← Book details Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yana murda kofar yaga lubnah ta zura da gudu zuwa toilet hartana kokarin faduwa,dariya tabashi sosei duk dadai beisan silar gudun nataba,ganin shine yasa tafashe da kuka tana cewa,kaima kaga aljanin ko?dan allah karufamin asiri gadawo da shi sun daukeshi waiyo ni lubnah.......sosei ahmad kemata dariya harda rike ciki yace,wai wana aljani? *ASHMAN* ne kuma yana daki yana bacci kijira tashinshi zakiyi bayyani dansaiya saba miki wlh......wallahi bani sake shiga dakincan aljani fa nagani....dariya Ahmad yayi yace,pls kiyimin bayani yanda zangane....nan lubnah ta kwashe tagaya masa komai har magani datasa.....ohoo allah yakara maganinki gwara dakikaga haka,tunda basirarki takare bara nafada miki dalilin dayasa kikaga haka,ni gidana ba aljanu gurin bokan dakikaje shine allah yanuna miki kuma ya tsare abokina daga sharrinki dan beitaba zunaba shine allah yakuma tsareshi seiki kiyayye nangaba kuma kijira haduwarki dashi.

"Sosei lubnah ta gamsu da maganar Ahmad nan tadan samu nutsuwa,kaya tasamu tasa adakin Ahmad dayake yana ajiyewa sbd 'yan matansa dasuke zuwa,tana zurawa bata dauki komaiba da duk abubuwanta suna dakin da gudu tafita agidan tayi hanyar gidan boka(o ni 'yasu mai hali baya fasa halinsa😏🤔lubnah baki dadaraba kenan)

"Bangaran *ASHMINAL* bayan sun kammala cin abinci kowa yaje yayi aikin gabansa,bayan takammala aikinta takoma dakinsu dan takwanta danji kanta namata ciwo,tana kwanciya bacci ya dauketa.

"dad ne keta balbalin fada,yanzu kikasan inda yatafi kunsawa yaro ido gashi yafice cikin fushi bansan inda yajeba duka phone dinsa kashe haba dan allah uanzu inyashiga wani halinfa kunbi kusawa yaro karan zuka wallahi layla duk abin dayasa my son seikimyi nadama.....haba alhaji kasandei dawayansa insha allahu ba abin dazai samaisa kawaidei......kawaidei me?kinga layla bansa surutun banza kimin shiru yanzu fa ji 10:00am fa babu alamarsa tun safe yafita aiduk leifinki ne,to anma alhaji yabaza a dunga tsawatar masaba seide yayi abin dayayi ra'ayi aihakan beidaceba,banza dad yayi da'ita ya lula duniyar tunanin dansa ko wana hali yake ciki.

"Bangaran *ASHMAN* sei 11:00am ya tashi Ahmad yagani zaune kusa dashi ya kura masa ido,dan tsaki yayi yace,yadai kake wani kallo na lpy dei ko?murmuswa Ahmad yayi yace,kai ai zan tambaya ya jiki?jikin mai kuma?ni lpy nake yashige toilet abinsa,wanka yayi yayo alwala yanafitowa ya mayar da kayansa yatada sallah,bayan ya kammala,kallon ahmad yayi yaga sei kallonsa yake yace dallah mainewai kake tawani kallo na?Nothing kawaidei ra'ayin haka nayi,ok naji ina wannan yarinyar take seinaci uwarta wallahi harni zatasawa maganin sha'awa ko,au dama kasani?nasani mana seide kushewar hankali bakomai nasaniba pls tana'ina?aita fice tun dazu,ok zamu hadune zata gane kuranta,mikewa yayi yace ninayi gida seimun hadu,Ahmad yace,haba dare yayifa ka kwana.....ni zankwanan maka cikin gida kudamaini da nishi nakidin.....dariya Ahmad yayi yace,yau bakowa hutu nake,kaga tafiya ta ni bazan kwanaba,sallama sukayi yawuce gida,koda yaje Direct part dinsa yanufa bei shiga cancikin gidaba sbd yana fushi.

_Washe gari_ yauma ammi ce zaune itakadai tana lazumi idonta lumshe kamar mai bacci,yan aikin kedan ne keta shigowa suna gaisheta hannu kawai take daga musu,dad ne da momy suka fito durkuswa sukayi suka gaisheta amsawa tayi ba yabo ba fallasa,gyaran murya dad yayi yace,ammi yaron nanfa shiru har yanzu....harara ammi ta zuba masa tace yooni ina ruwana Abubakari?bakun lalata yaroba ba ruwana dan haka can tadamaiku....dan allah ammi kiyi ardu'a kema....allah ya sauwake inzauna yiwa wanda yazagamin uba ardu'a wallahi banyi bazan bata bakina da agansa da kar agansa bandamu ba yawan tambadarsa yatafi ai..... *ASHMAN* yashigo ko sallama babu yana bankawa ammi harara,jiki na rawa dad yatashi ya rumgumaishi yana shafa kansa cikin so da kauna yace,my son inaka kwana kasamu cikin damuwa,pls dad bansa tambaya yunwa nakeji muje muyi break,batare da yadamuba yace to yaron kirki maxa jeka dining area gamunan muma,wucewa yayi yana shan mur,tsaki ammi tayi,tashi sukayi duka sukayi dining har ammi.

"Tunda tagansa zaune kan dining jikinta ke bari harara kawai yake zuba mata,shirya komai tayi ta durkusa tace,barka da safiya ranka ya dade,bugeta yayi da kafa tare da take mata hannu,kara ta saki hakan yayi daidai da karasowar su ammi,sarei taga abin dayayi mata ta share dan ita tasan maita taka da sauri

*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌹🌹🌸🌸🌼🌼🌺🌺
🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀😭🙆🏻🙆🏻
*"SANADIN GIDAN AIKI"*
🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀😭🙆🏻🙆🏻
🌹🌹🌸🌸🌼🌼🌺🌺

~Written by saleehat{s&s beauty}~

_*Ina mika sauko ta'aziyya ta gareki halima20 na babban rashin 'uwarki,allah ubangiji yaji kanta da rahama ya gafarta mata yasa ta huta ubangiji yakai haske kabarinta kukuma allah yabaku hakuri da juriya narashinta yasa muyi kyakyawan karshe ameen ya allah😭😭mutuwa mei yankan kauna allah yasa mucika da imani ameen🙏🏻*_

_my fans am sorry da mistake din danayi naji wasu na tambayata page 35-40 nayi posting dinsa tun shekaran jiya abin dayasa mistake din number nayi amaimakon nasa 35-40 seina sa 30-35 duk wanda ya duba zeiga badaya baneba guduba zaku gani thanks_

_"zakuji 2days kunjini shiru wallahi mai gida rangida ne ba lafiya kunga kuwa oga ba lpy ba posting kenan,anma Alhamudillah yasamu sauki zakujini kulli tnx._

_*happy jumma'at mubarak to all muslims.*_

_page 40-45_

........tsinkawa *ASHMINAL* mari yayi har uku wanda seide kawai jinsa tayi yiwa saukar aradu bakaramin firgita tayi da marinba dajin radadi mei zafi a face dinta sbd jin mari har uku lokaci daya,hawaye ne kezuba a idonta tana dafe da kumcimta wanda hannunsa yafito rudu-rudu.......ammi ce tace,lallai kacika tantiri ai inde kai mara kunyar gaskene nizaka mara ba'itaba tunda dai ni nadakeka karshen iskanci kanunamin kai fitsararan gaskene shine ka rama akaina mara tarbiyya kawai mtwsss.

"Sosei ran momy yabaci ganin lokaci daya fuskar baiwar allah ta tashi ga shatin yatsu ya kwanta abinka da fara fuskar tayi jazur cikin bacin rai momy tace,haba my son dan ammi tama hukunci shine zaka mari baiwar allah,ka kyauta yanxu?.....kinga layla dan allah kideina masa fada kubarshi ya karya kina ganidai jiya daya fita gidan nan bamu samaishiba mun tsorata kuma leifi akamasa to yau inya tafi mukasan maizai kasance pls ki qyele yaro yayi break jinake gabanki yace yunwa yakeji......ammi ce rike da haba tana tafa hannu tace,oni fadimai yauni naga tsiya wato kai Abubakari bakaso atabo dan gwal ko?kadaurewa yaro gindi ko?bakasan leifinsa ko?yauni naga tsiya daganin inda ake daurewa yaro gindi to wallahi dagakai harshi ku kiyayye yoo ai bansan layla bata da leifin komaiba gurin lalacewar danka ba ashe kaine kake d ruwa da tsaki akan komai ka kyauta ai kajira hukuncin dazan yanke tana fadar haks taja hunnun *ASHMINAL* warce keta hawaye ga azabar fuska gata ruwan tea.

"Mtwss gaskiya dad so ake akasheni agidan nan ya za'ace wulakantaciya mara Asali mara tushe agabanta za'a wulakantani sanadiyar araina ni gaskiya bazei yiyuba kuma wallahi anyi na farko anyi na karshe no respect bamutunci daga yau wallahi dan bazan dauki rainiba......cikin lalama dad kemasa mgn"sorry my son zandau duk hukunci daga yanke badamuwa kaji kayi hakuri my heartbeat komai kace daidaine.....sosai ran momy ya baci domin itama abin yaronta yafara isarta dakuma samgartar dayake da da samu tayi yawwa ayanzu duk hukunci da ammi tayanke ba ruwanta su suka jawa kansu dagashi har dad dinnasa haushine ya cikata tabar wajan cike da takaici,shikwa dad sei lalashi yakeyi dan duk dai dansa tilo yahuce yace zei tura masa da 50millions ta Account dinsa,sosei *ASHMAN* yayi murna badan bashi da kudin baneba kawai yaji dadin kyautar dan shima yana da kudi masu mutukar yawwa kuma duk daga hannun dad dinsa sukafito.

"Direct dakinta ammi ta nufa da *ASHMINAL* domin ran ammi yayi mutukar baci,cikin lalashi tace,kiyi hakuri diyar kirki ki share hawayenki kinji diyar arziki komai maiwucewa ne kitsaya ki saurari abim da zance dake yanzu,share hawayenta tayi tana sauraran ammi,yawaa diyar arziki yanzu dai nasan matsayin kaka kika daukeni ko,gyada mata kai tayi alamar eh,yawwa to yanzu nabaki abu ko umarni komin muninsa ko kyawunsa zaki karba? Murmushin karfin hali tayi domin yanda kanta kesara mata tace,tabbas zan amsheshi komin muninsa domin kinsoni sona hakikka fatana nasamu abin da zansaka miki dashi dan haka domei kikace nayi miki zanmiki kamar uwar data haifeni haka zam amsheshi hannu bin biyu kifadi maganarki kanki tsaye ammi nayi miki alkawarin biyayya insha allah,murmushin jin dadi ammi tayi tace yawwa yar albarka nagode sosei kinji allah yayi miki albarka tashi kije gobe zan gayamiki komainene kinji,to tace tare da mikewa zata fita ammi tace zoki amsa magani kisaka ahannun da muguncan yadake ki amsa tayi tasa ta fice tana tunanin maganar ammi cikin ranta tace,komai nene komai zata gayamin goben? ohoo nibansaniba haka harta tafi bangaransu tana maijin kaunar ammi har ranta.

"Yau *ASHMAN* babu inda yaje ko gidan Ahmad beisamu zuwaba yana daki yana latsa laptom dinsa hankali kwance" bayan salar isha'e yakira Ahmad awaya dagawa Ahmad yayi tare dacewa.

"Hello my friend ya akayine hope komai lpy dai ko ya gajiyar jiya y......?

"Mtwss wallahi suruntunka yayi yawwa friend to komai normal ya'akayine?

"Mumuswa Ahmad yayi yace,normal wallahi,dama yanzu nake niyar kiranka naji lpy baka zoba?

"Wallahi lafiya kalau kawai dai banyi niyar zuwabane ba,shegiyar yarinyarnan tazo kwa?

"Au lubnah wai? Atakaice yace um!

"Wallahi bata zoba anma takirani tace kazo nemanta nace aa shine tace taza shigo gobe! Ok shikenan nima goben zan shigo byee,beiji mai Ahmad zeiceba ya katse wayar.

"Ammi ce zaune dad d momy agabanta,fuska ba walwala tace,abin danasa nakiraku hukunci nayanke kuma zan zartar dashi koyayi muku kobaiyi mukuba dole abi kuma a amsa domin nayi dogon nazari, momy ce tace,haba ammi aikin isa damu koma maine zamubi insha allah,shima dad cewa yayi,insha allah ma za'abi!
Yawwa dama kan tantirin dankune wanda lalacewar naga tayi yawwa! Gaban dad ne yace ras domin yatsorata,itakuwa momy ko ajikinta domin sai anfara hukuntashi qila zei shiryu! Abisa dogon nazarin danayi naga danku bazei shiryuba kullin iskancinsa karuwa yakeyi kuna biyemasa shiyasa nayanke hukunci akansa kuma dole shima yabi dan ubansa,ni fadima inde na'isa daku nayanke hukuncin hada auransa da fadima takwarata mai aikin gidan nan wato *ASHMINAL*................

*"hhhhh ana dara ga dare yayi fa"shin ya dad da momy zasuji maganar ammi?*

*"shin ASHMAN zei amince ko kwa?*

*"shin ASHMINAL itama zata cikawa ammi alkawarin data dauka ko kuwa zataqi?*

*In hakan takasance waya zamansu zei kaya?*

_amsar tambayarku na cikin book din *SANADIN GIDAN AIKI* kudei kasance dani domin cin kannun labari dan yamzu akafara jamu jedai👍🏻_

_*more Comment more typing*_

~#pls share~

~Written by saleehat{s&s beauty}~
Chapter 7 · 0% Book details