Sashe 8
Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halima ta gyaɗa kai a galabaice, Baaba ta miƙa mata buta ta wanke bakinta, ta wanke wurin tana ta yi mata sannu, Halima ta koma ta zauna a wurin girkin, tana buɗewa don ta zubar taliyar wani aman ya sake taso mata, haka ta dinga yi babu ƙaƙƙautawa, wannan karon Baaba cewa ta yi"Zainab je ki ki ƙarasa mata girkin can, ina ga ƙamshin ne yake saka ta aman nan". Zainab ta je kan girkin, Baaba ta yi sallama a ɗakin Zainab tana kiran Haruna, ya fito yana gaishe ta, ta ce"Haruna wannan yarinyar kamata ya yi fa ku tafi asibiti, ka ga duk ƙarfin halinta ta galabaita lokaci ɗaya".
Ya ce"To Baaba bari ta shirya sai na kai ta".
Ɗaki ta koma ta kwanta, ya kalle ta yana taɓe baki ya yi mata sannu, ta gyaɗa masa kai, Zainab tana gama girkin ta yi sallama a ɗakin, ta ɗauki kula a kwando ta juyo taliyar ta kawo musu, suka faki idon Halima suka kashewa juna ido.
Yana cikin cin taliyar yake cewa"Halima asibiti ya kamata na kai ki, ga shi da É—ari biyar kawai na tashi, kin ga kuwa ba ta fi kuÉ—in adaidaita ba, yanzu ya za a yi?"
Ta ce"Babu komai, ai na sha paracitamol".
Ya ce"To me zai yi miki? Ba ki ga har da amai ba? Ko ciki ne da ke ma?"
Cikin ƙosawa ta ce"Allah masani".
Ya ce"To yanzu dai tashi za ki yi, ki lallaɓa ki shirya, ki saka kayanki ko kala uku ne a jaka sai na raka ki gidanku, idan jikin ya yi dama-dama kya dawo".
Cikin rashin son hakan ta ce"Gaskiya da ka bar ni a nan É—in..."
"A hakan ba kya iya aikin komai? Daga dafa taliya kin yi amai sau biyu, ina za ki iya wani moruwa? Duk aikace-aikacen gidan waye zai na yi miki?"
Hawaye ya zubo mata, ta san gaskiya ya faÉ—a mata, saboda haka ta ce"To shi kenan mu tafi É—in".
Tana jiri ta ɗakko ƙaramin akwatinta, ta zuba kaya, ta saka hijjabi ta kwanta a kujera tana jiransa, yana gamawa ya ce ta tashi su tafi, sanda suka fito Zainab tana daka yaji, Baaba tana zaune a tsakar gida, Halima ta ƙirƙiri murmushi ta ce"Baaba za mu tafi".
Baaba ta ce"Asibitin ne? Ya na ga akwati?"
Haruna ya ce"Ai daga can gida zan kai ta, kin ga yanayin jikinta a gidan sai ta fi hutawa".
Baaba ta ce"Haba ɗan nan! Irin haka ai babu daɗi yarinya tana fara laulayi ka kwashe ta ka kai gida, ban da abunka ba ga Zainab ba? Komai za ta yi mata, ga ni kuma zan dinga kula da ita, idan zazzaɓin ya sauka ai shikenan ma, ka dai duba".
Ya ce"Ai Baaba wannan duk wahalar da ku za a yi, ita ma ta fi son zuwa gidan, ko kwana biyu ne ta yi sai ta dawo, kin san halinta idan tana nan ba za ta huta ba".
Baaba ta ce"Ai shi kenan, kuma abincin da Halima?"
Halima ta ce"Zainab ta dinga yi, sai ta dinga cire ribarta ta ajiye min uwar kuÉ—in, har mu ga yanayin jikin".
Ta yi mata godiya, Zainab ta raka su har ƙofar gida, tana farin ciki. A ƙofar gidansu ya tsaya ko shiga bai yi ba ya ba ta ɗari biyu ya juya ya tafi, ta shiga da sallama tana jin jiri kamar za ta faɗi, nan ta faɗawa mahaifiyarta halin da ake ciki, Umma ta taɓe baki ta ce"Ke kuma ta ki ƙaddarar kenan Halima, wannan mijin naki sam ba mutum ba ne wallahi, amma babu komai lokaci ne".
Ta haÉ—a mata shayi ta sha da biredi, ta dafa mata ruwa ta yi wanka, ta fita ta siyo mata magunguna ta sha, ta kwanta bacci ya É—auke ta.
Haka Zainab ta gama abinci ta siyar ta ware ribarta, ta yo cefanen wanda za ta yi gobe. Tun kafin dare sun tsara yadda komai zai kasance, saboda haka dukansu babu wanda ya iya yin bacci, ƙarfe ɗaya na dare Baaba ta yi nisa a bacci, Zainab ta tashi ta zare sakata a hankali, ta fito ta tura ɗakin Halima da yake a buɗe babu sakata, dama yana zaune a falo yana jiranta, ya tashi da farinciki ya saka sakata, ya ja ta suka shiga uwar ɗaka, har kan gadon Halima.
GIDAN ALI
Washegari ƙalau suka tashi da Maryam komai ya wuce, ya ci abinci ya tafi aiki, wajan la'asar Hajiya ta kira shi, take tambayarsa yau zai samu lokacinta?
Ali ya ce"Wallahi Hajiya ina wajen aiki ne..."
Hajiya ta ce"Haba Aliyyu aikinka ai babu abin da zai tsare maka, idan ka tashi ba sai ka zo ba? Na ji daÉ—in haÉ—uwa da kai ne fa, shi yasa ka ga har ina nemanka, dubu goma zan baka wannan karon".
Ali ya yi jimm yana jinjina dubu goma, da dubu goman nan fa zai rage aiki, don haka gaskiya ba zai bar wannan damar ta wuce shi ba, ya ce"To zan zo idan an yi sallar magriba, sai dai gaskiya ba zan daÉ—e ba".
Ta yi murmushin jin daÉ—i ta ce"Babu damuwa, Allah Ya kawo ka lafiya".
Yana aiki yana tunani, ga Baby Farha ma ta takura masa sai ya je gidansu, sai kaucewa yake don so yake ya yi sabon ɗinki, idan kuwa yana so da wuri dole ya jajje wurin Hajiyar nan idan ya tattara ya gama buƙatunsa ya watsar da ita daga baya, ana idar da sallar magriba ko gidansu bai shiga ba, ya buga babur ɗinsa ya tafi.
A ƙofa ya tsaya ya faɗa mata ya zo, ta fito ta shiga da shi har babur ɗinsa, cike da farin ciki ta buɗe firji ta ba shi lemo me sanyi ya sha, sannan ya ce mata zai yi wanka, ta ce ita ma za ta yi dama, ba dan ya so ba suka yi wankan tare, ta kawo masa kayan ƙwalam yana ci tana kallonsa, sosai yaron ya shiga ranta, ta ce"Aliyyu kana burge ni sosai, kuma ina hango faruwar wasu muhimman lamura a tarayyarmu da kai, ga ka matashi mai jini a jika, a ina kuka haɗu da Reza?"
Ya sosa kai ya ce"Hajiya kenan, Reza a ƙasan layinmu take, mun daɗe da ita".
Ta ce"Waye kai? Ka ba ni labarinka, me yasa ka zaɓi neman mata a maimakon aure?"
Ya ce"Hajiya ai ina da auren, wannan ana yin sa ne saboda nishaÉ—i kawai".
Da mamaki ta ce"Da gaske kai ma kana da auren?"
Ya ce"Wallahi ina da mata, yanayi ne kawai ya sa ban daina harkar nan ba".
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ni ma ina da miji..."
Ya zaro ido da mamaki ya ce"Yanzu haka maganar nan da muke yi da auren wani a kanki?"
Ta ce"Ƙwarai kuwa, amma ga ni nan ina dai amsa sunan matar aure ne kawai".
Ya ce"Amma Hajiya me yasa kika zaɓi wannan rayuwar?"
Ta yi murmushin takaici ta ce"Aliyyu Wani Auren ba ya amfanar mutum da komai sai cutarwa, wani auren na jeka-na-yi-ka ne, wani auren sai dai ya kai mutum ga halaka, wani auren ana yinsa ne saboda mugunta da ƙuntatawa, wani auren ana yinsa ne saboda asiri ya rufu, kamar dai nawa auren, ina zaune a gidan nan ne kawai saboda asirina ya rufu, tun ina yarinya a haka rayuwar take, an aura min wanda ba sa'an aurena ba, ya rufe ni a gida saboda mugunta yana can yana yawon ƙasashe da sunan aiki, ko yana nan babu abin da yake iya taɓukawa, girma ya kama shi duk ya gajiya, kuma a hakan mu uku ne matansa, cikinmu babu wacce ta taɓa ko ɓatan wata, rashin haihuwa daga shi ne, ga shi zan tsufa babu ɗa ballantana jika, gani yake tun da ya bar min dukiya ya sallame ni, ya manta ni mai lafiya ce ba kamar shi ba, ina buƙatar abokin rayuwa, shiyasa nake amfani da kuɗin da yake taƙama da shi ina yin abin da ya kasa yi min, Aliyyu ka ga laifina?"
Har zuciyarsa ya san ba a kan daidai take ba, hujjarta ta yi rauni, tun da ai akwai hukuma, za ta iya kai shi a raba auren tun kafin abun ya yi nisa, amma dayake ya san ba wa'azi ya zo yi ba, sai ya ce"Gaskiya Hajiya ban ga laifinki ba wallahi, ai wannan shi ne daidai, mace sai da namiji, tun da har ya bar kuÉ—in ki ji daÉ—inki kawai, sai ki ta istigfari Allah gafurur rahim ne".
Ta yi murmushin jin daÉ—i ta ce"Na gode sosai Aliyyu".
Sun ɗauki tsawon lokaci suna aikata masha'a, shi kansa ya yi mamaki, saboda ya manta rabon da ya yi irin wannan daɗewar da mace, yau kam wasai ya ji shi kamar ya gama juye duk wata damuwarsa ta wannan ɓangaren, wani abu da bai sani ba Hajiya ta faki idonsa ta kashe wayarsa, Maryam har ta gaji da kira tana ji a kashe, sam ƙin ba shi damar tashi Hajiya ta yi, shi ma ya gaji sosai, don haka da taimakon sanyin AC bacci ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai ƙarfe biyu na dare.
A firgice ya tashi zaune tunowa da inda yake, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi lokacin da ya kalli agogo, ya ɗauki wayarsa yana mamakin yadda aka yi ta mutu, ya kunna gabansa yana faɗuwa, ya sakko daga gadon, ya zura kayansa sannan ya tashi Hajiya.
Ta tashi tana mirtsika ido ta ce"Aliyyu ina zuwa? Ka kwana a nan don Allah".
Da sauri ya ce"Ina? Ba zai yiwu ba wallahi".
Ta tashi zaune tana narkewa kamar yarinya ta ce"Don Allah ka kwana, zan ƙara maka dubu goma".
Ya ce"Ba ki san masifar da take tunkaro ni ba ne, wallahi ko a dubu É—ari ba zan kwana a nan ba".
Ta tashi ta É—akko masa dubu ashirin ta ba shi, ta ce"Amma ka san ba za ka keta unguwar nan a babur ba cikin daren nan".
Ya ce"Wallahi zan tafi ko a ƙafa ne, iya wuya dai a gidana zan kwana".
Hajiya ta ce"Ina zuwa" Ta É—auki wayarta ta kira wata lamba, ta faÉ—a masa ya zo gidanta yanzu da sauri, tana sauke wayar ya ce"Waye?"