← Book details Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Sauyin Lamari Part 1 Compplete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Jadwah na rawa ta matsa da sauri ta samu guri ta zauna. Kallo Moha ya watsa mata ya wuce gurin Amina dake kallonsa kaman tayi bindiga. Wannan wane irin tozarci ne da cin fuska?. Duk irin cin amanan da tayi mata bai isheta ba sai ta nunawa duniya ita cikakkiyar butuluce mai cin amanar abota?. Har Moha ya k'araso inda Amina ke tsaye tana kallonsa da jan ido. Wuceta kawai ya yi ya samu guri ya zauna abunsa bai damu da yanayin Amina ba. A sanyaye ta zauna kar tozarcin ya yi yawa .suna zama kuwa guri ya kaure da hayaniya. Tambayar kowa a gurin shine wacece wannan suka zo da ango mai mamakon a ganshi da amarya?.

B'angaren Jadwah abun ba'a cewa komai kaman tayi tsuntsuwa ta bar gurin. Tana ganin yanda mutane suka kasu kashi kashi. Wasu na zaginta wasu na ganin sun dace ita da ango, wasu na jifan ta da mugun kallo da harara. Kujerar dake gefenta Lameen yaja ya zauna yana d'an murmushi yace

"Karki damu da abunda suke cewa. Babu wanda ya isa ya hanaki zuwa da Moha wajen bikinnan don kin fisu right dashi"

Maganan sa ta d'aure mata kai amma batace komai ba. Zuwa wani d'an lokacin aka cigaba da sabgogi na harkar biki. Koya ta juya idonta sai ya tsarke dana Moha ,sai tayi maza ta sauke idon ta. Banda Moha harda Amina da kawayenta dake jifanta da wani mugun kallo na tsantsan tsana. Minti talatin da zuwansu aka fara ci dasha kafin a fara cashewa. An kira ango da amarya suzo su d'an taka. Amina ta k'anannade Moha suna bin slow music da aka saka musu yana tashi a hankali an rufe su ana musu likin kuɗi. Bayan sun gama suka koma inda suke zaune. Jadwah ta fara gajiya da kallo da ake binta dashi. Tana kallon yanda maza da dama suke son suzo suyi mata magana amma Lameen ya kasa ya tsare kaman mai bata tsaro. Da zarar wani ya yunƙuro zai jefi da mugun kallo dole ya koma inda yake zaune. Karfe shad'aya aka gama dinner aka fara k'ok'arin tafiya. Da sauri Jadwah ta miƙe ta fito daga Hall d'in Lameen ya biyo ta da sauri. Fita tayi ta tsaya harar gurin tana kollan yanda kowa ke shiga motar daya zo. Tunani ta fara na yanda zata koma gida. Shawara ta yanke tayi hanyar waje Lameen yasha gabanta.

"Ina zaki kuma? "

A hankali kanta na k'asa tace " zanje na samu mota ne a waje"

"Aa wace irin mota kuma ga wanda ku ka zo da ita?"

Kafin tace wani abu muryar Moha ta doki dodon kunnen ta. " meke faruwa?" A hankali ta juyo suka had'a ido da Amina dake gefen sa kaman zata shige masa ciki. Kallon data watso mata yasa ta sauke ido kasa da sauri. Sabad'in d'azu, yanzu wata dankareriyar Audi ce jeep baka ta faka gabansu. Moha ya matsa ya buɗe motar. Amina ya fara kalla murya a dake yace

"Get in"

A hanzarce ta shige motar babu musu. Juyowa ya yi ya kalli Jadwah kafin ya shiga bayan suka had'a ido da Lameen. Da sauri Lameen ya matso kaman zau turata yace

"Oya shiga- shiga muje we don't have all day"

Yanda yake matso ta yasa babu shiri ta shiga motar a hanzarce. Sanyi da kamshin motar ya ratsa ta ta sauke ajiyar zuciya. Ko kad'an bata juya ta kalli Moha da Amina dake gefenta ba duk idansa da take ji kansu. Idona nuwa da d'aya ke d'auke da burning hate d'aya kuma da wani burning lust.

B'angaren Balaraba tafi kowa takaicin abunda ke faruwa. Tunda taji zancen auren Moha da Amina ta d'aga hankalinta matuƙa. Bakin ciki kaman zai kashe ta. Ta lura Asiya Sam bata damu ba don yanzu ta fara watsar da LAMARIn Moha tunda tana tare da Jojo da sauran y'an harkallanta suna bad'alarsu. Randa ta kirata saboda Auren baran baran suka rabu a waya. Bakin ciki goma da ashirin ga rashin k'afa gashi yanzu komai ya daina tafiyar mata yanda take so. Balarabe tun kwanciyar asibiti sau biyu yazo dubata don shima ya fara gajiya da ita. Duk da haka yana bata kulawa yanda ya dace .Komai yanzun ya daina tafiya mata daidai. Allah Allah take ta samu lfy ta koma wajen Jalli. Ita ta tura Suwaiba gidansu Amina don ta tabbatar da zancen auren shine sanadin data ga Jadwah a gidan bikin.

𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.

𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎

𝐏𝐆 13.

Basu jima ba a kan titi saboda gudu da motar take suka isa k'ofar gidansu Amina. Motar na fakin Jadwah ta fara k'ok'arin buɗewa ta fice saboda yanda take jinta tension da ya yi yawa cikin motar, kaman an kunna mata wuta duk uban Ac dake aiki. Ta gefen idanta take lura da Amina dake kwance kan k'irjin Moha kaman zata koma cikinsa. A hanzarce ta buɗe motar ta fice tun kafin wani daga cikin su ya yi yunƙuri. Tana fitowa wasu motocin na fakin k'awayen Amina da sauran mutane suka fito. Dukkaninsu da kallo suka bi Jadwah data wuce da sauri cikin gidan kaman wata barauniya. Da ido ya bita harta b'ace ciki gate ya d'an sauke ajiyar zuciya a hankali. Amina dake kallonsa kaman tayi bindiga tsabar kishi tace

"Wai me ka ke nufi dani ne Dear? Wane irin cin mutunci ne wannan ranan farin cikin mu ka mayar dashi na bak'in ciki. Ko ba komai ai ka nunawa duniya nima ina da matsayi mai girma a wajen ka tunda yau ranan mu ce. Amma shine don cin fuska ka barni ka tafi gurin tsohon hannu?. Yanzu da wane ido ka ke tunanin zan fuskanci irin wannan cin mutunci?"

Uffan baice mata ba saida ta gama b'ab'atun ta taja neman rushewa da kuka ya bata amsa da kalma d'aya.

"Saida safe"

Kaman zuciyarta zata fashe haka Amina taji wasu hawayen bak'in ciki suka suka mata fuska. Juyawa tayi k'ofar gidan su ta hango su Saudat tsaye suja juran fitowar ta. Dole ne ta nuna musu itama tana da babban matsayi mai girma wajen sa. Dukkanin wata kuryar ta ajiye gefe ta juyo ta kalli Moha dake kallon gaba fuska babu wani emotion. Wani irin shammatansa tayi ta rungume shi tsam yanda kayanta. A d'an razane kaman wanda aka watsawa shock ko irin kashin nan mai d'uyi ya fara kici-kicin kwacewa. Saboda y'ar kokwar da suka yi head d'in ta ya zame rigar ta d'an cukwikwuye ta gaba . Idan ka kalla a naka b'angaren babu abunda zai hana kayi tunanin wani abu ne ya faru tsakanin su. Yana samun damar cireta daga jikin sa ya watsa mata mugun kallo. D'an far tayi da ido bak'in ciki cikin ranta kaman ta had'iye zuciya. Ita Moha ke kyenkyami kaman ya tab'a kashi?. Kwafa tayi cikin rai daga gobe ne zai shiga hannun ta sai yanda tayi dasho don a shirye take tsab. Juyawa tayi ta fice daga motar riƙe da head nata a hannun tana d'ahxhhhdn gyara gaban rigarta. Ai kuwa su Saudat na ganin yanda ta fito suka fara shewa da ihu Amina ta wuce da munafukin murmushi kan fuskar ta ita dole akwai abunda ya faru. Kai tsaye b'arin su suka nufa tana kissima cin mutunci da zatayi wa Jadwah a daran nan.

Jadwah kai tsaye ta shige d'akin da aka mata ma sauki. Y'an matan da suke kwanciya tare ta tarar zaune kan gado suna magana. Ganinta cikin d'akin ko waccen su ta tsayar da abunda take suka zuba mata ido. A hankali wuce su ta nufi jakatar daidai wayarta na ringing. Sunan Moha data gani rad'an jikin wayar yasa taki d'agawa ta zauna tana cire takarmin k'afar ta. D'aya daga cikin y'an matan mai suna Baby tace

"Am Jadwah ko? "

Kai Jadwah ta d'aga tana kallon ta kafin ta d'an d'aga kai. Baby ta k'ara gyara zama tace

" Don Allah menen had'in ki da Angon Amina? Wanki ne ko saurayin ki? Mutane nata fad'an maganganu kan ki. Kan kinzo bikin Amina zaki kwace mata miji kaman yanda ki ka saba yiwa mazajen wasu?"

K'irji Jadwah ta dafe tana kallon ta da ido a waje. Ita ce ake kira da sunan karuwa ko me, idan ta fuskanci inda magananta ta dosa?. Kaico ita Jadwah da ace tasan abunda zai faru kenan wlh da batazo bikin nan ba. Hawaye suka tarar mata a ido ta buɗe baki zatayi magana Saudat da Amina da wasu y'an mata suka shigo d'akin. Kai tsaye kan Jadwah suka yi Saudat bata jurar komai ba ta cire hannu ta d'auke Jadwah da wani b'arin makauniya. Bata bata damar jin zafin marin ba ta fisgi gashin kan Jadwah da k'arfi tsiya saida ta saki ihu ta kai hannu ta dafe na Saudat. Yan matan nan duk sukayi chirko-chirko suna kallon abunda ke faruwa. Hawayen dake kwance idan Jadwah ya gangaro kuncin ta. Amina dake gefe ta matso tanaji itama kaman ta rufe ta da duka. Da hannu ta nunata tana zuba uban huci tace

"Baki cika y'ar iskar karuwa ba saj kin hau kaciyar Moha gaban ido na sannan zansan cewa ke annamiya ce butulu mai cin amanar abota. Kinsan cewa ina son Big Brother amma don tsabar munafurci ki ka zagaya aka aura miki shi a b'oye ban sani ba saboda munafukaci. Waya santa hanyar da aka bi har yace yana so?. To ki kard'e kunnen ki kiji. Nida Moha mutu ka raba takarmin kaza. Idan kinsan wata baki san wata ba. Ki shirya zama dani a matsayin kishiya ba k'awa ba , sai kinyi dana sanin auren wamda nake so. Bake y'ar iska ba?. Ki nunawa duniya ke k'arshe ce a fagen yaudara a annamimanci? To mu zuba nida ke"

Tsananin mamaki da shock daya ziyarci Jadwah yasa ta sandare a tsaye bata iya motsawa sai idonta da k'irji ta dake masifar harbawa sai ka tsorata. Hankad'a ta Suka tayi da mugun k'arfi ta daki bango yaraf ta koma ta zauna idonta na kallon kasa. Duk cikin kalaman Amina kalma uku ke mata yawo a kwakwalwar kanta. KIN AURI WANDA NAKE SO. ANNAMIMIYA, KISHIYA?. Maganan Saudat taji tana k'arasawa Amina
Chapter 15 · 0% Book details