← Book details Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 16

Sashe 4

Walijaam Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amincewan Anwar da yayi ne yasaka Dr Haula cemasa" a yanxu na amince xaka iya zama da matarka kaman na kowa ,amma da sharadi xaka sanar mata cewa Zabeeena a gaban ta take ba tsarar ta bane . Duk da dama ko ka fada mata ko baka fada mata tasani . Xata hada kanta da Zabeena wacce a yanxu take da mastrs degree din ta ,da ita da ta fito cikin karkarar kauye ?. Ina ai banbancin a zahiri yake . Kaje Anwar ni na fadeka daga xarar ranan da ka auri Zabeena a wannan rana ce xaka san kayi Aure . Shi dai Anwar duk mgnan Da mahaifiyar tashi take bai ce da ita komai ba. Duk da yaji dadin mgnan nata a bangare daya na zuciyarsa da tace " a yanxu ya yi komai da Matar sa...amma a daya bangaren na zuciyar sa yy takaicin Auren Zabeeena ,wacce yasan ta tare suka tashi a ynxu Zabeena ta fi karfin shekara 30 ,yasan ta yasan shadanan ta . Hummm nisawa yy a wannan lokacin yana kallon Dr Haulat kana yace "Tom Momy xanyi duk yanda kikeso.

Murmushi Haulah tayi cike da jin dadi ,a zuciyarta tana cewa lallai aikin bokan nan yafara ci. Mashaallh Yaro na Anwar ,allh yy ma rayuwarka Albarka da nema. Ameeen yace da ita ,yana mikewa da fadin Momy bari na shiga part din Daddy... Ohk yana nan ciki kasan shi ma baya hutu kullum a fama da mutane yake .

Murmushi Anwar yayi yana nufan bangaren Mahaifin nashi .

*********

Nisawa Anwar yayi yana tunanin Abubuwa dabam dabam...kamin ya mike yana nufan falon gidan. Wata Hjy ce tsaye a falon tana yafe da mayafin ta da har ke reto kasa . Murmushi Hjy Maryama tayi kana tace "Ranka yadade ga kayannnan nan an taho dasu daga dubai ,shi yasa na sauka anan . Set 2 ne ko wanne anyishi ne tamkar na Aure kaman yanda kace . Ohk ina zuwa .

Juyawa yayi yana nufan bedroom din Shatu da take zaune ta rafka tagumi tana kallon Lemon da ta ajiye gavan ta . Ta gaza shan shi sam takaici yy mata yawa . Shikknn na tashi a masoyiyar Abbas ,Hamma Anwar me yasa xakamun haka?? Kuma bayannan har da tukucin kishiya ,kishiyan ma wai kaman Zabeena ,wato ku hadu da ita ku cutar dani ko?? Saboda baka kauna ta...uhmm ai Mama Rahmati da Umma na suna kaunata ,wlh xan tafi ne .

Eashan Hamma Anwar?? Tunanin me kkiyi anan wurin ? Taho ana jurar ki a falo .

Kallon sa tayi kamin ta ta6e bakin ta gyefe ,tana mikewa bata kuma kallon shi ba . Ta yi gaba zuwa falon .

A falo kam hjy Maryam ta gani zaune gaban ta da lemu da ruwa tana shan lemun. Ah sannu Aisha ko?. Hjy maryam tace tana murmushi.

Danne mamakin kirar sunan ta da tayi Shatun tayi kamin tadan yi murmushin yake tana gaisar da Hjy Maryam.

Amsata tayi cike da fara'a don ta lura macace mai harka da fara'a hakan yasa Shatu sakin fuskan ta . Kaga kam Major Anwar komai dai dai ita aka sayo ,kaman nasan jikin ta .

Dariya yayi yana riko hannun shatu kamin ya kalleta yana fadin " Kinga kayane na saka ayo maki ordern su daga Dubai ,duba kiga sunyi maki ?. Kasa basa amsa tayi ,sai dan kauda kanta gyefe tayi ,tana mmkin rainin hankali irin na Anwar ,wato kayan fadan kishiyan ne har yasa akawo mata ,sai wani fara'a yake wato zaiyi Aure??. Hamma Yy mun ,duk abun da yakawo mun nasan me kyau ne ,Hjy mun gode sosai . Tayi mgnan cike da fara'a kaman babu komai a ranta da zuciyar ta . Shiru yayi yana dan mmkin amsa hjy maryamu da tayi kaman babu komai .

Amm tom shiknnn Major bari na barka da Amarya Aisha ,idan tana bukatar wani abu da ban saka ba ,xaa iya sanar mun.

Major...³!!! Sunan da Shatun keta nanatawa a zuciyarta kenan. To yaushe ma ya xama majorn babu lbr? Har aka masa karin girma babu lbr ,tabbas na yarda Anwar baya sona .

Aisha!!! Ya kira sunan ta yana son hada idon shi da nata. Kallon ido cikin ido sukayi wanda yasata saurin sadda kanta kasa tana kokarin juyawa ,don bata ma son wata mgn ya hadasu da Anwar din . Murmushi Anwar yayi don yaga abun da yakeson gani a kwayar idon ta .

Murmushi yayi yana fadin Aisha na tasoma kishi na...nayi farin cikin ganin hakan .

Yana gani ta nufa kitchen da alama wani abun take bukata ,shi kuma yabi bayan Hjy Maryama kasantuwar dare yy ,yana son hadata da wanda xasu isa gidan ta lfy .

*********

Bangaren Diyana kam ta wuni kirar Anwar amma wayan a kashe bata samun shi ,hakan yy matikar daga mata hankali don ita a duk duniya bata da wanda taji tana so da kauna da ya wuce Anwar .

Yana shigowa daga barikin ne yaji wayan sa tana ruri. Hannun sa yakai yana kallon sunan dake yawoa a saman screen din . Fuskan sace ta sauya a lokaci daya ya daga kirar Diyanan.

Shashshekar kukan ta yaji tana kirar sunan sa da Anwar kai wani irin mutum ne dabaka san mai son ka ba. Ina sonka baxan rayuba indai bada kai ba ,baxan iya xaman Aure indai bada kaine ba.kasani ina fada maka wannan mgnan ne har cikin zuciyata . Kuma ko wani hali kaji labrin ina ciki kasan cewa kaine sanadi ,walau rayuwata ko mutuwa .

Kirjin Anwar ne ya buga ,don tabbas yasan Diya duk mgnn dake fitowa daga bakin ta bada wasa ne takeyin shi ba . Come on my Diyana ,ki fahimceni plx ki dakat....ya isa Anwar nace ya isa...!!! Any thing u want to said you have oready say it before. Babu abun da xaka fadamun Anwar na yarda da kai . Kawai kalma daya ce ka fada mun kana sona kuma xaka Aure ni!!. Kai tsaye ta tsinkayi muryar Anwar yana cewa " Aa Diyana baxan Aure ki ba. Kawaii inn....kit taji ta datse kirar ,wanda ba tare da ya damu ba ya nufi kwataz din Barikin , don shi yana farin ciki ne a yau saboda kawai ganin Shatun nashi da yy cikin farin ciki .

Faduwa diyana tayi kasa ,wanda dai dai Ammie na shigowa falon nata ,cikin hanxari cike kidimewa ganin yar nata daya tilo a wannan mawiyacin halin ta nufota tana daga ta hadi da girgixata da ambaton Sunanta "Diyana!! Diyana!!!

Mu tare a night update💃💃
[08/02, 8:25 PM] Maman Teddy🧸: 🐄WLJM🐄
Uwar teddy🧸

*_BUZHUWA EMPHIRE🐪🐪_*
_Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa damu a cikin wannan taskar tamu ta buxuwa Empire ,sannun mu da shigowa hallarar mu ta buzaye🐪 . Ina kuke matan Aure masu fuskan tar kalubalen gidan Auren mu ,dan gane da mazajen mu...?? Ina yammata marasa farin jini💃💃 ,ga Buzhuawa emphire ta taho maku da sabon sirrika ,da yake abun sirrine sirrikar mallaka dana farin jinin yammata..akan sassaukar farashi duka mallaka da farin jini munayin shi akan 5k ne kacal. Idan na farin jini ne daya 3k,muna kuma bada sirrin mallakan akwai na 2k da 3k. Ga masu bukata xasuna iya tuntuban wannan number 08081202932 / 09062466409 ...siyan na gariii....??? Sai kun taho taskar buzhuwa xakisha mamaki da yardan Allah da annabin sa._

```Idan kin karanta baki biyani ba keda Allah ,haka kema idan kika futar mun ke da Allah.```
_________________________

"Duk kiran da Ammie kemawa Diyana ko motsi daga inda take ,girgixa ta take hadi da kwala kirar Driver yanda xai iya jiyota . Wata mai aikin tace ta taho da sauri tana fadin Hjy lafiya ?". Sam Ammie ta gaza magana sai salati da fadin sunan Allah da takeyi . Da kyer ta iya cewa "Kama mun ita mukaita Asibitin dake kusa ... Da taimakon wannan ma'aikaciya suka nufi da Diyana Asibiti .

*****

Bangaren Abbas kuwa Kaman yanda ya saba kirar Shatu duk dare don baya kashe wayan sa sai yaji saukar munsharin ta . Koda kuwa cewa tayi Ya Abbas zanyi bacci ,sai ya bata amsa da kiyi baccin ki kar ki damu kinji my luv. A hakan kullum ya sabar mata ,sai idan yaji alamun tayi baccin sannan ya datse kirar .

A yau ma hakan ta faru ,ya kira wayar yafi sau biyar yana jin tayi ringing ba a dauka. Kira da ta ishe Anwar ne yasa shi kai hannun shi yana duban screen din wayan . Wani irin murmushi yayi na bakin ciki da da tsantsan kishi , kamin ya daga hannu shi yana picking call din.

Hlo Me ya sameki dear kina lfy babyn yah Abbas??. Turus Shatu tajah ta tsaya don ya aiko Mama Shafa ta kirawota . Dai dai kuma ta shigo kunnuwan ta ya sauka a jin furucin Abbas wanda Anwar yasa Wayan nata a handsfree.

Kallon shi take tana ware ware idon ta fal tsoro ,nan taji Anwar yace " tana lafiyalau malam Boss . Duk wannan kulace gsky i really apreciated da na samu aboki kuma amini kaman ka. Ina godiya da kulamun da Flower ta da kayi har a yau na sameta sharrr abun ma sai wanda yaji...ya karke mgnan yana sakin ma Abbas wani dariya ta iskanci da shashantarwa . Don wannan mgnan da yayi ma Abbas ya fahimci komai abun da yake nufi wato yau yacika kudurin shi da burun shi akan shatun . Ya riga shi komai shi ya dade da shukar amma a lokaci daya ya girbe masa . Kamin Abbas ya ankara ne yaji har Anwar ya datse wayan .
Chapter 4 · 0% Book details