← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Da Amin ta amsa masa ta miƙe tana k'ok'arin ficewa ta k'aramar K'ofar gate. Kafin ta kai hannun aka turo k'ofar tayi saurin ja da baya ganin Isma'il ne . Fuska a had'e ta wuceshi ya bita da wani mayan kallo bai damu da Mahaifin ta dake zaune gefe yana kallon sa. Tunda Jadwah tazo gidan nan yake bala'in son yarinya, amma sam taki bashi fuskar ma da zaiyi mata magana . Duk hanyar da zaibi don ganin ta kulashi ya yi abun ya faskara. Ga mahaifin ta da in har yana gida to sosai yake sa ido kan y'ar tasa don kareta daga sharrin sa. Numfashi kawai yaja bayan ta fice ya juyo kaman wani yaro arziƙi har inda Baba ke zaune yana kallon sa. Durkusawa ya yi har k'asa cikin girmawa yace

"Baba ina kwana?"

Tsananin mamaki da tu'ajjabi yasa Baba ya saki baki yana kallon sa ya kasa amsawa. Abune da bai saba gani ba. Yaushe ne Isma'il ya yi hankali?. Kai akwai wata a k'asa. Da kyar ya tattaro y'ar nutsuwar sa yace

"Anyi haka Alhaji?. Barka da zuwa bari na buɗe maka gate "

Da wani irin sauri kaman yaron kirki Isma'il ya tare shi yana cewa

"A'a yi zamanka Baba zan buɗe "

Harda wani munafukin murmushi. Shi a ganin sa idan ya nuna musu ya chanza hali, Jadwah zata amince dashi ta kulashi kaman yanda yake buri. Kallon sa kawai Baba yake har ya buɗe gate ya shigo da mota ya fakata kafin ya koma ya rufe gate d'in. Har ya wuce ya shiga ciki Baba na kallon sa yana k'ara neman tsari wajen Allah tsakanin y'ar sa da wannan yaron. Shi kansa yasan zamanta a gidan nan hatsari ne babba. To halin rayuwa da rashin mafita yasa yake zaune da ita a nan.

Main falo Isma'il ya same su H Balaraba da Suwaiba harda Asiya suna karyawa kan Family dinner. Haka ya kutsa kai cikin gidan babu sallama bare gaida na gaba dashi yaja kujera ya zauna yana zuba abinci. Dukkaninsu babu wanda ya damu da abunda ya yi hankali kwance suke cij abinci. Can Balaraba ta d'ago tana kallon Isma'il dake cin abincin kaman zai had'a da kwanan babu nutsuwa. Rai a b'ace tace

"Wane irin cin abinci ne wannan kaman wani k'aramin yaro?"

"Idan kina so na daina wannan dabi'u ki amince nayi aure. Kuma dole ki yarda da yarinyar da nake so"

Ya k'arasa maganan da wani mugun murmushi kan fuskar. Ido kawai ta zuba masa bata ce komai ba. Dariya Suwaiba ta fashe da ita daya k'ara tunzura Balaraba a zafafe tace

"Kinga halin nasu ba. Shi yasa nake so Moha yazo gari ya saitamin ku. Babu yarinya da zaka aura sai in har nice na baka ita. Kama ajiye batun ko wace yarinya ce a gefe babu kai babu ita. Zab'ina nake so kuma dole kabi umarni "

A fusace ya miƙe ya yi jifa da kwanan da yake cin abinci yana zuba uban huci yace

"Wlh baki isa ki hanani auren yarinya nan ba. Dole saina aure ta babu wanda ya isa ya hanani auren ta" ( da alama Isma'il yana manta cewa komai da ikon Allah ne yake faruwa). Fuu ya wuce yana jifa da dukkanin abunda yasha masa gaba.

"Kinga ni ba. Suwaiba yau zamuyi tafiyar nan kinsan halin Isma'il idan ya kafe kan abu, yana da mugun taurin kai. Haka kawai bazan yarda ya nemo wata yarinya da zata juyashi ba. Tun abun baiyi nisa ba ina buƙatar Moha don shine kad'ai zai tsawatar masa"

"Maganan da nake son yi miki kenan"

Suwaiba tace tana kurb'an tea. Asiya dai tunda ta zauna bata ce uffan ba. Hankalin ta gaba d'aya na kan wayarta tana chat da Jojo.

Tafe suke da k'awar ta Amina bayan sun taso daga makaranta. Amin y'ar makocin sune. Yarinya ce data fito daga Babban gida amma sam bata da girman kai. Tunda taga Jadwah take son ta saboda nutsuwar ta da hankalin ta. Amina ta jima tana son Moha. Tun tana k'arama take masifar son shi gashi shi kuma baima son tanayi ba. Sau d'aya ne suka tab'a had'uwa da ita lokacin tana shekara 13 a lokacin ne ya bar Nigeria ya koma Italy da zama saboda karatun sa.

Kallon Jadwah tayi tana murmushi a karo na ba adadi tana k'ara gaya mata irin son da take wa Moha. Da irin mafarke-mafarke da take a kansa na kasancewa matarsa. Baki Jadwah ta d'an tabe tana cewa

"Kin gamu da aiki wlh. In ba haka ba. Ina amfanin son wanda baisan kana yiba"

D'an murmushi Amina tayi mai d'an ciwo daidai suna tsayawa k'ofar gidan su ta juyo tana kallon Jadwah tace

"Baza ki gane abunda nake nufi ba sai ranan da ki ka ganshi. Ina nan ina Addu'a Allah ya dawomin dashi nan kusa"

"Hmm, to Allah ya kyauta bari na wuce ni kar Baba yaga na dad'e"

"Aikuwa kwana biyu ban samu na shigo mun gaisa da Baba ba. Ki gaidamin shi don Allah kafin na shigo"

Sallama suka yi ta wuce da sauri Amina ta shiga gida. Turus ta tsaya tana kallon yayan ta Junaid dake tsaye bakin k'ofar alamun ya dad'e a gurin. Yana ganin Amina ta shigo ya yi saurin riƙe ta yana cewa

"Ina ki ka san wannan yarinyar?"

Da mamaki tace "wai Jadwah?, kawata ce ai sosai. Suna zaune ne gidan su Big Brother "

Sata ya yi a gaba saida ta gaya masa dukkanin abunda ta sani game da Jadwah da Mahaifin ta.

𝐏𝐆 3.

Tun daga nesa ta hango Baba dake k'ok'arin buɗe gate alamun za'a fita da mota. Da azama ta k'arasa bakin k'ofar ta taimaka masa suka buɗe. Daga cikin motar da H Balaraba da Suwaiba ke zaune . Suwaiba ta d'an d'aga murya tana kiran ta. Matsawa tayi jikin motar cikin girmawawa tace

"Ina wuni Hajiya"

Murmushi Suwaiba tayi tana kallon Mummy Balaraba data mugun had'e fuska.

"Lfy lau Y'an mata ya. Ya sunan ki"

Babu tunanin komai tace "Jadwah, Hajiya "

"MashaAllah , sunana mai dad'i "

Kafin ta k'ara cewa wani abu Mummy Balaraba ta bawa direba umarni yaja mota. Da sauri Jadwah ta matsa gefe tana kallon motar data fice ta mayar da gate d'in ta rufe. A d'an fusace Suwaiba tace

"Ya haka ina magana da yarinyar zakice aja mota?"

"Suwaiba, ina k'ara gaya miki ki fita harkar yarinyar nan karmu samu matsala dake"

Ran Suwaiba a matuƙar b'ace ta yi kwafa bata ce komai. Tace duk abunda zatace amma bata isa ta hanata kauda kwad'ayin ta kan yarinyar.

Saida ta fara ajiye jakarta ta makaranta sannan ta fito riƙe da foam a hannun ta ta durkusa inda Baba ke zaune fuska d'auke da murmushi tace

"Baba ga katin mu na saukar Qur'ani nan da wata biyu masu zuwa inshaAllahu "

Da matsanancin fara'a da farinci ya karb'a ransa na kissimamasa hanyoyi da zaibi wajen ganin ya ajiye y'an kudade masu yawa da zai tara idan lokacin saukar yazo. InshaAllahu zaiyi bakin k'ok'ari wajen ganin ya yi mata abubuwa da iyaye ke yiwa ya'yan su a irin wannan rana mai Albarka da kuma farin ciki. Don haka tafiya ta kamashi zuwa Kano inshaAllahu wajen y'an uwa ko Allah zaisa a dace.

Albarka ya yi ta shi mata yana yi mata Addu'o'i na samun nasara. Farin ciki wajen Jadwah abun sai wanda ya gani. Haka ta koma d'aki ta chanza kaya zuwa doguwar riga da d'an k'aramin hijabi. Tana gyara wake don d'ura musu abincin rana Isma'il ya fito yasha manyan kaya. Blue d'in shadda d'inkin tazarce da bak'in takarmi mai yatsa sai bak'ar hula. Babu laifi ya yi kyau tunda abune da bai saba sawa ba. Har k'ofar d'akin nasu ya k'araso riƙe da mukulli ya durkusa kusa da Baba dake kallon sa ,Jadwah tayi mugun b'ata rai tana gyara wake bata kalli inda yake ba.

"Barka da hutawa Baba"

"Yauwa Alhaji Isma'il. Har an fito ne za'a fita?"

Kai ya d'an sosa yana cewa " eh wlh Baba zanje d'aurin auren wani aboki na ne da za'ayi k'arfe d'aya "

"To MashaAllah. Allah ya sanya alheri. A dawo lafiya "

Har cikin ransa zaka san yaji dad'in Addu'ar, saboda wani murmushi daya kufce masa ya miƙe yana kallon Jadwah da ko kurar sa bata kalla ba har ya wuce ya buɗe gate ya shiga mota ya fitar waje, kafin ya dawo ya mayar da gate d'in ya rufe ya fice ta k'aramar k'ofa. Daga Baba har Jadwah babu wanda yace komai dukkanin su ,suka bar maganan su cikin zuci. Tana gama gyara waken ta d'ora musu kafin ta dawo ta daka musu yaji mai shegen dad'i dayaji gyad'ar kamshi da tafarnuwa. Sosai suke hira da Baba aka sarin hirar su kan kakar ta ne Goggo dake zaune can rugarsu a Niger.

Wajen k'arfe biyu ta fito shirye cikin kayan su na islamiya. Tana k'ok'arin yiwa Baba sallama, Amina ta rangada sallama ta shigo gidan. Saida suka gaisa da Baba sannan sukayi sallama suka fito. Suna tafe suna y'ar hira Amina nata son ta kawo maganan yayan ta Junaid ,amma ta bar maganan zuwa wani d'an lokacin.

Mummy Balaraba da Suwaiba kai tsaye wajen Bauchi suka nufa wajen Jalli na kan dutse. Da yake suna zaune ne a AZARE/KATAGUM dake jihar Bauchi. Tafiya sukayi kaman zasu bar gari kafin su yanke hanya subi dokar daji. Daga Suwaiba har Mummy Balaraba babu tsoro ko d'ar a ransu don hanyace da suka saba bi. Saida suka d'auki wajen awa guda suna shiga cikin kwazazzabai da ciyaye kafin su fito wani katon dutse dake zaune tsakiyar dokan dajin babu gida gaba babu gida baya. Daga d'an nesa da dutsen kad'an direba ya faka motar shi kad'ai zaka kalla kaga tsoro tattare dashi.
Chapter 3 · 0% Book details