← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Banji mai yace ba na d'aga labulen na shiga ina k'ara kiran sunan Amina a raina. Bikinsa da Amina ne yazo?. Amma Amina shine babu labari?. Wai anya wani abu bai shiga tsakanina da Amina ba? Amma ace bikinta guda da Moha na kasa sani?. Wannan abun farin ciki ne a gareni don burinta ya cika ta samu wanda ta jima tana dakon soyayyar sa. Gabansa na ajiye kayan ina jin idon sa a kaina. Juyawa nayi zan fice Gwagwo tace

"Yauwa tunda kazo Muhammadu. Ka kaimun Jadwah kasuwa zata yimin cefane."

Da sauri na kalli Gwagwo dake k'ok'arin ficewa daga d'akin. Wai me Gwagwo ke nufi ne?. A hankali na mayar da ido na kansa har yanzu ni yake kallo. Kasa jurar kallon nasa nayi na juya da sauri na fice daga falon. D'aki nayi kai tsaye ina kumburi na samu Gwagwo zaune a hankali kwance.

"Waini Gwagwo menene sai faman had'ani ki ke dashi?. Mutum sai shegen kallo kaman maye ko kunyar ki bayaji, to kurwata kur"

Baki Gwagwo ta d'an hangame sai kuma tamin dakuwa

"Ungu nan. In bai kalle kiba ni zai kalla?. Kajimun wani shashancin banza. "

Haushi ya k'ara kamani na "kasuwar me kuma zamuje bayan akwai komai a gidan?"

"Aa babu Muhammadu na son cin tuwon masara niyar k'ub'ewa. Kije ki siyo mun k'ub'ewar da nama a dura masa. Da ai da kaina zanje amma tunda gaki ga mota kinga ai yafi sauki"

Wayyo yanda kuka san na rufe Gwagwo da duka wlh haka naji tsabar haushi.

"Wuce maza kije kiyi wanka ki chanza wannan kayan"

Ido kawai na zuba mata. Wai ba ita naji tana maganan auren sa da Amina ba?. Tasan kuwa abunda take tana neman had'ani dashi ta k'arfi da yaji don na gane inda ta dosa. Numfashi kawai naja na cire kayana fice zuwa banɗaki na watsa ruwa na fito. Sanda na dawo bata d'akin naji maganan ta falon suna hira. Shiryawa nayi cikin atamfa riga da sket na dura abaya a kansu. Gashina na nad'eshi kaman gammo nayi rolling mayafin abayar. Y'ar huda na shafa da man leb'e na fito riƙe da yar pose da flat takarmi da suka shiga da atamfar dake jikina light blue. Guri na samu a tsakir gidan nayi zamana saida naji Gwagwo ta kwad'amin kira na miƙe ina k'unk'uni na shiga falon

"Baki gama shiryawa bane tun d'azu ke yake jira?"

Bance komai ba naja na tsaya. Na fara gajiya da wannan kallon nasa. Miƙewa naji ya yi kafin naji wannan muryar tashi mai tsananin kaushi tace

"Bari muje Gwagwo sai mun dawo"

"To a dawo lfy Allah ya kiyaye. Kar ku manta da abinda nace"

"InshaAllahu Gwagwo "

Zuwa ya yi ya wuceni ya fice daga falon na ja doguwar ajiyae zuciya saboda kamshin sa mai sanyi da ratsa juya daya bugeni. Ban yiwa Gwagwo magana na fice daga falon don haushin ta nake ji. Ina fitowa k'ofar gida saida nayi dana sanin fitowa saboda jama'a da suka kewaye dankareriyar motar da yana nufa . Murfin motar ya d'aga sama sannan ya juyo inda nake tsaye. Jiki na rawa na nufi motar kaina a k'asa saboda idon mutane. Na tsani kallo wlh koya yake Jikina ta dinga rawa kenan. Da sauri na shige motar ya mayar da murfin ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya tada ida muka bar layin. Muna hawa kan titin sai ya rage gudun motar ya fara tafiya a hankali kaman mai sand'a. Numfashi na k'araja k'irjina na bugawa. Tunda na shiga motar naki kallon inda yake zaune. Kamshin motar da had'uwar ta ya sanya na jingina kaina jikin glass nata na rufe ido na. Chak naji motar ta tsaya da tafiya na buɗe idona a hankali ina kallan waje. Gefen titin ya faka motar motoci sai wucewa suke suna kallon motar dake fake gefeb titi. Idonsa da naji a kaina na had'iye wani irin yawu kafin na juyo a hankali muka had'a ido dashi. Kaifin idonsa yasa nayi saurin d'auke nawa na mayar windo. Wai menene ke damun mutumin nan ne?. Da deep voice nashi naji ya kirani

"Jadwah "

Yanda ya kira sunan kace don shi kad'ai aka rad'amin. Maganan nashi kana ji kasan hausa bata isheshi ba. Wani iri Ascent ne dashi mai dad'in gaske. Tsigar jikina ta tashi yamma, amma duk da haka ban juya na kalleshi ba.

"You have to tell me where we are going. "

Numfashi na fesar a hankali na juyo muka had'a ido nayi saurin kawar da kai. Dan dole nayi masa kwatancen inda zamu. Ina jin ya yi wani d'an k'aramin murmushi kafin ya tada motar ya hau titi yana bin kwatancen da nake masa. Kaman yanda Gwagwo tace na siyi k'ub'ewa da Nama. A hanya ya tsaya wani katon Mall ya shiga ban bishi ba don na kagu mu koma gida. Ya jima cikin Mall d'in can sai gashi da kaya niki-niki da yaran shagun biye dashi da wasu kayan. Saida suka gama saka komai cikin mota sannan ya shiga muka koma gida. Yana fakin na fice da sauri ina jin wannan mayuj idon nasa a kaina.
Tsakar gida na samu Gwagwo da wasu y'an maƙota suna hira

"A'a har kun dawo?"

"Eh" kawai nace na shige d'aki. Ina jin yanda ake ta shigo da kaya kafij naji muryar sa yana cewa da Gwagwo zaije ya dawo. Matan dake gidan sai hauka suke. Baki na tab'e ban fito ba saida naji tafiyar sa. Na fito nayi kitchen dan d'ura mana abinci. Kai na girgiza ganin yanda Gwagwo da matannan suks dukufa suna cin gashin kaza da lemo ga kayan makuleshe baje a gaban su. Tana cin nama Gwagwo ta kalleni ta d'auko katuwar leda ta miƙo min

"Ungu wannan taki ce kafin muga sauran kayan kuma"

Kabar kawai nayi na koma d'aki na ajiye na fito na d'ura mana abinci ban k'arabi ta kan kayanba. Wajen la'asar ya turo yaron sa aka karb'an masa abinci.

Ana yin sallan Magriba hadari ya had'u sosai muka shige d'aki nida Gwagwo. Allah yasa ma akwai wuta. Kwanciya muka yi bayan munyi sallah Gwagwo najin radio ba d'ago na kalle ta

"Gwagwo "

"Na'am "

Ta juyo tana kallo na " d'azu naji kina maganan Auren Amina? Amina dai tawa dana sani?"

Saida ta kashe radio ta juyo tana kallona sosai taja numfashi " eh ita. Me yasa ki ka tambaya?"

Jikina ya k'ara sanyi nace " Babu komai. Bansan me nayiwa Amina ba auren ta guda ta kasa aikowa a gayamin "

Gwagwo batace komai ba ta zubamin ido kawai. Numfashi na k'ara saukewa nace

"Yaushe ne bikin nasu Gwagwo ?"

"Jibi inshaAllahu za'a fara .haka Muhammadu yacemin "

Kai na jinjina " tafiya ta kamani gobe Gwagwo. Duk da bata gayamin ba ni zanje bikin nata nasan akwai dalilin da yasa bata gayamin ba. Amina ta wuce haka a gurina. Dole naje Gwagwo "

Zama Gwagwo ta gyara tana kallona "anya kuwa Jadwah. Me zakije kiyi?"

"Kinsan bani da kawa sama da ita. Zanje nayi mata bazata"

Gwagwo batace komai ba na juya na gyara kwanciya ban jima ba barci ya kwashe ni. Ido Gwagwo ta zubawa Jadwah dake sauke numfashi a hankali kafin ta yunƙura ta d'auko wayarta ta danna kira. Bugu d'aya ya d'auka

"Gwagwo "

Ya kira a hankali da muryar barci. " Taheer na tashe ka kana barci?"

"A'a Gwagwo "

"To kanaji yarinyar tasan zancen auren ka da Amina don ta ce gobe zata je. Nasan halin Jadwah da kafiya tunda tace zataje dole sai taje . Yanzu ya za'ayi kenan?"

Numfashi ya sauke mai zafi ya mayar da manyan idonsa ya lumshe. Sam bashi da burin zuwa bikin nan Kwata-kwata. Burin sa ya zauna a nan yana kallon wannan kyakkyawar fuskar tata dake so fierce kaman tiger.

"Babu komai Gwagwo nima goben zanje azaren sai mu tafi tare "

" to shikenan zance mata ta shirya ku tafi tare da tabi motar haya."

"Gwagwo bata buɗe wayar dana bata bane?"

Da d'an mamaki Gwagwo tace " au ka siyo mata waya? Yoo ai ita kanta bata sani ba. Bari da safe zansa ta fiddo da. An gode kaji Allah ya k'ara buɗi da arziƙi "

Da wannan sukayi sallama yana jin Gwagwo tamkar uwa daya rasa.

Washegari ya kaman alhamis. Ban koma barci ba bayan sallan asuba nayi tilawa da zikiri da gari ya fara haske na fito gyara gidan na d'ura mana abinci. Dana gama ba shiga wanka sai bayan na fito ne Gwagwo ta tashi daga barci. Kayana da zan tafi dasu na fara shiryawa cikin jaka sannan na shirya cikin atamfa maroon d'inki riga da sket. Duk abunda nake Gwagwo na kallona batace komai ba saida na gama shiryawa ta d'auko ledar dana ajiye ta buɗe tana lalube. Saiga kwalin waya ta fito da ita mai shegen tsada.

Ina kallo ta buɗe had'addiyar iPhone ta miƙo min. Da mamaki sosai kan fuskata na k'arba ina juya wayar tafin hannuna.

"Kunna mu gani"

Ban musa ba na kunna wayar .anyi set d'inta gaba d'aya don harda sim a ciki .cike take kuma da chaji. Karb'an wayar tayi ta saka number ta kira sannan ta miƙo min tana cewa

"Yauwa kinga na samu hanyar da zanji yanda ki ke sauka"

Na kasa cewa komai sai ido kawai dana zuba mata cikin matsanancin mamaki. Mamakina bai karu ba saida naji muryar Moha ya shigo gidan cikin shiri Gwagwo na cewa

"Yauwa Muhammadu k'araso. Maza ki wuce ku tafi kar kuyi rana"

Tana maganan tana turani ina binta da sakakken baki. Har bakin mota Gwagwo ta rakomu tana yima Addu'a.

𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.

𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎

𝐏𝐆 11.

𝙽𝙾𝚃𝙴 / sabods gudun rikicewa nayi wannan d'an notice. JORDAN kowa yasan jirgine za'abi ba mota ba. Amma ina so ku gane wannan JORDAN tawa kirkirar ce 😂. Don haka kar a rikicewa kusa tafiya zasuyi da baifi awa 4 ba a mota , to make it all short. Da fatan kun fahimci abunda nake nufi?. Ok?, OK 👌.

Alright on with the story.
Chapter 12 · 0% Book details