Sashe 8
Tawa Ta Sameni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gadon jina nayi sharkaf da lema ko ban duba ba na san jini ne na soma kuka yaynmu yazo ya rike min hannu ina ne yake miki ciwo?ban kula shi ba mama da Haj Maska suna min sannu nace Mama me yake zuba a jikina?ta dubeni yau me zan gani ni Habiba?wannan ai jini ne haka jini ya tsinke sai zuba kan kace kwabo har na fita hayyacina likitan kanshi ya rude da ganin jinin dake zuba daga jikina ya ma wani likitan waya yazo sun hadu su biyu a kaina suka ce su Mama da Yaynmu su fita,Yaynmu hankalinshi a tashe yama rasa me yake mashi dadi sai safa da marwa yake yi a kofar dakin tunanin shi in na mutu shine sanadi,dana sani da nadama kawai yakeyi dan da ya san hakan zata faru da bai bi san ran Hajiyan shi ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Awa daya,awa biyu,har awa hudu basu fito ba sai da aka kira magriba Mama ta matso gurin shi tace Abdulrahman kaji masallaci ana kiran sallah yace mmn Sagir ba zan iya salla cikin nutsuwa ba gara in sun fito sai nayi tawa,Mama tace ka daure ka je sai kayi addu'a kaji ko? Haka nan ya tafi ,yana dawowa sai yaci karo da Dr Salihi,yace yawwa Maska dama kai na fito nema ynxu mun shawo kan matsalar da kyar sai dai jini muke so leda hudu zamu duba,yaynmu yace a'a gani ka gwada nawa in yayi sai ku diba ko laida nawa kuke so Dr yace biyu zamu diba a naka yaynmu yace Allah duka za'a diba haka kuwa akayi Mama tayi ta yima yaynmu fada wai ya zai kwanta adibi jini har leda hudu?yace mmn sagir mu dai yi fatan samun lafiyarta haka aka sa min jini hannu biyu sai da na kwana biu bansan inda kaina yake ba sai da na farka jinin ya kare sai ruwa.Dishi-dishi nake gani ban san su waye a dakin ba, hasalima dakin shiru sai karar fanka a hankali idona ya soma washewa naga Mama da anty Yagana,sai Babana da Alhj, sai kuma Malam. Nakai dubana kusa da kaina Yayanmu ne daf dani da ganin shi yasa komai ya dawo min sabo a raina nace abin da kake so shi yake wahalar da kai,hawaye suka shiga yimin zarya sannan ne yaynmu ya gane na farka da sauri yace Iman kin tashi ne?ya kamamin hannu su Mama suka zo suna min sannu gami da yiwa Allah godiya,wasa wasa kwana na sha daya,Yau monday na fito wanka ina zaune a kan gado yaynmu ya shigo Mama da Haj Maska suka fita bayan sun gaisa ya dubeni Iman ya jiki?nace da sauki fuskata babu walwala yace iman ki min afuwa na san nine sanadin sakaki cikin wannan halin amma ki min hakuri bana son rasa ki ne shi yasa,ni dai shiru na mashi nasan duk dadin bakine yake min yanxu na gane in mutum yace baya sonka tun farko ba zai taba sonka ba,sai dai wani abu to shima yaynmu na gane albarkatun jikina kawai yake so ba wani ni ba dama nasan ni ba ajinshi bace shishshigi nayi Ya tabani Iman tunanin me kikeyi ne?na zame na kwanta hawaye ya soma min zarya abin da yafi bani haushi yanda har ynxu zuciyata take matukar son shi,har ynxu son na nan ba zan iya fdama wani ainahin abinda ya sameni ba,Likita ya shigo bayan dube dubene aka sallameni sun yanke shawarar Mama ta wuce dani gida don haka gida muka tafi shi kuma yaynmu su babana suka ce ya koma,ranar da zai tafi ya shigo tunda na gaishe shi ban kuma magana ba, ba yanda baiyi ba in yi magana naki daya matsa min sai na sa kuka, ya kifa kanshi akan gwiwoyinshi na dube shi duk ya rame a raina nace duk kai kaja ni ynxu don son da nake maka zanci gaba da zamada kai baya ga haka da sai dai ka sakeni ya mike to Iman na tafi sai kin jini a waya ko motsi banyi ba bare na tashi nace Allah ya kiyaye hanya yadan dubeni sai kuma ya tafii,Tunda ya tafi kullum zai min waya sau uku,amma daga gaisuwa bana kuma magana har mama ta gane sai fada take min tanacewa ai ba shi ne ya dora min ciwon ba in kuma cikine ai Allah ke badawa dan ya zube sai na zargi mijina.Na warke sarai jikina ya dawo nayi kiba mama tace na koma dakina nace nidai tunda Haj Maska ta koma Maska sai su yaynmu sunzo zan koma,watanshi uku da tfy suka dawo saboda zuwan watan Ramadan nan da sati daya, ina falo ina kallo naji ana masu oyoyo duk da son ganin yaynmu da zuciyata takeyi sai naki tashi,dakin Haj Yaya suka yada zango sai daga baya yaynmu ya shigo dakinmu, na dube shi kullum dai yana nan dan gaye dashi jikin nan sumul, yace gimbiya ina gajiya nace kunzo lfy,yace lafiya,ina mmn Sagir?nace tana Sallah mama ta fito suka gaisa da har nace ni ba ranar zan koma ba mama ta bude min wuta dole na bisu, Yaya Kabir yasa an gyara gidan an share shi,na zauna a falona ya shigo kusa dani ya zauna nayi kamar ban ganshi ba yace Iman kin canja min sosai yanzu ba kya kula dani kamar da shiru na mishi ya jawoni jikinshi tashi muje dakina mu kwanta nace kayi hakuri ba zan iya kuma kwana dakinka ba, yace kina hauka ne ko? nace ba hauka yace ya zaki ce ba zaki kwana dakina ba alhalin ina mijinki? nace yaynmu ina ganin girmanka kar kasa na gaya maka magana, yace gara ma ki gaya min dan shiru shirunki ya soma cutar dani ya cigaba ina matukar bukatarki ba zan iya jurewa ba, na soma kuka ina fadin dama nasan jikina kake so hakika iyayenmu sunyi kuskure da suka zata kaine zaka rikeni amana ashe ba haka bane....... Ya tare ni wayace miki ban sonki? fadin son da nake miki kauyanci ne kin gani in za kiyi magana ki daina kawo maganar so....da kana sona da ba kaini an cire min ciki ba ina son abina kila ma shi ne kadai kwaina a duniya tunda baka sona shi yasa baka son hada zuria dani,yace ba zaki gane bane shi yasa amma ynxu na yarda komai kika ce ki min afuwa nayi kuskure,shiru nayi mishi gami da shigewa bedroom. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Har azumi ya riskemu bamu jituwa da shi,yayi naki,karshe ma ya shareni,ina komai,girki da sauran aikace aikace, girkin ma nawa nakeyi tana na ta, kowa ran girkinta ta sama mijinta,duk da yaynmu yana kokarin ganin kar Mimi ta gane sai da ta gane,don haka take ta shigewa yaynmu gami dayi min kallon banza,yaynmu yayi siyayya irin na neman lada su gero,suga, madara ya aika kowanne gida,wato gidan mu da gidansu Anty Mimi kai harda babana,haka har sallah ta gabato ya mana siyayar kayan sallah ya sai ma yan uwa da abokan arziki sannan ashe ya biya musu ummara shi da Anty Mimi,ko ita ma bai gaya ma ta ba sai da abin ya gabato, murna ta dinga yi tana waya tana gayawa kawayenta da sauran danginsu,ni ko sai nayi kamar banji taba dama ranar nice da girki,yana shan ruwa a falona ni kuma na idar da sallah ya dubeni kiyi hakuri ba zamu je umra dake ba sai wata shekarar in Allah ya kaimu,bace Allah ya sanya alkhairi na tashi,da za su tafi yace komai na dangane da abincin sallah yaya Kabir zai kawo sannan ya bani kudi nace to ka san dai da sallah zani gida da gidan babana har gidan kawu malam ya dubeni ban ce ki fita ko inaba, haushi ya kamani, dama ina ciki gashi sai yayi ta jan Anty Mimi suna wani soyayya a gabana dan naji haushi ni ko sai na tashi na basu guri,na dubeshi gsky zanje yawon sallah tun da nazo gidan nan ban taba fita ba sai sanadin ciwo kusan shekara sai ka ce matar kulle yace tun da ba matar kulle bace ki je ai zan ji lbr na kara fusata nace ba fa siyana kayi ba hasalima ba gori ba ganina kayi kawai an kawo maka shi yasa kake wulakantani,yace Zauna ki gaya min me na miki? kuskure daya na san na miki kuma na baki hakuri ni nan da kika ganni kece mace ta farko bayan uwata da na taba ba hakuri kuma kin ki ki hakura dadin abin ba ke kadai gareni ba,abinda kike rowa ki jika ki sha ga tsinuwar malaiku da kin bari ma cikin da kike fushi kanshi da yanxu kin maida wani,raina ya kuma baci na shige bedroom ina kuka.Tunda suka tafi kullum sai yayi man waya wata rana in dauki wata rana na ki dauka, dama dady wajen Haj Yaya suka kaishi,ko shekara bai yi ba watan shi tara amma yana tfy.Da sallah ina zaune gida dan ma yan yawon sallah sunxo min sosai Jamila muna tare da ita tana tayani aikin sallah,shima yaya Kabir yazo da Zee dinshi,babana ya aiko min da kudi da kaji har da zannuwa ni da Anty Mimi har da Yaynmu ranr baba uwa tazo da yaranta biu sun min wuni, Mami da Amira rana daya suka zo min,mun sha hira har dare,ita bikinta bayan sallah da Gidadonta,Sallah ta wuce da kwana goma sha daya yaynmu suka dawo ko waya bai min ba ranar ina daki ina karanta littattafan da na ba Amira ta siyo min,na fito zani babban kicin ne sai naga mutane baje a falo,na tsaya ina mamaki araina nace lallai yaynmu,ya dubeni yace kin tashi?ko ba barci kike ba,ko tanka mishi banyi ba.Da daddare ya shigo ya kawomin tsaraba na ce ya barshi na gode bana so ga mamakina bai tsaya roko na ba yace to shi kenan ya dauka ya fita.Satinsu daya suka soma shirin komawa nace tab ai ko wannan karon za'ayita, tunda Anty Mimi ta gama makaranta to ita ma sai dai ta zauna amma barina jira ya kare dan wulakanci sai da ana