-saɗaf ya shiga ɗaki, ya ɗakko wata babbar rigarsa ta shadda ya bazata ya jure su a ciki, ya ƙudundune ya cusa a sif, ya nemi waje ya kwanta bacci mai daɗi ya kwashe shi.
Yana farkawa ya ga gari har ya yi haske, ya kalli agogo ya ga bakwai saura, ya tashi da sauri ya fito, falo ya leƙa ya tarar da Maryam zaune tana cin abinci ga kuma babban akwati a kusa da ita, gabansa ya faɗi, ya dai fita ya yi alwala ya dawo falon, a bakin ƙofa ya shimfiɗa salayya saboda kar ta fita yana sallah, yana idarwa ya ce"Maryam yanzu duk fushin ne ya sa kika ƙi tashina sallah har gari ya waye?"
Ta ce"Ai dama ba dolena ba ne, kai ne yake dole ka tashe ni".
Ya ce"To shi kuma wannan akwatin fa na mene ne?"
Tana ajiye farantin hannunta ta ce"Gidanmu zan tafi Ali, don ba ƴar iska ka ajiye ba da har za ka kai ƙarfe goma sha ɗaya a waje! Gara na tafi idan ka gama tara kuɗin na dawo, idan kuma ka samu wata ma shi kenan". Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar hijjabi za ta saka.
Ya ƙarasa ya riƙe hijjabin kamar zai yi kuka ya ce"Haba don Allah Maryam, ai na san na yi kuskure tun da na ba ki haƙuri ya kamata ki yi min uzuri, ki gani ko zan ƙara? Naga jiya ne kawai hakan ta faru, kuma na faɗa miki dalilina, tun da ba mu fahimci juna ba na haƙura da aikin daren, wallahi haka ba zai sake faruwa ba, yi haƙuri mana kin ji kyakkyawar matata".
Ta koma ta zauna tana ɓata rai ta ce"Wannan ya zama na ƙarshe, don idan ka ƙara kai wa irin haka a waje ba zan fahimce ka ba, wa ya faɗa maka zafin nema yana kawo samu?"
Ali ya ce"Ba ma zai sake faruwa ba in sha Allah".
"Ina ka bar babur É—inka jiya?" Ta jefo masa tambaya.
Ya ce"Ai da na ga na yi dare sai na bar shi a gidanmu saboda kar masu ƙwacen babur su tare ni".
Sai da ya tabbatar ta haƙura sannan ya tafi wajen aiki, bayan la'asar sai ga wannan Hajiyar ta kira shi a waya, ya ɗaga suka gaisa take ce masa yau ma idan da dama tana son ganin shi, da sauri ya faɗa mata babu dama, suka yi sallama yana jin rashin jin daɗi, saboda yana son zuwan amma yana son zaman lafiya a gidansa don haka ya kau da kai, ya ci gaba da aikinsa.
Sai bayan magriba Maryam ta ɗauki akwatinta ta mayar da kayan ta jere a sif, buɗe nashi sif ɗin tayi, don ta kwana biyu ba ta gyara ba, tana kwaso kayan ta ji motsin leda, da mamaki ta shiga bincikawa, ai kuwa tana zazzage babbar rigar nan sai ga kayan ciye-ciye sun bayyana, gabanta ya faɗi ta hau duba su cike da mamakin yaushe suka fara haka da Ali? Abun har ya kai ya sayi kayan daɗi ya ɓoye a sif yana ci shi kaɗai? Gefe ta yi da su, ta kwashi kayan ta mayar sif don ta fasa linkewar, ta kwashe kayan ƙwalam ɗin ta je ta baje a falo, ta dinga ci kamar babu komai, sai da ta cinye komai ta sha ruwa ta zubar da ledojin tana ta mamaki, tana kuma jiran dawowarsa don ta ji dalilin wannan sabon salon da ya tsiro da shi.
Ƙarfe takwas tana yi Ali ya kamo hanyar gida, har kwakwa da dabino ya siya mata a hanya, saboda ya san tana so, ya tura ƙofar ya shiga da babur ɗinsa, ransa fes ya shiga ɗakin, ta kalle shi babu yabo babu fallasa ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa yana miƙa mata ledar kwakwar, ta karɓa ta yi godiya tana jinjina rainin hankalinsa, wato ya siyo kayan ƙwala har da dambun nama, ita shi ne zai haɗa ta da kwakwa, ta maze ta kai masa ruwa ya yi wanka, ya fito ta zuba masa abinci ta koma kujera ta kame tana cin kwakwa da dabinon.
Da É—an mamaki ya kalle ta ya ce"Ya dai Love! Yau kin ci abinci kafin na dawo kenan".
Ta girgiza kai ta ce"Wallahi ban ci ba".
Ya ce"To me yasa?"
Ta ce"A ƙoshe nake, nan da ka gan ni cikina babu masaka tsinke tura kwakwar nan kawai nake don ina so".
Ya yi Æ´ar dariya ya ce"To ke kuwa me kika ci?"
Ta ce"Abubuwan da ka ci jiya ka ƙoshi har ka kasa cin abincin dare".
Gabansa ya faÉ—i ya dake ya ce"Kamar ya? Me na ci jiyan?"
Maryam ta ce"Au har ka manta ka yi saura ka ajiye a sif kenan".
Ya ji ƙirjinsa ya ba da sautin dumm! Ya kasa cewa komai.
Ta ce"Hmm! Na yi mamaki wallahi, yaushe muka fara haka da kai? Kuma idan za ka ci kai kaÉ—ai ai da sai ka ci abunka a waje, ban gani ba ballantana na saka maka rani..."