← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Bance komai ba na k'ara matse ta ina kuka sosai. Ban damu da idan Moha dake tsaye bayana saida Gwagwo ta janye ni daga jikinta da sauri ta shiga d'akin tana kiran Baba da har zuwa lokacin bai motsa ba. Barci yake mai tsananin nutsuwa da wani irin annuri da murmushi kwance kan fuskar sa. Numfashi naji Gwagwo taja mai k'arfi murya tana d'an rawa ta juyo ta kalleni kafin ta mayar kan Moha dake tsaye har zuwa lokaci.

"Kira Likita Muhammadu "

Bai musa ba ya juya da sauri ya fice Gwagwo ta juyo ta rungumeni sosai cikin k'irjin ta tana faman maimaita Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Rikicewa nayi na d'ago ina kallonta nace

"Gwagwo menene? Ko na tashi Baba ne ya ganki?"

Kai ta girgiza " barshi ya huta Jadwah. Yana samu hutun da bazai k'are ba"

Cikin rashin fahimtar maganan ta naja doguwar ajiya zuciya. Dr ne suka shigo da sauri da Moha. A hanzarce naga ya yi kan Baba yana tab'a k'irjin sa zuwa hannun sa kafin yasa abunnan kaman dutsen k'arfe ya fara tab'a k'irjin sa dashi. A yanzu na fara gane inda maganan Gwagwo ta dosa k'irjina ya fara wani irin harbawa da k'arfi numfashi ya faramin wahalar fita. Banyi zato ba naji wasu hannu masu tsananin laushi da kauri suka sauka kan kafad'ata. Luu nayi baya sai jina nayi cikin faffaɗan k'irjinsa. Muryar Gwagwo naji sama-sama tana salati Dr na cewa a fita dani daga d'akin. Cak naji ya d'auke kaman y'ar tsana ya yi waje dani daga nan idona suka rufe ruf.

"Muhammadu "

Gwagwo ta kirashi tana nufo inda yake tsaye bak'in gadon daya kwantar da Jadwah ana mata k'arin ruwa. Baisan wane irin yanayine yau yake ciki ba. Abubuwa da bai tab'a zato ba sun had'u sun chunkushe. Har yanzu he don't even know what his feeling a kanta .bai sonta haka kuma bai k'inta. Bazai tab'a iya watsawa mutum kaman Baba dake neman alfarma ba wajen sa yana kwance kan gadon tafiya Alfarma da yake nema gurinsa. A ganinsa karb'an wannan alfarmar da ya yi ,ya yi ta ne saboda abunda ya yiwa Baba. Gani yake amincewa da buƙatar Baban ita ne zaisa ya daina saka masa da rashin kunyar da ya yi masa. All this is to much for him. Asiya da Balaraba na can sun tada fitina tun da sukaji abunda ya faru. Asiya sai hauka take , Balaraba kuwa Alhaji Balarabe tasa a gaba tana gaya masa duk irin bak'ar maganan dake fitowa daga bakinta. Daya gaji da masifar ta yace mata

"Idan har kina insisting kan wannan abun daya faru saboda munyi taimako. To ki sani yanda ki ka ce ya aikata abunda ki ke umarta ce shi, itama Asiya hakan ne zai faru a gareta. So choose wisely"

Shi kanshi Balarabe matsanancin mamakin mayar mata da martani da ya yi yake ,bare Balaraba data zuba masa ido cikin matsanancin mamaki baki a hangame tana kallonsa. Yau ita ne take magana Balarabe ke mayarwa?. Kafin tayi wani yunƙuri ya fice daga falon gaba d'aya. Tsayawa ya yi bak'in k'ofar yana sauke wani irin numfashi. Ji yake kaman an yaye masa wata jijiya data d'aure masa harshe. Zai k'ok'ari yaga ya taimakawa Moha wajen ganin sun riƙe wannan amana da aka basu. Jikinsa na bashi kasancewar yarinyar da Moha babban alkhairi ne a garesu.

K'afad'ar sa Gwagwo ta d'an dafa tana cewa

"Har yanzu bata farka ba Muhammadu?. Y'an uwa kowa yana son ya ganta. "

A hankali yace "eh Gwagwo "

Numfashi taja ta cigaba da cewa" yanzu ya batun wannan magana. Da wane ido Jadwah zata d'auki wannan batun?"

Juyowa ya yi sosai ya fuskance ta yace

"Kiyi hak'uri Gwagwo amma ban shirya sanar da ita hakan ba yanzu. Bazanyi miki karya ba Gwagwo dagani har ita babu wanda yasan yanda d'an uwansa ke cikin ransa. Tabbas ita d'in amana ce a gareni kuma nayi alk'awari riƙe ta na tsawon rayuwata. Amma nida da ita muna buƙatar lokaci da zamu koyar da zuk'anta mu san juna har ya kaimu ga zama inuwa d'aya "

Murmushi Gwagwo tayi na manta "kana nufin na tafi da ita can Jordan ko A'a "

Wani irin shaking voice ya sauke a hankali yace

"Ina ganin hakan shine best dayafi dacewa. Muna buƙatar mu fara koyar da zuk'anta mu son juna. Zanyi k'ok'ari na koyawa kaina sonta kaman yanda zan koya mata sona"

" ni nasan kai yaron kirki ne kuma tabbas MUSTAPHA yaga hakan tattare dakai har ya iya damka maka y'ar tsa guda d'aya tak da duniya ta sheda so da kauna da yake mata. Ubangiji ya taya mu rik'o baki d'aya. "

A hankali ya amsa da Amin kafin ya juya ya fice daga d'akin. Kai tsaye gida ya nufa. Tun daga bakin gata ya hango Isma'il dake safa da marwa bakin gate rai a matuƙar bace. Numfashi yaja ya fesar ya tsayar da motar yana kallo Isma'il daya nufo shi kaman bijimin sa. Wani irin buga glass d'in window d'in ya yi yana maga da kumfar baki.

"Har ka isa kaci amanata. Wlh baka isa ba Jadwah tawa ce. Baka da right a kanta. Nike sonta kuma ni zan aureta. "

Kallo ya watsa wa Isma'il dake huci baice komai ba ya buɗe motar ya fito rai a matuƙar bace. Gate d'in ya buɗe ya koma mota ya shige gida. Isma'il ya biyo shi yana ihu. Hayaniyar Isma'il ta fito da Asiya da Balaraba da suke ta fama da ita saboda kuka da take ta rusawa. A hankali suka yo kanshi ya k'ara sauke wani ajiyar zuciyar kafin ya wuce ya yi b'angaren sa. Yana shiga suka shigo.

"TAHEER "

Balaraba ta kirasa da ainihin sunan sa na yanka. MUHAMMAD TAHEER. sunan mahaifin mahafiyar sa. Chak ya tsaya tsakiyar d'akin kafin ya juyo yana kallonsu fuskar na a turb'une.

"Wane irin magana nake ji haka?, wane irin cin mutunci ne wannan?wannan mara mutuncin mutumin duk irin kyautata masa da muke a gidan nan da abunda zai saka mana dashi kenan?, kuma ka amince da hakan saboda tozarci?"

Rai a matuƙar b'ace yake kallonsu baice komai. Balaraba ta cigaba da tsananin b'acin rai

" in har na isa da kai na baka umarni ina so yanzu nan ka cika shi"

"Are you done?"

Baki suka hangame Asiya ta k'ara rushewa da kuka. Wai what is happening ne? Mene ya jawo wannan SAUYIN? mene tayi ba daidai ba?.

"Idan har kina so nayi abunda ki ke so. Zanyi but da sharad'i she needs to go itama. I don't care if we just get married "

Ya k'arasa maganan yana jifan Asiya da wani irin kallon tsana. Gunji kuka kawai take Balaraba ta zuba masa ido cikin matsanancin mamaki abunda ke faruwa. Matsawa ya yi ya d'auki y'ar takarda daga cikin memo nashi ya ciro biro daga aljihun wandonsa. Wani irin kururuwa Asiya ta saki ta nufo shi aguje ta riƙe hannun tana kuka sosai . Baki Balaraba ta cije idonta ya yi wani irin ja na tsantsan bacin rai kafin ta juya fuu ta fice daga d'akin. K'ara riƙe shi Asiya tayi

"Na amince zan zauna. Kar ka sake ni don Allah "

In all honesty ya yi wishing su amince da sharad'in nan nasa ko ya saukewa kansa wannan nauyi. Numfashi kawai yaja ya fisge ya shige d'aki ya barta a nan. Zama ya yi gefen gado ya dafe kansa. Yanzu yake dana saninsa na zuwa Nigeria. He wish bai dawo ba wata kila da duk wannan dramn baza ta same shi ba. Shi kansa baisan mene ya dawo dashi ba in the first place. Suna ta hauka kan yarinyar da batasan menene ke faruwa ba. In all honesty shi kansa baisan mene zai faru ba next. Ta ina ma zai fara?.

A guje Asiya tayi b'angaren su ta sami mummy nasu da Suwaiba suna magana rai a matuƙar b'ace. Allah kad'ai yasan irin abunda ke cikin ran Suwaiba. Bak'in ciki da bacin rai abun har yafi na Asiya da Balaraba. Duk da haka bata cire kudurinta ba gani take hakan ma wata damace da zata cimma manufarta ta hanyar amfani da Asiya. A guje tayi wajen Mahaifiyar ta da tayi bene tana k'ok'arin kiran waya gabanta tasha tana nunata da hannu tace

"Laifin ki ne. Tuntuni saida nace ki sallame su ki ka k'i. Wlh in har ya sake ni sai nayi abunda sai ran kowa ya b'aci a gidan nan"

Tas Balaraba ta d'auke ta da mari tana huci. " ni zaki dinga yiwa maganan banza?. Kin fini jin zafin abunda ya faru ne?"

Da k'araji Asiya da bak'in ciki tace " eh na fiki. Yau rana ce ta farin ciki a gareni amma ta zama ranan bakin ciki saboda ke. Saboda kinsa cin masu gadi a gaba baki d'auki maganata da muhammanci ba. Ko kin d'auka bansan dirty little secret naki ba na kwanciya da masu..."

"Asiya " Balaraba ta kirata da wani irin k'araji ta kai hannu zata d'auke ta da mari Asiya ta riƙe hannun. Ita kanta bata san me yazo kanta ba da k'arfin ta gaba d'aya ta hankad'a Balaraba . Ihun Suwaiba dana Balaraba baisa Asiya taji d'ar abunda tayi ta ba, ta zubawa maifiyarta dake wuntsulawa kan bene tana huci. Gani take duk laifin tane. A guje Suwaiba ta tare Balaraba data sume saboda buguwa da kanta ya yi .

Fuuu Asiya ta wuce d'aki tana hucu. Suwaiba tayi saurin kira suka fita Balaraba daga gidan cikin gaggawa. Isma'il shima tuni ya fice daga gidan ya yi mashayarsa dake cike da y'an matansa.

Kwana d'aya Moha bai k'arayi ba a gidan ya bar gari bayan ya k'ara zuwa wajen Jadwah da har zuwa lokacin bata farfado ba. A daren ya shirya su gaba d'aya suka bar azare. Shi ya wuce UK wajen mahaifin sa daya rigashi tafiya. Jadwah kuma suka wuce JORDAN da Gwagwo.

Bayan kwana biyu.

Lokacin dana farka a gigice ina kuka da kiran Baba. Gwagwo ta shigo da sauri ta rungume tana lallashi. Ina kuka sosai nace

"Gwagwo ya mutu ko?"
Chapter 9 · 0% Book details