← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Amina najin wannan batu ta wartsake jiki na rawa ta fara neman number Moha. Saida taki wajen uku a kashe ta hud'un ne number shi ta US ta shiga. Wayar na fara ringing Amina ta dafe k'irjinta dake tsananin bugawa kaman zai tarwatse. Har ta fidda rai zai d'auka sai taji wannan muryar mai tsananin taushi da gardi ta ratso speaker wayar

"Hello"

Wani iron d'auke numfashi tayi ta kasa cewa komai saida Saudat ta zungureta. Muryar a hankali tace

"Ya Moha"

Shiru ya ratso wayar na y'an mintina kafin taji yace

"Who is this?"

"Amina ce"

"Amina" Ya maimaita sunan da wata irin murya data kaaa fuskartsa. Da ido Malam yace yi mata nuni ta kashe wayar. Bata musa ba ta kashe do gaba d'aya ta rud'u bata Sam abunda zatace ba.

"Wannan kiran nashi da ki ka yi. Baza ki k'ara ba daga yau. Shi zai dinga kiran ki a ko da yaushe. Ki tsaya ki gani. Aikina yankan wuk'a ne a take yake ci"

Ya k'arasa maganan da wani irin murmushin mara kyau kam fuskarsa. Yana rufe baki kuwa wayar Amina ta fara ringing. Wayyo Allah ran Amina kaman wacce aka yiwa albishir da Aljanna.

SOME WEEK'S LATER.

US.

A gajiye ya faka mota harabar motoci. A hankali ya fito sanye yake da k'ananan kaya farar riga mai botira da bakin jeans. Kayan sunyi masa kyau sosai duk da rashin barci dake tattare dashi. Kai tsaye cikin gidan sa ya nufa tun daga k'afar bene ya fara balle botiran rigar sa ya cireta ya wurgar. Yana buɗe k'ofar d'akin sa ya tsaya turus ya k'ara wara ido yana kallon Asiya dake kwance kan gadonsa da wasu y'an iskan kaya a jikinsa. Yaushe tazo nan har tasan inda yake zaune.? Wani irin mayen kallo Asiya ke masa tana bin murdadadden k'irjin sa da kallo zuwa fatar cikinsa dake shak'e da Abs. Lebe ta lashe ta taso tana wata y'ar iskar tafiya sai tana juya Mazaunai ta nufo shi. Ido kawai ya zuba mata fuskarnan babu expression harta k'araso gabansa ta tsaya. Hannu ta kawo a hankali zata d'ura kan k'irjin sa ya wani riƙe hannun kaman wanda ya riƙe kashi.

"Are you mad? What are you doing in my house?"

"Gidan ka? Gidan ka kai kad'ai? Nima ai gidana ne. Ai ba laifi bane idan mata tazo wajen mijin ta"

Taune harshe ya yi yana kallonta da wnai irin tsana. Kina matsayin mace amma kece ke nuna maitar ki kan namiji. Yana kallon yanda take wani kashe ido tana cije lebe ya wurgar da hannun nata kafin ya juya da sauri zai bar mata d'akin. Da azama tasha gaban sa

"Gaskiya abunda ka ke kana d'aukan hakkina. Yau watanmu nawa da aure? Tunda ka bar Azare baka k'ara waiwayata ba bare ka duba Mummy dake kwance gadon asibiti. Kasan ni dai ba dutse bace dole na buk'aci mijina tunda an daura shi yasa nayi tattaki nazo har inda ka ke"

Haushi takaici yasa ya zuba mata manyan ocean Blue eye's nashi ya kasa cewa komai. K'ara matsowa tayi sosai k'irjin ta kad'an ya rage bai had'u da nashi ba. Da wata y'ar iskar murya tace

"Kaima nasan kana buƙatar haka. Ba waliyi bane ba kai. Ka bari muji dad'in juna. You will enjoy this yanda baka tunani"

Wani irin shafo k'irjin sa tayi zuwa nipples nashi wani irin shock ya ratsashi .yana jin sautin numfashin ta daidai wuyansa tana k'ok'arin kai masa sumba. Kaman rad'a yaji wannan murya mai tsananin taushi da dad'i cikin kunnan sa kaman iska

"MOHA"

firgigit ya wartsake daga trans daya shiga daidai Asiya na neman had'e bakin salu . Wani irin ja ya yi da baya labbanta ya sauka kan iska. Idonta dake rufe ta buɗe tana kallon Moha daya juya da sauri yana sauka daga kan benen. Bata san sanda ta saki ihu na frustration ba tana kallon sa har ya fice daga gidan gaba d'aya. Da ihu ta shige d'aki tana jifa da dukkanin abunda taci karo dashi. A mugun buk'ace take ga Jojo bata nan. Rashin sanin abunyi ya haye gadon da hoton Moha tana saukewa kanta ishin dake damunta. Ihunta da sunan sa kawai ka ke ji yana tashi cikin d'akin.

A guje ya fice daga gidan shi kansa bai san inda ya nufa ba. Abubuwa ne sai kara jagule masa suke. Gefen titi ya faka motar ya koma ya kwanta jikin sitiyarin motar yaba sauke numfashi. Can ya d'auko wayarsa yana k'ok'arin kira kiran ya shigo masa waya. Ido ya zubawa number Amina dake yawo kan screen nashi. Wai what is happening to him ne?. Sam baya jin yarinya cikin ransa but ya rasa dalilin da yasa ya kasa cireta cikin ransa haka ya kasa daina kiran wayarta a kullum. Ya kasa hana kanshi neman aurenta duk da cewa can k'asan zuciyar sa bashi da wannan burin. Numfashi yaja mai k'arfi ya k'ara wayar a kunne.

A shagwaɓe ta kirasa kaman za tayi kuka

"Big Brother ko nayi maka laifi ne yau?"

Saida ya fursar da numfashi yace " No. Sorry nayi busy ne yau. "

Murmushi tayi " OK dama nace bari na sanan da kai abubuwan dana shirya na bikin da event da zamuyi"

"Hmm"

Kawai yace harta gama b'ab'atun ta baice komai ba sai OK. Suna gamawa ya kashe. Tunda ya tura mahaifin sa neman Auren ta bayan neman shawarar Gwagwo ta bashi had'in kai d'ari bisa d'ari. Shi yasa yake son matar duk da sanin matsayin sa gurin Jadwah . Sam bata da son kai. Numfashi yaja mai k'arfi ya fesar yana maimaita sunan JADWAH kan leben sa. Lokaci ya yi da ya kamata yaje ya ganta. A hankali ya d'auko wayar ya lalubo number Gwagwo ya danna mata kira.

Miƙewa nayi ina mik'a bayan na idar da sallan isha. Gwagwo dake kwance kan gado har ta fara munshari na kalla nayi y'ar dariya na gyara mata bargo. Garin yau sanyi ake sosai sabida ruwa da aka wuni anayi. Kan tawa katifar na nufa ina k'ok'arin cire hijabin dake jikina. Rigar barci nasa mara nauyi na samu guri na kwanta ina Addu'a tunanin Baba fal cikin raina. K'arar wayar Gwagwo yasa na d'ago da sauri ina kallon gefen Gwagwo da wayar ke ajiye. Da azama na tashi na d'auko wayar ina kallon suna TAHEER JIKA NA da Gwagwo tasa. Baki na tab'e na d'aga wayar da y'ar sallama

"Hello, Slma"

Wani irin shiru ne ya ratsa wayar sai numfashi da naji an sauke a hankali. Shirun nima nayi ina sauraran ko zaice wani abu.

"Gwagwo tayi barci"

Nace ina cigaba da sauraran yace wani abu. Haushi ya kamani na cire wayar daga kunnena ina d'an tsaki . Da wata irin rad'a naji ance "JADWAH " sai kuma diff wayar ta katse. Baki na hangame ina kallon wayar da tunanin waye ne kuma wannan? Ina kuwa nasan wannan muryar?.

𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.

𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎

𝐏𝐆 10.

Washegari ban gayawa Gwagwo kiran da akayi mata na cigaba da sabgogin gaba. Bayan kwana biyu da faruwar hakan yau muna zaune tsakar gida ina yiwa Gwagwo kalba. Duk da cewa shekaru sunja amma gashin Gwagwo har yanzu da tsayin sa da santsin sa, da kyar yake kamuwa .gashi ne har gadon baya. Baba da Ammi na basu da gashi sosai, amma ni kuwa gashina har hip's d'ina yake nayi gado wajen Gwagwo. Gashi baki mai tsantsi. Numfashi naja mai k'arfi na fesar Gwagwo ta d'an juyo tana kallo na.

"Lafiya ki ke sauke ajiyar zuciya? "

Murmushi nayi da baikai zuci ba nace

"Wlh Gwagwo ina son cigaba da karatu na. Yanzu lokacin saukar mu ya gabato za'ayi babu ni. Bansan ya ake ciki game da saukar ba. Zaman gidan ne ya isheni. Ina son na cigaba da karatun boko ma"

Kai Gwagwo ta jinjina kaman mai tunanin wani abu tace

"Kina da gaskiya. Bari za muyi magana da TAHEER naji yanda za'ayi "

"Waini Gwagwo waye wannan Taheer d'in ne da komai zakiyi sai kin nemi shawarar sa?"

Nayi magana da jin haushi. Y'ar dariya kawai tayi batace komai. Washegari na tashi da kiran Gwagwo. Miƙa nayi na miƙe zaune ina kallon agogo dake kafe jikin bango. Numfashi naja a hankali na miƙe ina salati. Hijabi na d'ura kan rigar barcin dake jikina na fito nayi falo inda nake jin muryar Gwagwo na kira. Baki na turo da d'an shagwaɓa na d'aga labulen d'akin ima cewa

"Waini Gwagwo kiran na menene haka kaman zaki fasamin dodon k..."

Maganan tawa ta mak'ale sakamakon tsarkewa da idona ya yi dana Big Brother. Wannan manyan Blue eye's nashi sun kafeni da ido. Dum k'irjina ya buga nayi saurin d'auke nawa ido na k'arasa shiga falon na samu guri kusa da Gwagwo na zauna.

"Yauwa kin taso. Maza ki gaidar da Muhammadu. "

A hankali na d'ago inda yake zaune sanye da k'ananan kaya. Farar riga mai botira da bak'in wando sai bak'ar jacket d'aya d'ura kan rigar tashi. K'asa k'asa nace

"Ina kwana?"

Bai amsa ba sai ido kawai daya zubamin ko kunyar Gwagwo dake zaune gurin baiji. Rai na k'ara b'atawa Gwagwo tace

"Maza jeki deb'o masa Kiddirmun nan da ki ka hada akwai ragowar sa da gashin naman nan"

Ban musa ba na miƙe da sauri na fice daga falon ina jin idansa na bina. D'aki na koma na fara chanza kayan dake jikiba zuwa doguwar riga bak'a da d'an hijabin ta, sannan na fito nayi kitchen. Kiddirmun da na had'a mana jiya da daddare daya sha kwakwa da inubi na d'auko na zuye cikin glass jug da cup nashi na d'ura kan tire kafin na k'ara gasa masa gashin tsiri da nayi mana na tunkuya na juye cikin d'an flasks mai kyau. D'auka nayi na koma falon. K'asa-k'asa nake jin maganan Gwagwo tana cewa

"Bikin ya gabato kenan. Jibi-jibi nan. Ita Aminan ce dai?"
Chapter 11 · 0% Book details