Sashe 3
Tawa Ta Sameni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bishi da kallo yana fita na fda kan gadon don murna da farin ciki sai na nemi ciwon ma na rasa kai a karshema durowa nayi na shiga bayi alwala nayo nazo nayi ta nafilfili ina ma Allah godiya daya sa iyayena suka zaba min abin sona,shiko daya koma dakinshi sai da ya gama komai na al'adar rayuwarshi sannan ya dauki waya ya kira layin Mimi ta dan jima tana ringin sannan ta dauka,lafiya?abinda ta soma tambaya kenan,ya baki kawo min lipton ba ne? tace Amarya ba sai ta kawo maka ba ta kashe wayar ya jima yana duban wayar shi mimi zata kashe ma waya?lallai ma, da kanshi ya shiga kicin din ya dafa ya fito bayan ya gama ya kwanta ya jawo filo ya rungume tsam a kirjinshi idanuwanshi a lumshe ido surar Iman kawai yake gani,gsky ya girgiza da ganin halittar kirjinta bai taba tunanin haka take ba wato shi wannan abu baiwa ce daga Allah ba shekaru ne ba domin ko yanzu tafiMimi kira duk da dai kirjin kawai ya gani ranar yayi baccin da ya jima baiyi ba tunda ya samu yarinyar daya jima yana so gashi tana da abin da yafi so a gurin ya mace duk biyun wato kasa da sama sai dai inda zai samu matsala yaya zai yi ya tinkareta da wani batu na bukata?a ganin shi sai girmanshi ya zube a idonta da wannan tunani yayi barci. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Da safe nayi wanka na gyara gado na share na goge inda yayi datti sannan na jona naurar saka turaren wuta na zuba nan da nan dakin ya gauraye da kamshi kwalliya na sha cikin atamfa yar Ghana dinkin riga da siket rigar fitet Breazier style gashi na na daure shi da ribon sannan na daura dankwali turare na fesa na koma falona na shiga kokarin hada TV,ban ji karar bude kofa ba sai dai naji sallama gabana ya fadi na juyo yana tsaye da Jeans baki da shirt,yayi kyau sosai na zauna kan kafet na ce ina kwana?ya amsa lfy ya jiki?nace naji sauki ya juyo tare da fadin zo nabi bayanshi har falo ya zauna kan kujera sannan yace shiga dakin Mimi ki gaisheta sannan kice tazo ina kiranta cikin tsoro na shiga tana kwance a kan doguwar kujera cikin ta ya tsufa girman falonta kamar nawa nace Anty Mimi ina kwana da sauri ta tashi ke!! Ta daka min tsawa ni ba antyn ki bace batun kwana kuma banganshi ba cikin tsoro na ja baya nace yaynmu yace kizo ban jira amsa ba nayi waje da gudu ya dubeni menene?nace am....ba komai yace to zauna nan ya nuna min kujerar da take kalonshi kusan minti goma sannan ta fito kusa da shi ta zauna tana wani cin magani yace kinsan tun dazu nace ki zo shine kika ki zuwa ko?ta kauda kai taki magana yace to dama nayi kiranki ne dan na gabatar miki da Amina wato Iman a matsayin yar uwa.....ta katse shi ni ba yaruwata bace ya ce to ya isa haka ni matata ce kamar yanda kike matata tace to kace dama can kana sonta munafunci ne kawai.....ya mike yanda uwata tace in aureki haka na aureki ke ma zabin mahaifiyata ce kin gane?wannan kuma ya nuna ni zabin mahaifina ce dan haka ba zabina a cikinku sai ku kula na san gaba kila na samo zabina. kuma kina cin albarkacin cikinki ne,ya fita gsky naji haushin abinda yayanmu yace ko da yake Anty Mimi ta fini jin haushin tunda ya ba da ita gabana. Da rana bala dryva ya kawo mana abinci inji Mama,yaynmu ya dawo lokacin ina kwance a kan kujera a falona na sake wanka na sanya material baki me zanen fararen fulawoyi ya zauna kan kujera na tashi zaune sannan nace sannu da zuwa yace yauwa na mike na shiga kicin na zubo mishi kayan ciki salat ma kadan na zuba mashi na hado da coke da ruwan cway na ajiye a gabansa nace mama ce ta aiko yace to kin ba mimi ne?nace a'a yace bari na kai mata wannan mamaki ya kamani a raina nace ita ba tayi ta bani ba sai ni na ce da saura bari na kai mata yace kawo dai na kai mata nace to na shiga na dauko na kawo mishi ya fita jim kadan ya dawo ina zaune shima ya zauna yana cin abinci yace kunna min TV nan na dubeshi nace ai ba'a hada area din ba sai dai kaset zan saka maka yace barshi sai da ya gama na kwashe kayan ya dan kishingida yace Iman kina jina?nace eh yace kar ki yarda na samu lbr kin ma Mimi rashin kunya sannan ki dinga yin abinci kullum kina bata saboda kinga tana da ciki sannan zansa Mama ta samo miki mai tayaki aiki kin gane ko?nace eh bama sai ka nemo mai aiki ba ni zanyi,yace shi kenan yanzu Babanki ya cika mana Store da kayan abinci gami da kayan cefane sai ki duba babban kicin duk abinda babu sai ki rubuta Kabir zai kawo nace to ya mike ya fita na bishi da kallo a raina nace dama nasan mai aiki zan zama a gidan nan. Yayanmu zaune a gaban Haj Yaya san da yazo ya sameta tana ta sunturi a daki abin duniya ya taru ya mata yawa, in da ta san danta zai auri matsiyaciyar yarinyar nan da bata kashe kudinta a banza ba gashi kuma abinda ya faru tana kishi da uwarta sannan yarta ta aure ma ta danta kuma wanda ta fi so; bazata yiwu ba ta ta tada masifa Alhj yace zai saketa in har ta sa dan nata ya saki Iman,ita kam ba zata iya hada zuriya da Habiba, ta dube shi wacce shawara ka yanke a kan yarinyar nan?gabanshi ya fadi yace to Haj ni ya zanyi haka Allah ya kaddara.....ta dubeshi haka ka ce?yace to ya zanyi ne Haj kina jin fa abinda Alhj yace ki kwantar da hankalinki bana son ace ta kaina kun rabu tace to naji amma sai ka min alkawari ba zaka kula yarinyar nan ba dan gsky ba zan so hada zuri'a da Habiba ba,yayi shiru na dan lokaci can yace to Haj shikenan? tace in har ka min haka shi kenan kar ka yarda ka saurareta dama kayi ta mata wulakanci in sun gaji suje su dakkota yace to duk zanyi tace to yawwa Allah yayi maka albarka,ya fito yana nazarin yanda zaiyi. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Shida daidai na yamma na gama dafa abinci gidan sai kamshi yake na zuba ma Baba mai gadi da direba na fita na mika musu,ina fitowa wanka akayi kiran sallah sai dana yi isha'i sannan nayi kwalliya, paper less nasa yellow nayi kyau sosai na fito yana zaune a falona nace sannu da zuwa yace yauwa kin kaima Mimi abincinta ne?a'a ban kai mataba na dauka sai ka shigo amma bari na kai mata yace kawo nan in bana nan kika gama ki kai mata nace to na kawo mishi ya dibar mata komai ya fita,nace kai auran mijin wata ko matsala, ya dawo zo muci ai naci yace shi kenan daya gama ya fita sai misalin tara ya min waya na dauka yace na dafa mishi lipton zai zo ya dauka na dafa mishi mai kayan kamshi da tafarnuwa kadan a falo na ajiye mishi na shige dakina na kwanta. Haka naci gaba da zama tamkar yar aiki kullum da safe inyi gyaran dakina da falona in gyara babban falo na hada Break fast na gyara kicin ban dai taba gyara mishi daki ba ban ma taba sanin yanda dakin yake ba,inyi abinci da safe da rana da yamma wataran ma har Anty mimi tace bashi take so ba yaynmu yace in sake mata wanda takeso, duk aikin da nakeyi bai taba damuna ba tunda na riga na saba saidai bai kai wannan ba kuma nasan lada nake samu batun kulani da yaynmu baiyi ba ko a jikina tunda dama ni tsoro nakeji.Ina da kwana shida su Anty Yagana suka zo suka kawo min akwatuna har na gurin Adams, yaynmu dai bai min akwati ba sadakima babana ne ya bada. shina na ashirin da hudu Anty Mimi ta tashi da nakuda cikin dare misalin karfe biyu Yayanmu ya kwankwasa min kofa na bude cikin tsoro yace nazo muje Asibiti Mimi batada lfy da sauri muka tafi ya uzzura min da na fito mu tafi gyale kawai na rufa a kan kayan barcina riga da wando shi ya kaita cikin motar sannan na shiga na riketa sai fizge fizge takeyi tana kuka takasako salati,muna isa aka shiga da ita dakin haihuwa,jim kadan suka ce ta kusa mu kawo kayan haihuwa inji likita, yaynmu ya koma gida ya dakko abubuwan da likitan yace mishi,sai shida na safe ta haihu,san da suka zo mana albishir yaynmu yana masallaci sai ni suka ce min an samu namiji murna na dinga yi na kosa yaynmu ya dawo sai da ya dawo sun zanta da likitan na tare shi da murnata nace yaynmu Anty ta haifi Baby boy da murmushi yace alhmdll ina take?nace tana ciki ina kallon likitan ni ya kura ma ido nurse suka fito da yaron ni na soma daukanshi kyakkyawa yana kama da yaynmu sai dai farin mamanshi ya dauko,yaynmu ya daukeshi yana mishi addu'a likitan ya matso yana taya yaynmu murna ya dubeni kema sai ki kokari kiyi aure ko kin samu naki babyn,duk da murnar da yaynmu yake sai daya gimtse fuska gami da cewa naje na zauna na koma kan benci na zauna can aka fito da Anty Mimi zuwa dakin hutu,can ya dawo ya sameni zaune fuskarsa a daure yace min na tashi ya kaini gida yaje yayi waya su Haj zasu zo, dama dan bai zo da wayoyinshi bane muna mota yace shi ne na fito da kayan barci dan wulakanci ba ko hijabi naxo ina ta dariya a gaban doc,nayi shiru to me zance?shine fa ya uzzura min na fito na fito