Sashe 11
Tawa Ta Sameni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tawa Tasameni3-03 Posted by ANaM Dorayi on 09:47 AM, 09-Jan-16 Under: TAWA TASAMENI __________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________ Mamidhaku da Aisha sosai cikin yan kwanaki, yau watan mu uku da zuwa kasar nan nayi kyau fata ta ta kara murjewa sai sheki da kyalli na keyi, komai na ya kara cika,na fito wanka na gama shafe shafena wani wando na sa iya gwiwa ya dameni,rigar bata kai cibi ba sannan wuyanta babbane dan duk albarkatun kirjina gasu nan a waje,ana gani irin kwalliyar da yaynmu ya fi so in yi mishi shi yasa baya shigowa da kowa sai ya shigo ya duba dan ya san ina mishi yanda yake son anina,ina kwance ina taunar cingam naji tsayuwar motar shi ta window na leka ya fito cikin blue din jc adidas da farin takalmi a kafarsa,ita ma motar kyakkyawa fara tas,samanta a budw daga nesa kamar ta wasan yara,ya sabo wata jaka adidas dince a bayansa, komai yaynmu yake yi ya amshe shi gashi mai kyau ina son guy din nan,tunanina ya katse sanda ya danna ,intercom na bude ya saki jakar yana kallona ni ko na juya na kuma juyawa a gabanshi nace nayi?ya rungume ni gami da fadin zaki kashe ni da salon gayun ki big gal,ina sonki nima na kankame shi nace nima ina sonka guy,muka nufi cikin gida,rayuwa kenan koda sunan wasa ban taba zaton yaynmu zai zama mjina ba. sai bayan babbar sallah muka soma shirin zuwa gida don bikin yaya Kabir Amira kam anyi nata, ban so bana nan ba sai dai alkawarin zanje yola gurinta Mun fita dan yin tsaraba kudin da yaynmu ya zube min har tsoro ya bani, nayi kwalliya cikin suit riga da wando na sa karamin hijabi mai tsayawa iya wuya yayanmu yace kinyi kyau sai dai ba in sadaukar da jikinga ga wasu, canja, dole na sa siket da riga na jeans blue,yace saka abaya na saka yace kai itama tana nuna jiki sai dai muje na ringa kareki nace kai yaynmu ka cika kishi,yace na ji ba komai. Mun yi tsaraba sosai sannan mun zaga sai gurin sha biu muka dawo,a cikin jirgi ina lafe a jikin shi kamar mage yace saura yan mintuna mu sauka a kano nace to waye zai kaimu KD?yace akwai jirgi da zai je daidai sanda zamu sauka sai mu shiga,na ce amma gidan su mMama zamu ko?yace a'a gidanmu zamu nace kai yaynmu kai guy kaga nayi missin din maMama,yace kada ki bata bakinki nace to ai da Aunty Mimi ne can kuke sauka sai ynxu na tuno da Aunty Mimi har gabana sai da ya fadi saboda tuno su da nayi,dana manta da yan matsaloli yace naji kinyi shiru ne ko da nike sauka a gidan dan saboda ke ne in ganki kawai amma ke sai ki boyewa ganina na dago ina dubanshi saboda ka ganni yace tabbas nace dama kana sona ne?yayi murmushi gami da kara rungume ni tsam! Kamar yanda kike sona muka yaudari zukatanmu ke ban san hujjar ki na kin gaya min ba amma ni hujjata na riga na cika baki gurin abokina bana son su min shakiyanci shi yasa naso kiyi karatun in kin girma sai in nuna ina sonki ,sai gashi kin nuna aure ki keso kika sa hankalina ya tashi(confession tym)karshe sanda na samu lbr sa ranar ku da Adams naje Umara na roki ubangiji ya bani ke, ya amshi adduata cikin sauki ya bani ke lokacin da na soma yanke kauna da samunki,na kara shigewa jikin shi nace nima sonka nake guy tamkar raina yace kar ki rainani kar ki ga rashin girmana nace yaynmu ba raini tsakanin mu sai ma girmama da ka kara a idona.Muna ta hira har muka iso, muna mota nace yanxu yayanmu gidan ka zamu wuce?yace kina ganin zan yarda nayi missing dinki? jikina ba zai iya kwanciya ba in har bake.Muna isa gidanmu yaya Kabir yasa an gyara mana gidan tsaf, Aunty Mimi bata gidan nayi mamaki ban tambaya ba bayan munyi wanka mun ci abinci da mama ta aiko mana sannan muka fito sai gida.Munyi murna da ganin juna na shiga gurin Haj Yaya ta tamke fuskarta ko kallona batayi ba, na kari gaisuwata na tash,i da daddare muka koma gida.Haka akayi bikin yaya Kabir,mun hadu dasu Mami mun rungume juna,Mami tana da tsohon ciki ta ce kai Iman me yaynmu yake baki ne?kinyi kyau kin zama big gal ga wani class na musamman da kika kara nace Mami kinyi fa gsky Nasir yana kula mana dake,muka shiga dakinsu Jamil,a nan take bani lbr rigimar yaynmu da Mimi, tayi mamakin da nace mata ban sani ba dan yaynmu bai gaya min ba,nace gsky naga bai taba kiranta a waya ba tun da muka je,Mami tace ki tashi tsaye ki dage da adduoi dan an ce suna nan suna shiga bokaye don su rabaku,wai kema da asiri aka aure ki wai duk abinda yayanmu ya ma Aunty Mimi ba yin kanshi bane asiri ne, nace su dai sun kasa gane kaddara, Mami na san ina son yaynmu so daya tak amma ban taba tunanin zan aure shi ba dan na san cewa koda wasa niba ajin shi ba ce,to da da yake Allah ya kaddara da aure a tsakaninmu ana saura kwana uku biki Adams yace ya fasa Allah ya sani ban taba shan wani abu ko zuwa gurin wani dan yaynmu ya aure ni ba,Mami tace na sani kin san abinda mutane yakeyi,zai dauka haka kowa yake, tace saima kin ga Mimin duk ta rame, nace sun sa kansu a uku ni ban ma ganta ba,Mami tace tana nan ban ganta ba sai a gidan amaryanan muka hadu,gabana yayi mugun faduwa amma na dake tana ganina ta tafi,Dady ma gurin mamanta na hange shi.Zaune yaynmu yake a gaban Haj shi tana yi mashi fada akan abinda yayi wa Mimi ta kawo kara har da cewa yau din nan nake son kaje gidansu ka bata hakuri ta koma in ba haka ba zaka sha mamaki zaka ga yanda zanyi maka, ai ka bata min rai na karshe ka daketa sannan ka tafi abinka ba waya ba aike,yace yo ya take so ne haj? Ya Mimi take so dani ne? baki fa san abinda take min ba banda ke Haj da kike tsakaninmu da tuni ta koma gidansu ta koyo tarbiya in dai tana son zama dani,ya cigaba ke kanki ki dubi jikina wannan zuwan nafi kiba yarinyar nan da kika tsana tafi kula dani fiye da yanda ba kya zato gashi tana bin dokata tare da girmamani duk abin da nake so tana min fiye da yanda na bukata sannan.....ta daka mishi tsawa kai!.....ni dai na gaya maka in ta maka ina ruwana?ni dai nace kaje ka mai da Mimi yace ai bani nace ta tafi ba tace bana son wani kwane kwane, kaje ka maida ita yace shi kenan baru inje wanka,Bansan abinda ake ciki ba ina gida na gama gayuna yaynmu ya shigo nayi sauri na tashi na tare shi ina fadin yaynmu ina ka shiga ne?yace naje gida hadamin ruwan wanka nace ina zaka? Ba ka yi wanka dazu ba yace to ai ynxu tadi zanje na rungume shi nace gaya min gsky?ya sha mur ana wasa da maganar aurene?Na fada kan kujera nayi shiru ya zauna kusa dani tashi big gal kar tace ta fasa aure in shiga uku, nayi kicin a zatona da gaske ne nace cikin shagwaba ni ba zan hada ruwan wanka da za'aje tadi ba na turo baki gami da cewa to menene bana maka?gaya min na dinga yi maka kaji?na fada ina dubanshi sai ya fita yana fdin to ni bari naje na hada nayi ina nan zaune sai gashi cikin tattausan yadi milk yayi kyau sosai na tashi da sauri na fisge key din motan na ruga uwar daki da gudu na wurgashi bayan gado ya biyo ni big gal ki bani key dina na shiga toilet na kulle na gaji da jira ya tafi.Ina girki duk raina a jagule na son ko wacce yarinya ce zata so yaynmu dan ba irin mazan da za'a kisu bane shi kam wancan lokacin yana gidan su Aunty Mimi, bayan ya faka da mota sai ya kira ta a waya sau uku tana tsinkewa sannan a na hudu ta dauka yace ke ana miki waya kin ki dauka kar ki raina min hankali fa,tace gidan bakonka ne da ba zaka shigo ba?ta kashe wayar yayi kamar ya juya sai kuma ya fasa dan ya tuno da Haj, yasa kai cikin gidan tana zaune a falo ddy yana barci a kan carpet,Haj Laure tana waya,ba wanda ya amsa mishi sallamar da yayi ya sami guri ya zauna,Mimi tski kallon inda yake a karshe ma sai ta tashi tayi ciki abinta ya dubi Haj Laure yace momy ina wuni? fuskarta a murtuke ta ce lfy lau ,yace momy nazo ne mu tafi gida da Mimi, tace eh da yake babyn wasan yara ce Mimin dole kace haka to ba zata koma ba sai naji dalilin duka da kana son ka tafi da gimbiyar taka ai ba sai ka daketa ba in kace ba zaka bita ma ya isa yace momy kar ki tsaya dawo da abin daya wuce kuma zagina fa tayi ai ko kina gurin kya ce na ladabtar da ita tace karya ne kace ta zage ka, kai dai kaje kaida Allah batun komawa kuma ba zata koma ba, yayi shiru yana tunanin yanda zaiyi shi dai yana son cika umarnin Haj shi ne yace momy kiyi hakuri dan Allah ba zan kuma ba jin haka sai tayi zaton aikin Malmin nasu ya cine,dama yace da kanshi zai zo yana bada hakuri kuma komai suka ce yayi musu zai yi masu,koda Haj Laure ta tuno da wannan kuma ta ga abinda ya faru(yana bada hakuri)sai tace mishi ko zata koma tana bukatar kudaden da zatayi gyaran daki,yace ba matsala zan bata tace to sai ka aiko da kudi in an gama gyaran gidan ta koma yace shi kenan zan zo anjima ko gobe na kawo,ya fita ranshi a bace ya tafi,yana mota Haj shi ta mishi waya wai ya dakko Mimin?yace sunce sai anyu mata gyaran daki ta ce sai ka