← Book details Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waye yace ba danki bane ba ? Anwar shine yaron ki da kk haifa Fatima ,Shine danki Umar farouq ". Taajibi ne da mmki ya kama Ammie kawai sai kwallah hawaye yahau gangaro mata....Dafe kirji Diyana tayi tana fadin Daddy wai kana nufin Hayaty Anwar Yaya na ne...ammie na ta haife shi??. Maganan tayi tana nufan Daddy kwallahn itama na zubo mata idon ta ya kada a lokaci daya . Ganin Yanda Hankalin Daddy yayi matukar tashi ya rasa bakin mgn yasa Diyana nufan shi tana rungume Daddyn hadi da sakin kuka mai ban tausayi da taba zuciya ,daddy meyasa baka kawo mana shi mu ganshi...?? Daddy bakasan muna tsananin bukatar shi bane ,idan Ammie bata da bukatar shi nifa inayi ,ni ni kadaice bana da kowa sai Ammie na Abbi na ya rasu ,meyasa baka kawo mun Hayaty Anwar ba.....duka maganan take lokaci daya babu tsayawa ko sauraran mene Daddyn zaice .

Abun da basu sani ba shine tuni Jalila ta daga waya ta kira Abbas tana shaida masa komai".

*********

Har ya kammala kimtsa kansa bata farka ba ,falo ya nufa yana nufan dakin lil Zahra , Daddy na". Ta kira sunan shi dai dai Mama Sha tana gyara mata gashin kanta mai cika da tsaho . Ware hannun shi yy da gudu ta fada jikin shi tana dariya don yarinyar akwaita da fara'a ,sam bata raina abun da xata wangale maka baki . Magana yy mata kunsan dai muskilanci irin nashi can ciki yy mata mgnan ,wanda ji nayi dai Zahara tana cewa " Daddy mama Shafa tana kula dani sosai ,da dare jiya da banyi bacci ba tayi ta mun waasa har falo muka fito naga baka nan. Humm nisawa yayi yana mmkin surutu irin na lil Zahra. Bakin shi yakai yana kissing din saman goshin ta kana yace " meyasa baki bar Mama bacci ba jiya....yanxu bari mu tafi kigaida momyn ki ,kibar mama tayi bacci ... Daga masa kai tayi tana murmushi wanda sai da Hushiryar yarinyar ya bayyana wanda yake kara bayyana kyaun yariyar . Shikam dabadon yasan Shatu ba itace ta haifi Lil zahra ba da kuwa yace " Surutun da faraar nata duka na Shatun ne ,amma a hakan yana lura da Shatu ba miskilamci ne take dashi ba kyalliya ne kawai .

A haka ya fita da ita daga falon yana nufan bedroom din shi da Lil Zahra ,a tunanin shi kila Shatun ta farka daga baccin yanxu .

Kwance yanda yabarta haka ya ganta ,sai ma kara rufa jikin ta da tayi rijif da alama tana jin dadin baccin ta . Sauka Lil tayi daga jikin shi tana fadin " Dad momy bacci fa takeyi". Mu fita mu tafi kar mu tasheta . Tayi mgnan a hankali tana kasa da muryar ta wai duk don kar su tashi Shatu . Murmushi yayi yana kallon kyakykyewan fuskar Shatun da yy dan haske yakuma yi fiyau kawai na zullumi tsakanin jiya da yau .

Hannun shi yakaai yana shafa lallausar gashin ta ,da yake a wqrwaje saman fillon ,itakam Lil sai tsalle tayi tana hayewa saman gadon tana murmushin da yazamana halirtaccen ta ne . Kissing din Kumatun Shatun yy ,wanda nan ya tsinkayi muryar Lil tana cewa " Nima Daddy".

Kallon ta yayi yana murmushi kamin ya yi nata alama ta matso kusa dashi ,matsawa tayi kusa dashi su duka suna cure wuri guda ,yana kissing din kumatun ta.... Abun ne ya mai dashi wasa duk don Zahran ,shi kurum yana son yarinyarne saboda sunan da take dashi ,babban suna ne a wurin shi yanajin sunan a ranshi ,da kuma yanda Yaga Shatun na matukae son Lil zahran .

Idan yy kissing din Shatu sai yy na Lil zahra dariya Zahra keyi har da kyakyatawa ,wanda itadai Shatu ji tayi ana sumbatan ta da kuma dariya sama sama.

Motsi tafara yi da idanun ta hadi da budesu a hankali tana ware su. Zahra ta gani akanta gyefe kuma Anwar yana kissing din Ta sai kuma taga yy ma Zaharan . Kamin tayi mgnane taji muryar Lil tana kai hannun ta hadi da dagota da cewa " Mom tashi kimawa Daddy shima. Ita dai idon ta da bai gama budewa bane ta mike daga zaunen tana kallon Lil zahra....Kawai sai ta tsinci kanta cikin nishadin ganin Zahran nata cikin wannan yanayi . Murmushi ta sakin mawq diyar nata ,kana taji muryar Lil tana cewa " Momy ki masa shima . Kauda kanta tayi ,sai tsinkayar muryar Anwar taji yana cewa " kin gani lil bazatayi mun ba . Eyya Daddy xatayi maka . Momy ki ma Dad idan ba haka ba xanyi kuka . Tayi mgnan tana narai narai da ido tana shirin kuka .

Ganin haka yasa Shatu cewa " bari xanyi kissing din nashi kinji lil?". Share kwallan nata tayi tana murmushi ...kallon Anwar Shatu tayi da farin ciki ya gama cikashi .

Harara tayi masa kasa kasa tana jan kwafa a zuciyarta . A hankali takai bakin ta kuncinshi kaman xatayi kissing din nashi ...aiko kuwa ta dage ta gantsara masa cizo ,yanda tasan xaiji xafi... Jah baya tayi tana dariya itama lil Dariyar takeyi don batasan me Momyn nata tayi ba. Shikam kallon Shatu yy yana murmushin azaba hadi da mata kallon xamu hadu .

Mikewa tayi saurin yi tana masa gwalo da cewa " Nima na rama!!". Tana dariya ta shige toilet . Murmushi yy don shi ko ayanxu ranshi da zuciyar shi tayi sanyi ,ganin ko yaya dai da soyayyar Sa a zuciyar shatun yana da magurbi ko kadanne .

Mikewa yayi yana daukar Lil don duk girman ta bayajin nauyin ta xai daga yar bakutan yarinyan ya fice . Haka ya dauketa yana barin bedroom din...a falon su ya tsaya yana cigaba da kwasan dariyar lil Zahra don bakin ta baya ta6a shiru .

*********

Bangaren Abbas kuwa sam a wqnnan rana ya gaxa bacci sai kuma tsakar rana yaji wannan mgnan daga bakin Momyn shi . A zuciyar shi ne yafara farin ciki n faruwar hakan ,don acewan shi dole finnal solution din shine Mahaifiyarsa xata ce ya rabu da shatu daganan sai kuma shi ya Aureta .

Hannun shi yakai yana marin kanshi yana fadin " Anwar abokin kane ,abokin kane Abota tafi komai . Tsawon lokaci yakai yana kaiwa da komowa . Hannun shi ya kallah yana daukar hankie yana fara goge sunan Shatu ,bakin shi da zuciyar shi yana fadin Aisha matar Anwar ce Abokin ka ,kawai sai wani irin xaxxafan kwallah yafara zubo masa . A tsakin abota akwao sadaukarwa . Na sadaukar mawa Abokina Anwar ,nasan xai kula mun dake kamanni ai aboki nane . Abun da yake cewa kennan wasu irin zazzaban kwallah na bin fuskar sa . Ganin yanda duk ya sauya yaf fice a hayyacin shi baki daya yasani saurin barin falon don ni kaina na tsorata matuka da ganin namiji jarumi kaman Abbas yana zubda hawwye Akan so!!

*********

Kiga da Skirt maroon da golden na lace Shatu ta sanya ,sai fuskan ta tayi maasa simple makeup. Ganin bashi a bedroom din har ta kammala yasa ta mikeawa hadi da kokarin fitowa .

Ringing din wayan ta taji yana tashi hakan yasata saurin jah baya ,ta isa kenan taga ya katse . Don Abbas katse kirar yy yana fadin bai kamata ba Abbas Anwar Abokin kane . Ganin y katse kirar yasa Shatu saurin bin kirar don taga sunan Abbas .

Kaman baxai daga ba ,sai kuma ya daga yana yin shiru don jin mene xata ce . Hlo Yah Abbas kayi hakuri Hamm....Ya isa Aisha ,ni a jawo komai Anwar abokina ne ,nina yaudare shi , inason shi ne ,shiyasa soyaayyar shi ya shafeki ,ni kuma ban san da hakan ba ,nakasa tsayawa na tantance me nake maki sone ko mene??. Yah Abbas wannan wani irin mgna ce kk mun haka ? Eh Aisha ,ki dauke ni abokin Anwar kinji ,anwar yafini komai xaki fi jin dadin zama dashi fiye dani ,gyra kadan xakiyi ma rayuwar sa niko xaki wahala sosai kamin ki xama dani yanda kk so ....ji tayi shiru sai kuma taji ya datse kirar ,shiru tayi tana tunani tausayin Abbas yy mata yawa ,tabbas mgnan yake amma dagaji muryar sa tasan kuka yakeyi . Kwallahn da ya ciko mata idon ta ne ta goge...tana takawa hadi da ficewa tana isa falon...a can dinning ta hangesu suna xaman jirar isowan ta .

Takawa take a hnakali take wanda gaba daya hankalin Anwar ya dawo kanta...ya saki baki da ido yana kallon ta , har ta karrako bai sani ba . Shiru tayi tana masa kurr da ido ,tabbas tasan Hammman na mugun son ta ,amma shi matsalar shi baya fada mata cewa yana son ta kaman Yah Abbas . Amma a zuciyarta tasan waye gwanin ta .

Tausayin Abokai biyun ne ya kamata ,wanda bacci baya rabasu amma akanta anyi uwar watsi sun xa6i rabuwar su ,dole nasan yanda xanyi na dawo da wannannabotan ta dore har abada .

Hamma Anwar!

Ta kira sunan shi ,wanda sai a sannan ya lura da isowan ta ,dan sosa kyeya yy yana murmushi kamin yace " kinyi kyau tawan ". Hawwye ne ya zo mata ,wanda ganin hakan yasa Anwar saurin mikewa yana kallon cikin idon ta hadi da girgixa mata kai alamun kar tayi kukan . Da sauri ta fada jikin shi tana rungumeshi shima hannun shi yasa yana rungumeta .

Hamma na kayi hakuri kayafe ma Yah Abbas ,idan baka yafe masa ba xan ta6a daina kuka ka ba , savoda nasan duk nice na hada komai kayafemun Hamma nida Yah Abbas.
Chapter 6 · 0% Book details