Sashe 1
Tawa Ta Sameni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tawa Tasameni3-01 Posted by ANaM Dorayi on 09:01 AM, 07-Jan-16 Under: TAWA TASAMENI __________ NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________ Tindaga nan bansan inda kaina yake ba sai a Rimi Clinic lokacin ma bayan magriba ne na farfado,Dakin dam da mutane, Babana shine kusa dani yana rike da hannuna,ina farfadowa shina soma gani na shiga 'yan dube dube ina kokarin tuno me ya faru?Babana ya dubeni sannu uwata ya jikin?duk yan dakin kowa ya shiga yi min sannu,hannuna na daga zan share fuskata sai naga lalle sai na tuna ashe fa ni Amarya ce nan take na tuna mai ya faru da sauri na tashi zaune nace Babana kaji abinda Adams yayi min ko?yace ya fasa aurena, babana ya rungume ni kiyi hakuri kar ki damu,sai a sannan na dubi mutanen dakin Alhajine da yaya Kabir da yayanmu sai Mama da Aunty Yagana nace ashe har su yayanmu sun iso dako Adams yace min tare zasu zo sai kuka ya kwace min babana da Alhj sai lallashina suke mama kam cewa tayi saiki yi tayi tunda yace bai sonki dole ne?cikin kuka nace mama yace har yanzu fa yana sona saidai ba zai aureni ba kila ma yana tsokanata ne,na dubi yaynmu nace dan Allah yayanmu tare kuka zo?harara ya sakar min sannan yace kiyi wa mutane shiru ynxu da kike magana gobe ne daurin aurenshi a yola can garinsu kuma iyayenshi sun. bada hakuri dan da yarinyar suka so ya aura yaki tashi daya yace yanajin inbai auri yarinyar ba mutuwa zai yi ina ganin shima ba laifinshi bane da akwai wani abu,mama tace ba komai Abdulrahim wulakancin shine kawai dan cin mutunci sai da ya bari ana saura kwana uku biki sannan zai ce ya fasa ga shi mun gayyaci mutane ya zamuyi kenan?ai gsky abinda Adamu yayi mana sai dai muce Allah ya saka mana,Babana yace ku dai ku yi hakuri ynxu mu samu kanta in yaso sai mu san abin yi,da sauri nace yawwa Babana don Allah ku taimaka min ku shawo kan Adams ina sonshi, Mama ta kawo min duka Alhj ya tare har suna hada baki shida babana suna cewa Habiba haba menenebna duka?shi ko yaynmu fita yayi, jim kadan sai ga su Doctor yace ciwona bai tashi ba na dai firgita shi yasa amma a guji tashin hankali dan haka ynxu ya sallameni,mun fito kan titi gurin da suka ajiye motoci Alhj yace na shiga motar nace ni ba zani can gidan ba baba yace to muje nan ma nace a'ah,mama haushi ya kamata tace to ko gidansu Adamun zakije?sai kin dawo nace ni Anty Yagana zan bi Alhj yace to kuje,ya dubi yayanmu yace kai su Abdulrahman,a mota ina jikin Anty Yagana a kwance shi kuma yana tuki Anty tace Abdulrahim yaya abokinka yayi mana haka?yace anty ni kaina na rasa gane kan abin jiya fa muna tare da shi bayan mun tashi daga wani wasa wanda dama ranar zamu gama yau mu taho gaba daya da abokanmu dan har na ma Kabir waya akan ya kama mana Hotel zamu sauki baki a jiyan da daddare sai ga shi wai shi Ghana yake son zuwa ya je yaga Aisha,nace wacece kuma Aisha?sai yace yarinyar nan da aka ce ya aura yaki yanzu kuma ita yake so,da kyar ya kai safe, yau da sassafe ya dau hanya babanshi ya min waya wai ko da wata matsala ne tsakaninshi da Iman?nace ba komai shine babanshi yace to ynxu yace yau ya ke son ya auri Aisha ba sai gari ya waye ba koda suka ce a'ah su ba zasu yi karanta ba sai ganinshi sukayi ya fadi sumamme shine fa ba shiri suka dau hanyar Yola,Babanshi din yace in sun dawo zasu zo nan su bada hakuri.Jin wannan lbr sai wani sabon kuka na saki dan lokacin sai naji wani son Adams din ma nakeyi,yaynmu ya daka min tsawa yi mana shiru ko na tsaya na bubbuge ki, wannan bakin ya yi tsit nayi shiru har mukaje gidan anty yagana. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Washe gari ina kwance anty yagana ta shigo ta dubeni tashi Iman kiyi wanka ko kya ji dan dadi nace dan Allah anty ya zanyi wannan lallen ya fita ne?na tsaneshi tace ba zai fita ba sannan ke da kike Amarya ya za'ayi ki goge lalle da sauri na tashi Adams din ya dawo yace zai aureni ne?Anty tace ni dai ban sani ba Babanki da Alhj sun ce a ci gaba da shirye shirye biki ba fashi sai dai ina zaton ba da Adams din ba ne nan na koma na kwanta na dora sabon kuka nace TAWA TA SAMENI ni iman aure ban san mijina ba?na shiga uku,Aunty yagana tayi ta bami hakuri gami da lallashi.. Ashe abinda ke faruwa shine boka yayi aiki sun hada Adams da aljani ya juyar mishi hankali dan haka da suka samu lbr zancen aure ya rushe da Adams sai murna da farin ciki hatta Aunty Mimi tayi murna dan dama tace bata son in auri Adams dan kar mu zama abokai,a cewarta in auri abokin mijinta taci baya(hahhhah lallai a gaisheki mimi)ita tana auran mai kudi nima na auri mai kudi ba zai yiwu ba..Zaune gaban boka Haj Yaya ce da Haj Laure suna murna gami da godiya boka ya katse su to ynxu kunsan wanda za ta aura ko?Haj yaya tayi sauri tace duk ma wanda zata aura Allah gafarta boka taje ta tayi ta aura tunda dai ta rabu da abokin dana ai shi kenan dama bani son ta rabu dana kusa da dan nawa ne bare shi kansa,ta cigaba dan haka tun da duk kanmu....Haj Laura ta karasa da cewa ya fada kan kowa,sun bashi kudi da alkawarin in wata matsala ta taso zai gansu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Yaune juma'a kuma yaune lunchn,nace ma anty yagana nifa ban san wanene mijin ba anty yagana tace inje don kada mutane su gane halin da ake ciki tun da ba kowa ne ya sani ba ki kwantar da hankalinki Babanki yaba Alhj damar ya fidda miki miji a cikin kwana ukun da suka rage shi kuma ya fitar miki da miji dan gaske ki dauka haka Allah ya tsara,cikin kuka nace Aunty wanene?tace nima ban sani ba dan ko mamanki bata san kowa ye ba sai dai tace tasan ba zai miki mugun zabe ba shi yasa ma kikaji nace dan gaske.Ina ji ina gani ta shirya ni suka zuba min dubai less da gwala gwalai nace anty ni dai kayan Adams ne ku cire min,tace a'a ba nashi bane ai ke yar gata ce wannan cikin kayan da babankk ya hado maki ne daga dubai sannan mamanki da Alhj sun maki gwala gwalai shima Adams ya bar maki akwatuna,dan haka in kinje gidan ango sai kiyi ta kwaliya,na share hawayen idona,Anty Saudatu ta miko min kayan shafa nan na kuma yin wata kwaliyar. Gurin lunchn yayi guri ko ina ya tsaru mutane kamar kasa har abin ya bani mamaki ni da kawayena muka hau high table shalele ya cashe sosai su Mami da Amira da sauram kawayena sun yi min kara wajen buga abubuwa,na sha liki gurin dangi da yan uwa sun min liki baran ma Kabir har nace a raina kodai da Kabir din aka hadani ne?yaynmu ne ya bani mamaki ko leke duk yanda muke dashi shine ko yazo bikina niko a na shi nayi rawa nayi tsaki ba komai duniya ce.Bakwai aka tashi daga gurin lunchn, gidansu Anty Yagana muka koma kuma can aka min kamu sai dai banga dangin miji ba kamar yanda naga ana yi a al'ada Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/? _e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347 Washe gari daurin aure tun safe direban babana yaxo ya daukeni ya maidani gidan Babana nan na samu gidan cike da yan garinmu har da tsohuwa jikinta na fda na soma kuka tace kuji mun sakarai ai ni murna nayi da dan Ball yace baya yi dan Allah ya sani tunda akace Adamu Ball yake sai naji bana sonshi ynxu da babnki ya mana bayani yace ya fasa nace gara haka kila ma yace ba zai iya rike ki bane yace ba yayi tunda Ball ai ba sana'a bace, duk da halin da nake ciki sai da na yi murmushi a raina nace to shi wannan baki san ta sana'ar ba kila ma gara Ball.Karfe biyu gidan babana ya soma cika da yan daurin aure niko ina can dakin Babana na kudundune sai kyarma sanyi nake zazzabi ya rufe ni ba wanda ya san inda nake ban sani ba har an daura aure su Amira sunzo muje gurin sai nemana ake gidan cike yake dam da jama'a can babana ya shigo bedroom dinsa yana cewa bari ya karoma baki dabino sai ya sameni kwance ina ta rawar sanyi da sauri ya iso gurina,uwata menene?dama kina nan?ya dago ni jikina zafi rau ya shigo falo ya shiga kiran Anty Maijidda a waya data zo yace mata gani nan ba lfy shi kuma ya fita ya sallami baki ya dawo,Anty Maijidda ta dagani ta zaunar dani ta dubi babana tace to baban Iman ya za'ayi ynxu?ga gidan dinke da mutane ko zaka kira likitan mu ne?yace a'a bari na kira wata likitar kin san tana da matsalar zuciya ya dubeni kin san number Doc dinki na girgiza kai alamar a'a yace to bari na kira yaynku ai shi yana da no dinsa ko?nayi alamar eh,ya shiga neman layin yaynmu Anty Yagana ta yowa Anty Maijidda waya wai inzo yan walima sun soma zuwa Anty Maijidda tace yagana ga Iman nan kwance babu lfy ynzu ma likita muke kira,Anty Yagana tayi salati tace gamu nan zuwa babana ya samu yayanmu ya sanar dashi yazo da likita gani nan ba lfy yayanmu cikin rikicewa yace ba dai ciwon ta bane ko,babana yace shi yasa nace kazo da liktan ta dan kar abin yayi nisa,jim kadan sai ga yayanmu shida likita daga dakin babana aka daukoni zuwa falo kan doguwar kujera aka kwantar dani