Sashe 8
Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read
Turus na tsaya ina kallon Big Brother dake durkushe kusa da Baba. Tuni raina ya b'aci tuna irin nakastamin mahaifi daya so yi daran jiya. Da sauri na k'araso ina jifansa da mugun kallona na tsana da k'iyayya. Kusa da Baba na tsaya don yasan shirye nake na k'ara zuba masa wasu marukan idan har ya yi niyar k'ara cutarmin da mahaifi. Daga shi har Baba murmushi naga sunyi kafin yana kallona da wani abu cikin kwayar idonsa dana kasa gane shi. A hankali naga ya miƙe tsaye still idonsa na kaina cikin zuciyata sai d'ura masa zagi nake . Ido muka k'ara had'awa dashi ya had'e leben sa guri d'aya kafin ya juya a hankali bayan ya yiwa Baba sallama ya wuce na bisa da muguwar harara. Muryar Baba ta katsemin tunani nayi saurin d'auke ido daga kan Moha dake nufar sashen sa
"Har anyi markad'en ne"
"Eh Baba bari na fara soya mana rana nayi"
Ina maganan ina k'ok'arin juyawa kan barandar mu. Wajen juyawar ne idona ya kai k'ofar d'akin Moha. Yana tsaye jikin k'ofar hannun sa kan murfinta amma idonsa na kaina. Baki na cije irin na ban haushin nan na watsa masa harara lebene na motsawa a hankali 'mashayin Banza da wofi' . D'an murmushi naga ya yi ya buɗe k'ofar sa ya shige naja d'an k'aramin tsaki. D'aki na shiga na ajiye hijabi na saka k'arami kafin na fito na d'ura mana kosai da kunun gyad'a.
Kwana biyu tunda nazo na same shi tare da Baba yanzu yana yawan fitowa wajen barandar sa ya zauna. Wani lokacin haka zan kamashi ya kafeni da ido kaman bak'in maye. Duk irin harara da k'ananan manganu da nake jefe masa masa baisa ya daina kallon nawa saima murmushi da zakaga ya yi, hakan kuwa ba k'aramin konamin rai yake ba. Muguwar tsanan sa na k'ara ruruwa cikin raina. Ga Amina tun ranan data tafi take kwance wai babu lfy ta d'urawa kanta wahala zata hallaka kanta a banza a wofi. Ita kanta matar tashi da zai aura kar kuga irin sintiri da rawar kai da take sashen sa, haka zata fito wani lokacin tana kuka. Jaraba kenan.
Ance rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya. Satin bikin Moha da Asiya ya gabato. A gobe juma'a za'a d'aura aure. Yau tun safe nake safa da Marwah bak'in gate. K'afafuwa sunyi kugin gajiya. Amma duk da haka na hana Baba tayani. Har fad'a saida ya yi mun nayi mirsisi dashi. A daren yau na alhamis na farka k'arfe d'aya saboda nishin Baba da nake juyowa daga d'aki da gudu na fad'a d'akin nasa na sameshi akwance cikin wani irin mawuyacin hali. A guje nayi kansa na rungume ina kira. Saboda hannuna kawai ya iya riƙewa cikin mawuyanci hali numfashi na masa wahalar fita. Wani irin kuka na saki na miƙe a guje na fito nayi sashen Hajiya Balaraba dake dake cike da bak'i . Duk da cewa dare ne hayaniyar su ta cika gidan ta ko ina. Jiki na rawa na hau buga k'ofar ina kira cikin matsanancin kuka. Saboda ihun su da hayaniyar su basuji bugun ba. Hankalina duk ya tashi na rasa inda zanyi a guje nayi b'angaren Moha. A haukace nake bugu ina kira kaman tab'abbiya. Babu zato aka buɗe k'ofar Moha ya fito sanye cikin kayan barci doguwar riga da wandon ta mai mad'auri. Ido ya d'an ware cike da matsanancin mamaki yana kallona. Ina kuka sosai na fara k'ok'arin yi masa magana muryar Asiya ya katseni
"Honey waye?"
Ido na zubawa Asiya data bullo ta bayansa sanye da kayan barci. Saurin kyifta ido nayi ina girgiza kai na juya da sauri zan bar gurin. Babu zato naji an rik'o hannuna . Wani irin shock ya ratsani ba juyo a razane ina kallin hannun Moha dake riƙe da nawa kafij na mayar kan manyan Blue eye's nashi daya kafeni dasu. Da wannan deep voice nashi yace
"What happen?. Menene?"
Tuni na manta da Asiya dake gefensa tana jifana da wani irin kallo, bare na tsaya tunanin abunda take sashen sa yanzu da daddare. Muryar ta na wani iri rawa nace
"Don Allah a taimaki Babana bashibda lfy"
Ido ya d'an ware damuwa naga ta bayyana kan fuskar sa kafij ya wuceni da sauri ya yi b'angaren mu na bishi da gudu. Ina jin Asiya na kiransa da wani irin b'acin rai.
"Moha ina zakaje?"
Dagani harshi babu wanda ya juyo inda take .ya rigani shiga d'akin mu. Yanda muka iske Baba na k'ara rushewa da wani irin matsanancin kuka don yanzu da kyar yake fisgar numfashi. A hanzarce Moha ya ciccibi Baba muka fito ina kuka sosai . Muna fitowa ya bawa d'aya daga cikin masu tsaro ya d'auko masa mukullin mota. A guje ya shige b'angaren sa bai jima ba ya fito da gudu da mukulli a hannun sa. Motar Moha ya buɗe ya saka Baba a ciki na zagaya jiki na rawa na shiga na rungume Baba. Ina jin ya fisgi motar a guje ya fice daga gidan.
Har mukaje asibiti kuka nake rusawa rungume da Baba da yanzu jikinsa ya saki gaba d'aya. Sai ka k'asa kunne sosai kake jin fitar numfashi sa. A hanzarce Moha ya faka motar ya fito da gudu ya zagayo inda nake riƙe da Baba ya sureshi ya yi cikin asibitin da gudu na rufa masa baya. A gaggauce aka karb'i Baba zuwa emergency. K'ofar d'akin na durkushe ina kuka sosai. Motsin mutum da naji gefena yasa na d'ago a hankali na kalli Moha dake durkushe kusa dani kaman yanda nayi. Numfashi ya sauke fuskar nan tashi d'auke da damuwa sosai kanta. Saurin d'auke ido nayi daga kansa. Har yau ban manta abunda ya yiwa Mahafina ba. Mun jima a durkushe k'ofa d'akin har sama da awa d'aya kafin likita ya fito . Da sauri na tashi nayi kansa jikina na rawa. Wani irin kallo ya watsamin na tsantsan pity kafin yace
"Ki shiga yana buƙatar ki. Kece Jadwah y'ar sa ko?"
Kai kawai na d'aga na kasa cewa komai saboda kuka dake cina. Da kai ya min nuni na shiga. A guje nayi d'akin da suka kwantar da Baba. Yana kwance kan gado cikin d'an k'ank'anin lokaci ya lashe ya yi wani fari kaman wanda bashi da jini a jiki. Ina gunjin kuka na na rungume Baba dake murmushi na tsantsan ciwo. Da kyar ya d'aga hannu ya rungumeni. Murya a shak'e yace
"Yi shiru ki daina Kuka. Naji sauki "
Sosai na k'ara matse shi ina kuka sosai. Ina ji aka buɗe k'ofar d'akin aka shigo. Ban damu da d'agowa naga waye ba na k'ara matse Baba ina sheshshek'a. Bansan ya akayi ba barci ya yi awon gaba dani na tsantsan wahala.
A hankali Baba ya d'ago ya kalli Moha dake tsaye gefensa fuskar sa cikin matsanancin damuwa. Murmushi Baba yace
"Nagode sosai d'ana"
Wani irin d'agowa Moha ya yi jin sunan daya kirashi dashi. Hawaye suka tarar masa a fuska. Hannu Baba ya mik'o masa Moha ya yi saurin motsawa ya kama a hankali yana kallon Jadwah dake barci sai ajiyar zuciya take ja.
"Nasan kai yaron kirki ne Muhammadu. Wannan hali da dabi'u naka ,nasan akwai mak'asudi da yasa kake aikata su. Ko wane irin bawa da kaddarar sa. Ina so ka riƙe Allah ,Muhammadu inshaAllahu komai zaizo maka da sauk'i. "
Wani iri sanyi jikin Moha ya yi kaman an zuba masa k'ank'ara. Rana ta farko a rayuwar sa yaji wani irin kunya da nadama Shaye-shaye sa yake .
"Ina son wata Alfarmar guda d'aya a gurinka Muhammadu. Ban sani ba ko ina da sauran kwana a gaba, amma ina neman taimakon ka saboda Allah "
Jikin Moha na rawa ya k'ara matse hannun Baba cikin nasa. Murmushi Baba ya yi ya d'ago d'aya hannun sa da akewa k'arin jini ya shafa kan Jadwah kafin yace
"Wannan yarinya ita kaɗai ce Allah ya mallakamin a wannan duniyar. Mahaifiyarta ta rasu watanni da suka wuce. Ita ce rayuwar mu. Ita d'in alheri ne a garemu nida mahaifiyar ta da bazamu tab'a samun sama da hakan ba. Alfarmar guda d'aya nake so kamin saboda Allah"
K'ofar d'akin da aka buɗe hankalin su gaba d'aya ya yi kan k'ofar. Wani kyakkyawan mutum ne ya shigo magidanci fari tas dashi,kana ganinsa kaga Moha. Tamkar ya yi kaki ya tofar. Murmushi Baba ya yi cikin ransa yana hamdala. Yasan komai zaizo masa da sauki.
Wane Alfarma ne ku ke tunanin Baba ke nema gurin Moha?
𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.
𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ
( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ)
𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎
𝐏𝐆 8.
Numfashi naja a hankali na fara buɗe idona. Bansan sanda barci ya d'auke ni ba. Kallon Baba nayi dake barci cikin nutsuwa fuskar sa d'auke da murmushi. Wani Numfashin na k'araja na janye a hankali daga k'irjinsa na miƙe in salati. Mamaki ne ya kamani ganin rana tayi a hanzarce na shige banɗakin da nake tunanin cikin d'aki na d'auro alwala na fito. D'ankwalin dake kaina na cire na shimfiɗa na tada sallan asuba. A hankali na shafa Addu'ar dana gama na miƙe ina k'ok'arin d'auke d'ankwali na aka buɗe k'ofar aka shigo. K'irjina ya wani irin harbawa lokacin da idona ya sarke cikin nasa. Sanye yake da manyan kaya wata dakakkiyar farar shadda da tayi masa masifar kyau babbar rigar tasha surfani. Kanshi sanye da bak'ar hula data k'ara fito da ainihin kyansa. Kamshin da yake mai tsananin dad'i da sanyaya gabba ya yimin sallama naja dogon numfashi. Yaune fa d'aurin auren sa ko? Zuciyata ta tunatar dani.
D'auke idona nayi daga kansa na mayar kan k'ofar da ya k'ara buɗe ta sosai. Ido waje nake kallkn Gwagwo data bullo ta bayan nasa tana cewa
"Ina suke ne Muhammadu?"
A guje na tashi nayi kan Gwagwo ina kuka da kira. Wani irin d'ane ta nayi har muka kusa fad'uwa.
"Subhanallahi Jadwah zaki kadani. Yi a hankali kinsan ba lafiyar k'afa ce dani ba."