← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda muka d'auki hanya na mayar da hankalina da nutsuwa ta waje. Ban bari idansa da nake ji a kaina ya sani damuwa ba. Cikin raina nake Addu'a da y'ar tilawa duk dan hankalina ya kau daga kansa. Bansan awa nawa mukayi ba ya hanya ya faka gefen wani k'aton masallaci mai girma gaske da ke d'auke da kasuwa ta matafiya. Yana fakin motar na fara k'ok'arin buɗewa na fice saboda hango masallacin mata da nayi . Motar tak'i buɗewa saida na juyo na kalleshi already dama naji idon sa a kaina. Kaifin idonsa yasa kashemin jiki na sunkuyar da kai na k'asa k'irjina na harbawa. Wani irin firgita nayi na koma jikin window na mak'ure sakamakon hucin numfashin sa da naji ya daki fuskata babu zato. Kamshin minti breath nashi da daddad'an Kamshin sa ya bugeni. Ido waje nake kallon shi ya yunƙuru sosai wajen fuskata yana kallona da wani irin yanayi kan fuskar sa . Ido muka zubawa juna ina tunanin menene yake shirin aikatawa haka kuma? Numfashi ya d'an daya daki fuskata kafin naji yace a hankali

"Me ki ke so kici?"

Bakina ya fara rawa na kasa furta komai saboda yanda yake kallona. Wai meke damunsa ne?. Ganin na kasa cewa komai ya d'an ja baya kad'an ya riƙe sitiyarin motar da duka hannun sa biyu. Wani Numfashin ya k'araja a hankali ya fesar ya danna wani abu jikin motar ta buɗe. Da sauri na fice daga motar har ina k'ok'arin kifawa. Kai tsaye b'arin mata nayi na kama ruwa nayi alwala na shige masallaci nayi salla. Saida na d'an b'ata lokaci wajen Addu'a sannan na shafa na fito. Zaune na hango kan motar yana danna waya mutane sai kallonsa suke kaman sunga sabon halitta. A hankali na nufi motar ya d'ago daga duba wayar da yake dubeni kafin ya duro daga kan motar. Kafin na k'arasa ya buɗe min motar. Shiga nayi a hankali bance komai na shima ya zagayo ya shiga. Ledoji ya fidda dasu daga bayan motar ya ajie kusa dani. Tuni kamshin kaji da snacks suka cikamun hanci cikina ya fara kukan yunwa. Ina ji yace a hankali

"Eat something sai mu tafi"

Babu yanda za'ayi na iya cin abinci a gaban sa. Kaman yasan tunanin da nake naji ya yi d'an murmushi kafin ya buɗe motar ya fice. Yana fita na zage naci abincina hankali kwance saida nayi nak na ture gefe. Kaman minti biyu da gama cin abincin nawa ya dawo cikin motar muka d'auki hanya. Bamu jima da d'aukan hanya ba barci ya yi awon gaba dani ban farka ba saida muka isa Azare. Ido na buɗe a hankali ina salati. Gani nayi har mun shiga layi ya dunfari gidansu. A hanzarce na juyo ina kallonsa nace

"Ina zaka kai ni?"

Bai kalleni ba yace " Home" kai na girgiza da sauri ina kallon sa ido waje. Me zanyi a gidansu kuma?

" A'a gidansu Amina zaka kai ni me zanyi a gidan ku?"
Baice komai ma ya juya da motar zuwa gidansu Amina. Tun daga bakin layin nasu za kaba motoci nata shige da fice. Murmushi nayi sanda ya faka motar a k'ofar gida ba farara k'ok'arin buɗe motar amma taki motsi. Juyowa nayi na kalleshi.

"Ka buɗe min k'ofar "

Kaman bazai motsa ba sai kuma yaja numfashi ya buɗe min motar na fice da sauri shima ya fito. Zagayawa ya yi ya buɗe boot ya fiddo da jakata da wani d'an akwati mai kyau ya ajiye k'ofar gidan su Amina. Kallonsa nayi da akwatin nace

" Wannan ai ba nawa bane"

Wani irin motsawa ya yi gabana nayi saurin ja da baya na had'u da gate d'in gidan ina kallonsa ido waje. D'an sunkuyowa ya yi saitin fuskata yace

"Take care of yourself Alright?. Zan ki raki anjima"

Galala na tsaya ina kallonsa da d'unbin mamaki da tu'ajjabi. Menene hakan ne yake yi? Ya kuwa san nan k'ofar gidansu matar da zai aura ne. Idan mutane suka ganmu a haka me yake tunanin zasu d'auka?. K'ofar da aka d'an tab'a alamun za'a fito yasa ya d'an ja baya yana kallona. Yan matane suka fito sunci kwalliya sai shek'a dariya suke da alama hirar da suke tana musu dad'i. Gaba d'aya sukaci burki suna kallkn Moha da ido a waje. Shikam ko kallon su baiyi ba ya juya bayaj ya k'ara jifana da wani one last look ya juya da tafiyar nan tashi ta izza ya shige mota. Bansan na riƙe numfashi na ba saida motar ta b'ace daga idona na sauke wani irin dogon nishi. Jakata na d'auka da akwatin na shige ciki na bar y'an matan nan tsaye suna kallona har zuwa lokacin shock baibar kan fuskar su ba. Su zuzuce ganin Moha. Murmushi ne kwance kan fuskata na shiga gidan da ya cika da mutane kai. Ina shiga falon naci karo da Hajiya Fati da mutane. Taja ganina ta saki murmushi sosai kan fuskar ta ta nufoni da sauri

"A'a Jadwah. Kece a garin yau. Ashe zaki zo?. Lale maraba sannu da zuwa ya Gwagwo?"

Manyan matan dake d'akin ta bi tana nuna musu ni kafin tace a kaini wajen Amina suna can suna shiryawa za'a tafi kamu. D'akin Amina mua nufa har zuwa lokacin da murmushi kan fuskata. Daga I sai wasu kayenta guda biyu da maiyi mata kwalliya. An shiryata cikin wani arnan less da akayi masa d'inki doguwar riga maroon colour. Sosai tayi kyau. Ta mudubi muka had'a ido da Amina da akewa kwalliya. Mamaki ne naga kwance kan fuskarta tana kallo haka ma kawayenta.

"Jadwah "

Ta kira sunana babu wani farin cikin ganina. Ban damu da hakan ba na k'ara matsowa ina murmushi.

"Wlh baki da kirki Amina. Yanzu ace bikin ki guda da Big Brother ki kasa aikowa a gayamin?"

Fuska babu walwala tace " abubuwane sukayi yawa shi yasa na sha'afa" ido kawai na zuba mata aka cigaba dayi mata kwalliya daga haka bata k'ara cemin komai ba. Ina lura da irin harara da kawayen nara keta zubamin. Duk sai naji na fita daban, amma duk da haka ban sareba na cigaba da tsayuwa har aka gama yiwa Amina kwalliya aka k'arasa gyarata. Gaba d'aya suka miƙe zasu fito na biyo bayansu. Ban damu da chanza kayan jikina ba tunda babu abunda kayana sukayi. Harabar gidan da aka k'awata da decorating nan akayi kamu. Anci ansha an dance. Ina ta murmushi na jindaɗi sam ban bari ko in kulan da Amina kemin ya dameni ba. Ba'a tashi daga kamun ba sai wajen tara na dare kowa ya nufi makwanci. Hajiya Fati da kanta ta nemomin d'aki da zan kwanta inda na tarar da y'an mata biyu ne kawai a ciki. Jakata na hango gefen gadon na zauna ina tunani daga baya na shige bayi na watsa ruwa da alwala na fito nayi salla da nafila . Lokacin dana idar tunani y'an matan nan sun kwanta kan gadon. Kan kujera na samu na kwanta riƙe da wayata. Kunnata nayi ina tunanin kiran Gwagwo nasan yanzu dare ya yi tayi barci na barta saida safe. Ina k'ok'arin kashe wayar tawa kira ya shigo min. Mamaki ya kamani ganin sunan Big Brother a jiki. Koda yake ba abun mamaki bane tunda shiya kawomin wayar. Kaman karna d'aga na dai d'aga da y'ar siririyar murya.

Numfashi naji yaja a hankali kafin yace

"Bakiyi barci ba?"

"Hmm" kawai nace .

"Dama na kirane naji yanda ki ke. Fatan kinci abinci. Kuma suna treating d'inki well?"

Tunanin yanda Amina ta sauyamin ya fad'o " Lafiya nau nake. Me yasa ka ke tunanin za suyimin wani abu?"

Shiru ya yi baice komai ba har na y'an sakanni sannan yace " OK. Dama na kira naji yanda ki ke have some sleeps. Nayi waya da Gwagwo tace wayar ki a kashe."

Shiru ya ratso wayar har nayi tunanin ya kashe sai naji ya k'ara cewa "gobe ina so kisa kayan dana baki. "

"Wane kaya bayan nazo da nawa?"

" Jadwah pls kisa wanda na baki"

Kasa musawa nayi a hankali nace " to" Murmushi naji ya saki ta cikin wayar

"I will see you tomorrow. Good night "

Bai jira amsata ba ya kashe wayar. Numfashi naja mai k'arfi na ajiye wayar gefe ina Addu'a. Washegari babu wanda ya tashi sai wajen shad'aya sannan aka fara sabgogi bayan an karya. Har d'akin Hajiya Fati naje na gaisar da ita da manyan mata dake gurinta. Da zan fito naci karo da Junaid. Sosai naga mamaki kan fuskar sa muna gaisawa da d'an murmushi kan fuskata na wuce wajen au Amina. Sanda na shiga hira suke sosai suna ganina ko wacce ta b'ata fuska. Ban damu ba tunda ba gurinsu nazo ba nayi wajen Amina dake danna waya. Zama nayi gefenta ina murmushi nace

" Amarya kinsha kamshi barka da safiya"

A takaice ta bani amsa " yauwa" kawayenta suka rushe da dariya da nasan dani suke. Ido kawai na zubawa Amina ina tunanin menene nayi mata haka mai zafi daya sa ta SAUYA min haka cikin d'an k'ank'anin lokaci. Wajejen azahar aka fara shirin tafiya dinner. Nima na miƙe don naje na shirya. Ina fitowa daga wajen Amina na tsaya turus ina kallin Hajiya Suwaiba da suke tare da Hajiya Fati suna magana tsakiyar falon. Gabana ya yanke ya fad'i kafin nayi saurin wucewa ta ganni da mamaki sosai naji ta kira sunana

"A'a Jadwah. Kece"

Yake na d'anyi na d'an rankwafa ina gaisheta. Wani irin farin ciki ne naga kan fuskarta ta nufoni da sauri tana amsawa.

"Saukar yaushe Jadwah babu labari ?"

A hankali nace jiya . Kai ta jinjina ta k'ara cewa " Kina nan har sai an gama bikin kenan? "

Kai kawai na jinjina. " to MashaAllah. Ai kuwa kin kyauta da ki ka zo duk da sanin matsayin ki dana Amina yanzu. Amma zakije duba Balaraba ko?. Kinsan ta dade gadon asibiti bata da lafiya sakamakon faduwa da tayi daga bene. Ta samu karya duka kafuwan ta"

Da d'an mamaki na kalli H Suwaiba ina d'an girgiza kai nace " wlh ban sani ba. InshaAllahu zan dubata kafin na tafi"
Chapter 13 · 0% Book details