Sashe 1
Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read
𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
LAMARI
𝐏𝐆 1.
K'aton gida ne dake d'auke da part ɗai-ɗai har gudu uku. Haɗeɗɗen gida ne na gani na faɗa abun sai wanda ya gani. Daga d'an gefen gate d'in gidan k'aramin flat house ne mai d'auke da d'aki biyu. Ciki da falo sai banɗaki. Flat d'in na da y'ar baranda da aka kewaye da tayels gefen sa kuma fanfo da aka yi masa d'an semint aka zagaye wajen fanfom. Yarinya ce da bata wuce shekara 17yr durkushe gaban fanfom da kwanaku gaban ta tana wankewa. Hijabina a jikinta Ash colour mai hannu daya kai mata har gwiwa. Daga gefe cikin barandar babban mutum ne a kwance kan tabarma gefen sa radio na aiki. A hankali ta d'ago karo na ba adadi ta kalli mahaifin ta dake kwance. Kwana biyu yana fama da d'an zazzabi da ciwon k'afa. Dogayen yatsun hannun ta ta kai goshin ta dake cike da gashi yala-yala da suka kwanta . Gumi ta sharce saboda rana yau da ake mai zafin gaske. Yanayin garin na hunturu. Ana cikin tsakiyar zafi musamman yau daya kama ranan juma'a.
Cike da nutsuwa ta maida kanta ta cigaba da wanke-wanke da take tana Allah-Allah ta gama ta d'ora musu abincin rana. Horn da akayi daga can bayan gate d'in gidan yasa ta ajiye kwanan da sauri ta miƙe har tana tuntu'be ganin mahaifin nata na k'ok'arin miƙewa. Da muryar ta mai tsananin sanyi tace
"Baba bari na buɗe "
Murmushi ya yi yana kallonta ta nufi katon gate d'in ta fara k'ok'arin buɗewa. Yasan zata iya buɗewa tunda wani lokacin tare suke buɗeshi. Gate d'in irin mai biyu ne da k'ofar in an buɗe ta ta tsakiya sai ta buɗe kaman littafi. Yana kallo ta cire sakatar taja b'ari d'aya gefe ta koma d'aya b'arin shima taja shi gefe. Dankareriyar Prado jeep ce ta sawo kai cikin gidan bayan ta k'ananan motocine Honda sports biyu. Da ido tabi shegun motocin da suka shigo gidan har wajen k'aton parking space dake cike da motocin na kece raini.
Numfashi taja ta juya tana k'ok'arin maida gate d'in ta rufe. Daga can b'angaren parking space d'in Bodyguards ne suka fito daga cikin k'ananan motocin ko wanne sa sanye da suit bak'i. A hanzarce d'aya daga cikin su ya matsa jikin prado d'in ya buɗe gidan baya. Hamshakiyar macece ta fito daga cikin motar da a k'alla zatayi shekara 40 zuwa da biyar. Duk da shekaru da suka fara ja, saboda kuɗin da jindaɗin rayuwa baza kace takai haka ba. Wani arnen less ne a jikin ta da yake kudan kuɗi an kashe shi da d'inki da kana gani kasan yaci Naira. D'an yololon mayafine a jikinta pink colour daya shiga da leshen jikinta. Mayafin yane yake gefen k'afad'ar ta. Wuyan ta zuwa hannun ta shegun gwala-gwagwalai ne kaman wacce tayi wanka dasu.
Dankareriyar Louis VUITTON jakace a hannun ta da had'addiyar Samsung galaxy Fold. D'aya b'arin da aka buɗe. Kaman wannan data fito itama hamshakiya ce taci ado kaman mazu zuwa gasan kyau. Tunda ta fito daga motar idon ta ke kan Jadwah dake k'ok'arin maida gate ta rufe. Da wani irin yanga da kasaita ta juyo ta kalli d'aya matan .
"Wai Hajiya Balaraba wacece wancan yarinyar ne?"
Wadda aka kira da Balaraba ta d'an yatsina fuska tana k'ok'arin wucewa ta shiga cike tace
"Yarinyar maigadi ne"
Kallon ta matar ta k'ara kaiwa kan Jadwah da yanzu ta matsa can wajen wanke-wanken ta ta cigaba. Kallo d'aya tayiwa yarinyar ta hango tsantsan kyau tattare da ita gata da k'ananan shekaru. Kai ta jinjina ta wuce ta shiga ciki. Katon falon k'asa ta samu H Balaraba zaune kan kujera gabanta lemo ne mai sanyi tana d'an kurba. Falon babu wani tarkace a ciki amma kayan da aka zuba masa kayane na mak'udan kuɗi. Guri ta samu ta zauna yarinyar dake kula da cikin gida ta dawo d'auke da ruwa da lemo cikin jug ta ajiye gaban ta. Lemon ta tsiyaya cikin cup ta fara jika mokogaron ta ,kafin ta maida hankali kan Balaraba dake ta faman danna waya tace
"Wai ya akayi ban taɓa ganin ta ba tunda nake zuwa gidan nan?"
D'agowa tayi daga kallon wayar da take ta watsa mata ido cike da tuhuma tace
"Wai menene ya dame ki da yarinyar nan ne. Na gaya miki yarinyar maigadina ce. Bata dad'e da dawowa gidan nan ba bayan Mahaifiyar ta ta rasu wata bakwai da suka wuce. Na sanki Suwaiba. Yarinyar is off limits kaman Asiya. Kar ki zubarmin da mutunci. Kiyi duk abunda zakiyi da wasu amma banda ita. "
Wata y'ar dariya H Suwaiba tayi tace " dole na kyasa yarinyar tayi. Kin ganta kuwa?. Gaskiya baza ki yimin katanga da nama na ba. Tunda ke kin k'i ki shiga wannan harkar. Baki san abunda ki ke missing ba wlh. Akwai sugar yanda baki tunani"
Baki Balaraba ta tab'e rai a d'an b'ace tace " eh bana ra'ayin hakan. Muyi duk abunda zamuyi amma banda wannan harkar taki. Ina k'ara gaya miki ki kyale yarinyar nan kar ki zubarmin da k'ima wajen Ubanta dake ganin girmana"
Baki Suwaiba ta tab'e bata ce komai ba, cikin ranta tana kyestima abubuwan da zatayi wajen cimma manufarta. Zama Balaraba ta gyara fuskarta very serious tace
"Wai kinsan d'an iskan yaron nan duk d'awainiya da nake dashi har yanzu ya gagara d'aukata uwa. Mene ban masa ba?
, ni naci kashin sa ,naci fitsarin sa tun yana tsumma. Duk wannan abun bai gani ba. Ganin sa ma kawai idan zanyi sai nayi ta masa magiya da roko?"
"Taya ki ke so ya gani tunda baki gina shi kan tarbiya mai kyau ba. Baki d'ora shi kan sanki da tsoron ki ba?,Ki gaggauta dai ki san yanda zakiyi ki mallakeshi kaman yanda ki ka mallake uban sa kafin ya hau kan kujerar nan. Idan Asiya ta aure shi kinga ko ta ina kece a sama. Kin riƙe uba kin riƙe d'a sai yanda ki ka yi"
Numfashi Balaraba taja mai zafi tace " dalilin kenan da yasa nace kizo. Zanyi duk yanda zanyi na shawo kansa yazo Nigeria yanda aikin zaifi tafiya da kyau. Ina so jibi ki rakani wanjen JALLI yamin aiki"
Murmushi Suwaiba tayi "angama" kai Balaraba ta d'aga ta miƙa hannu jikin kan tebir ta d'auki wayarta ta dannawa wata number kira. Babu jimawa saiga d'aya daga cikin masu tsaron ta ya shigo a sukwanne. Yana shigowa ta miƙe ta kalli Suwaiba dake zaune tana murmushi.
"Bari na shiga daga ciki na d'an matse gajiya"
Da y'ar dariya ta shak'iyanci tace " a fito lafiya".
Da ido ta bisu har suka haura sama. Kai ta k'ara girgizawa tana tunanin da ita da Balaraba wa yafi shed'anci?.
Kaman wadda ta tuna da abu ta miƙe da sauri ta haura sama tayi wajen balcony dake da clear view na compound d'in gidan har k'ofar d'akin Baba Maigadi. Zaune ta hango ta tana tankad'e fuskar ta d'auke da murmushi. Da alama maganan da mahaifin nata yake mata ne yasa ta wannan murmushin.
Tana gamawa ta miƙe ta shiga d'aki bata jima ba ta fito riƙe da d'an bokiti a hannun ta mai murfi ta kalli Mahaifin nata.
"Bari na kai mana markad'e Baba. Nasan yanzu an sakko daga masallacin"
"To a dawo lfy. Allah ya tsare"
Cike da tsananin jindaɗin Addu'ar sa ta amsa da Amin fuskar ta d'auke da murmushi . Murmushin da tayi ya bada daman ganin dimples nata da suke lub'awa koya ta motsa fuska. Harta fice idon Suwaiba na kanta tana kissima abubuwa da dama.
K'oda ta fito a hankali take tafiya cike da nutsuwa har gidan da zata kai markad'en dake d'an gaban layin su kad'an. Layin data tarar yasa ta ajiye nata, ta fito tayi bakin kasuwa tasan yau juma'a kasuwa naci sosai. Chanjin dake hannun ta ta siyo musu magi ,gishiri da d'an sauran kayan kamshi don wanda ta siyo ya k'are. Hardasu daddawa da busheshshen kifi. D'an canji daya rage ta siyo musu d'an nama na dubu d'aya tana tunanin yaushe rabon data ga nama da ido bare a miya. Musamman ma saboda rashin lafiyar Baba bakin babu dad'i tasan zaiji dad'in tuwon sosai.
Bata jima ba ta fito daga kasuwar ta koma gidan markad'en ta tarar har anyi mata nata. Dauka tayi ta fito bayan ta biya kuɗin. Tana fitowa ta tsaya cak tana kallon bak'ar motar dake fake k'ofar gidan data lura tun data fito daga kasuwa motar ke binta amma bata bawa abun muhimmanci ba. Kyakkyawan saurayi ne d'an fari jingine jikin motar cikin manyan kaya. Yana ganin ta ta fito ya saki murmushi ya d'an matsa daga jikin motar ya matso ida take tsaye.
Fuskata ta b'ata tana kallon sa yana mata sallama.
"Assalamu'alaikum warahmatullahi wa barkatuhum"
Saboda sanin muhimmancin sallama yasa ta amsa masa fuska babu walwala Ciki-ciki. D'an murmushi ya yi mai k'ayatarwa yace
"Kiyi haƙuri baiwar Allah nasan na takura ki, amma bazan iya barin ki tafi ba tare da nasan sunan ki da gidan ku ba. Sunana Junaid"
"Hmm, kayi hak'uri bana tsayawa a waje"
Tana gama fad'in haka ta wuceshi da sauri bata jira abunda zaice ba. Murmushi ya yi ya shiga mota yabi bayanta. A ransa babu abunda yake cewa face yaga matar Aure. Har k'ofar gidan Balarabe ya bita. Mamaki sosai ya kamashi ganin ta buɗe k'aramin gate d'in gidan ta shige. Kai ya jinjina k'afin yaja mota ya tafi tambayoyi kala-kala cikin ransa. Dama bayan ASIYA DA ISMA'IL ya'yan Hajiya Balaraba dake zaune cikin gidan nan akwai wata budurwar ne da bai sani ba?. In haka ne menene alakarta dasu?. Batun yau yasan wacece Hajiya Balaraba da yaran ta ba. Sai Babban yaron Alhaji Balarabe SHAZALI dake zaune k'asar waje. MUHAMMADAN BALARABE SHAZALI da akewa lakab'i da MOHA ko BIG BROTHER.
A da zai iya cewa lokacin da suke samartaka sunyi abota da Moha. Bayan tafiyar sa jam'ar Oxford karatune abotar tasu ta dakushe. Kowa da burin daya sa gaban sa. Rayuwar da Moha ya d'auka ne zai iya cewa tayi sanadin da zumuncin su ya b'aci.