← Book details Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Buzhuwa empire ina matan Aure y'ammata ku taho ga warakar ku tazo da alfarman annabin S.A.W . Muna bada maganin mallakar aure da dai sauran su ,kuma muna da ajent namu a kowani gari ,da yanken k'asashen dake kewaye na gida nigeria💃💃. Domun samun daman karin bayani zaku iya tuntu6an wannan number 09061466409.

Alheri writers asso.📚

________________________

"Bayan tafiyar Anwar ne abun yafara dawo mawa Mahaifiyar tashi sabo , hankalin ta ya gagara natsuwa ,wanda rasa wanda xata fada mawa halin da take ciki ne yasata sanar mawa Diyana a ranan tarewan Ammie. Ita kanta Diya hankalin ta bakaramun tashi yayi ba ,ahaka tayi kaurewa ba tare da ta bari Ammie ko wani ya fahimci damuwarta ba ,sai tufka take da warwara. Zaune ta sa hannu biyu tayi ta gumi zuciyar Diyana da tunanin ta ya tafi akan yanda xatayi taga ta dawo da Abbas k'asar sa ,ta kuma sama masa natsuwa ta hanyar kokarin mantar dashi komai . Kai ina wannan ba shawara bace ba " baxai yiwuba wannan tace tana kauda kanta gyefe. Oh ni Yalwa wannan wacce irin yarinyace kina zaune kina ta zuba shirmen surutai duk ke kadai?? Anya ba...Ba mene ba?? Kai hajiya kaka ,ni wannan tsohuwa da damu kike". Diyana tayi mgnan tana mikewa daga tsaye. Eh dole innaga abun magana nayi ,ku bakwaso asan cikin ku kuyita kunbi kunbiya ku kadai...aiko ma dai meye kike 6oyewa in yayi wari maji. Dariya Diyana tasa hadi da kama baki tana cewa" Tofah Hajiya kaka kenan ,to ai ma bazai warin ba bare har kuji din". Tana maganan ne hadi da nufar hanyar da xata bar falon. Ahaf kyayi ki gama komai xakuyi a tafin hannu nake kallon ku. Hajiya kaka tayi maganan tana kai hannun ta zuwa saman plate din kayan Marmarin dake gaban ta...tana cin Apple hankalinta sunan a kwance yake amma har a lokacin mita take game da diyanan.

A wannan karon da kyer diyana ta cinye wata a nigeria , ta san yanda tayi ba tare da mom Abbas ta sani ba da sauran iyayen ta ta nufi kasar malasia. Don duk hankalinta yaki kwanciya tun da tajiyo labarin komai da ke tsakanin jaruman kuma taurarin uku. Anwar shatu Abbas kenan.

Wanda Bayan isan ta Shatu kadai ta sanar mawa ,don itama hankalinta ya kwanta...duba ga yanayin lafiyan ta a ynxu...

Sosai Shatu taji dadin albishir din da Diyana tayi mata na haduwa da Abbas da tayi ,kuma anan take baima zuciyarta cewan Abbas yana dab da dawowa ,shima yafara sabon rayuwa cike da farin ciki da walwala kaman yanda take ciki da nata mijin.

********

A hakan ne kwanaki ke shudewa zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da nuna soyayyar juna tsakanin Anwar da Shatu abun sai dai muce mashaaallh....don wani kula yake bata na musamman ,motsa kafan ta baison yaga tayi bare kuma ganun chanjin fuska daga gareta. Lil zahra kuwa tuni ta cigaba da zuwa sabon school din da aka sakata tana babyclss ,wanda so da kauna n da suke nuna mawa diyar tasu baa mgn. Hutu Anwar ya samu wanda a wannan lokacin ne ya dauki iyalan nashi su duka suka nufi kasar egyft dangin Ammie...Kai tarba nuna tattali soyayyar da wannan mutane suka nuna masu mai yawa ce. Don fahimtan da sukayi shatu na dauke da juna biyu yaasa Yayar Ammie wato Bilqees hana su dawowa akan kari ,sai da suka kwashi tsawon lokaci daganan. Suka wuce kasa mai tsarki kana suka dawo gida nigeria. A wannan shekarar Abbas ya dawo kasar mu ta haihu ,tare ds taimakon diyana ,wanda tayi nasarar afkawa soyayyar abbas alokacin da batayi tsammani ba ,abun da xata iya sani shune tana matukar jin tausayin sa sanadin cutar Son da ya kamu dashi marar magani ,anan ne tafara alkawarin ganin ta zame masa wannan maganin da xata bashi kulawa ta har abada.

A bangaren Abbas din ma hakan ya faru ,duk da dama akwai shakuwa tsakanin shi da Diyana ,amma a wannan lokaci sakonni ne yakeji na dabam a tare da ita. Wanda basu baimawa kansu wahala wajen bayyana sirikan zukatan su ba. Koda iyaye suka fahimta bakaramun farin ciki sukayi ba. Wanda aka sanya lokacin auren su a lokaci kalilan.

Rugar surbajo kuwa idan Shatu taje yanda kasan su maida ta ciki don murna ,komai yafaru ya wuce kaman baayi ba ,an ma manta dashi. Hardo ya auri yar uwar sa a wannan ruga itama bafullatana ce yariga da ya hakura da shatun don yasan sama tayi ma yaro nesa. Anwar da Shatu sun samu Dr salma kawar mahaifiyar lil zahra, sunje har gidan marayu don suji ko sun san wani asali na mahaifiyar zahran amma basu samu komai na daga labarin taba. Hakan yasa su hakura ,shatu takara kama Lil ta rungume tamkar yanda ta dauketa a da baya.
Su teeema kam anga ala wadai ,don tun wannan tsahon shekarun babu mijin aure ,tuni ta fidda ran ta ga Anwar ,tafara neman miji amma babu. Nikam mmn teddy nayi zaraf nace ta nufi wurin jaruma BUZHUWA ,wanda da taimakin buzhuwa empire mijin aure ya tsaya anan fa duk wani hali nata mara kyau ta gyara shi ta rungumi kaddarar ta.

Bangaren mahaifiyar zabeena kam da ita ma zabeenan ,wani yaron commissioner ne ya tsaya mata ,anata iyayi da karya....Sai a ranan biki yace ya fasa ,wannan yasa Zabeena kamuwa da heart attack...tun da aka kwantar da ita a asibiti tsawon lokaci tana nan rai ga hannun allah. A wannn ciwon nata ne komai na mahaifiyar nata ya karka6e...ta dawo babu dukiyan da ake ka fahari da shi . Suka dawo babu cin yau dana gobe sai anyi maula.

Daga karshe dai har gidan Dr haula taje ta roki yafiyarta ,tare da taimakon ta akan ciwon zabeenan. Bataji komai ba sai tausaya mata da tayi ,anan ta bata makudan kudi akan lafiyan Zabeena.

Bayan shekera shida ,komai na farin ciki ya wanzu a wannan ahali ,abubuwa da dama sun shude farin ciki da walwala ya yawaita ,arxiki ya ninka na da baya. A wannan lokacinne Shatu ta nada yaran ta uku...duk da Lil zahra.bayan lil ta haifi yara biyu mace dana miji yan tagwayen ta.an sanya mawa macen sunan Hafsa Wato Hasile don sun yaba da Gwagwarmayan da wahalan data sha a GIDAN KWARATA ,namijin kuma aka sanya masa sunan jarumin gidan kwarata wato ALIYOU HAIDAR. Sai Diyana da Abbas da suke ta jero yaran su don a shekara shida yaran su uku ,maxa biyu mace daya macen sun sanya mata sunan likitan su da ta amsa haihuwar wannan tauraruwar wato DR MARYAM nasan baku manta da mairon ku ba ta BAFULLATANAN RUGA.... Sadeeq kuwa Ya auri Yar kanwar mahaifin sa ce a kano shi kuma yar sa daya ne yasaka mata sunan jaruman da tayi gwagwarmaya wato AHYAAN ,don yasan rawar ganin da ta taka a SIYASATA.

TO ANAN NAKE CEWA ALHAMDULILLAH . Anan na kawo karshen wannan littafi nawa....
'kurakuren dake ciki allah ya yafe mun,abun da na rubuta dai dai allah kabamu ladan dakuma damar aiki dashi . Inda kukaga kuskure don allah kuyi mun afuwa kunsan dan Adam ajixi ne ,nasan da yawan ku bazaku so na yanke labarin a nan ba ,amma hakan xaifi mana ne yanda muka fara cikin nishadi mu gama a haka ,ina godiya kwarai da yanda kuka nuna mun soyayyar ku a wannan littafi na WALJM ,ina fatan na gaba xan samu linkin linkin soyayyar ku ngd...taku har kullum mai maku fatan alheri maman teddy

sai mun hadu a littafina na gaba mai suna......
*🕊️KWARTON MANYA🕊️*
_(Mr Perfect🕊️)_

FROM THE EXPIRIENCE WRITER OF👇
BAFULLATANAN RUGA
ZUMA DA MADACI
SIYASATAH
GIDAN KWARATA
YAR WAYE
YAR MAULA
DIJAMA YAR FULANI
WALIJAAM
YAR AIKI
HABIBY DAIMAN
KAWALIYA TAH
BINTOTO da sauran su...

_Na kira sunan labarin da KWARTON MANYA ne badon komai don so nake na nunar da makaranta wasu abubuwa dake kulull6e da jaama'a baki d'aya kuma yake kalubakantan mu ,da bamu san dashi ba ,kuma duk yanda kuka ga labarin dama salon da yazo dashi kenan. Hummm idan na zauna ina tunanin labarin kwarton manya wato MR PERFECT sai inji kaman na dakata da yin ko wani littafi na kawo maku shi ,don lbrn ya dauko maku salo na dabam ,wanda ya kunshi abubuwa Na dabam , zamba! yaudara ,gadara izza ,butulci tare da tsantsan madarar tare da zuman kanannadaddiyar soyayya ,wanda yake bansan me xan fassara shi bama , ni kaina nakan kosa don naga na kawo maku wannan labari ,but any where ku kasan ce dani uwar teddy a new book dina mai taken MR PERFECT wanda nayi masa lakani da KWARTON MANYA!!

Inshaallh inda rai da lafiya xai fara zuwan maku ne a bayan sallah after ramadan da yardan Allah. Zaku iya tmbyan wannan littafi wato mr perfect KWARTON MANYA da zarar yau ance maki anfice sallah ,a kowani website youtube whatsaap facebook da dai sauran su...

Taku mai maku fatan alheri tare da nuna maku son so lillahi.....
Ayusha mohammed
Maman teddy🧸
08081202932
Chapter 16 · 0% Book details