← Book details Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"bata dau lokaci ba ta kammala dakin lubna tashiga taga bata ciki gyara mata tayi fes tasa turare tazo ta haura sama tana shiga palour ba kowa aciki gyara shi shima tayi fes tukunna tashiga bedroom din.......gaban tane yafadi ganin lubna zigidir azaune....wata tsawa lubna ta daka mata tace!kan bala'e dan bura'ubanki wayace ki shigomin dakin miji shegiya tsinanniya mayya kawai ke zanci kan ubanki fa yar iska,wuce toilet kihada min ruwan wanka kizo kuma naci ubanki! jikinta na rawa tawuce tahada mata ruwan wanka tafito.....cakumota lubna tayi ta zabga mata lafiyayan mari tare da zuba mata rankwashi wanda har tsakiyar kafarta tajishi!dan uwarki daga yau nakuma ganin kin shigomin daki kai tsaye saina 6a6alaki........kuka takeyi cikin kunar rai zagin iyayenta da akeyi tanajin zafin abin sosei bazata iya jurewa ba kowa ya dunga zagin iyayenta cikin aro jurumta tace!kiyi hakuri kidaina zagin iyayena domin ba abin da sukamiki duk mai zakimin kiyi shi iya kaina zan jure anma zagin iyayena da kikeyi baxan iya jurewa ba domin suma iyayene kamar kowana iyaye.........

"wani wawan mari taji anzuba mata kafin ta ankare taji ankuma sakar mata wani....cikin masifa da tashin jijiyar wuya yace!iyayenki din banza kidahumai jakuna 'yan iska iyayenki basu da daraja basu da kima ko kadan bazan hofine iyayan naki kuma inda sunsan darajarki da kimarki su iyayene nagari da kinzauna agabansu mana banza 'yar iska iyayanki karuwai ne suma...........tana rizgar kuka takuma aro jarumta ta mike tare da daga masa hannu tace!yallabe ka zagesu ada anma ayanzu inzaka zagesu saina kare hakkin iyayena yanda kakeji da naka haka nakeji danawa duk da bana gabansu wallahi ina kaunar iyayena yallabe kaji tsoron allah........duka ya rufeta dashi kamar ya ilata ta daker tasamu tafito daga dakin kiris ne bata hantsila kasaba ta sauko daker tashige part dinta tasa key.

"zubewa tayi abakin kofar tana rizgar kuka!saida tayi mai isarta tashiga toilet tayi wanka,kayan ta mai kyau tasamu tasa fuskarta duk shatin mari haka ta shirya tana daga daki taji muryar ammi da sauri tafito palour tana murmushi nunaalamar ba abin daya faru.......tunda tafito ammi ke kallonta cike da tuhuma ganin fuskarta jazur ga kuma shatin yatsu a fuskarta....karaso wa tayi tace!ammi barka da asuba,ke waya dakeki naga kamar mari afuskarki?uban waye gayamin inci masa uba dan bazan lamunci duka ba"waye fadimani?Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace!ba kowa ammi shatin bacci ne fa......karya kikeyi fadima baxaki fadamin ba kenan......dakatawa ammi tayi ganin *ASHMAN* suna saukowa daga step shida lubna sai dariya sukeyi haka sukazo suka zauna batare da daya acikinsu ya kalli su ammi ba.

"cikin fada ammi tace!sannu 'yan iska marasa kunya kai yanzu kwanan diyar nanne anma dan rashin imani shine kaje ka kwanada wannan mai sufar angulu din ko?to gaji tsoron allah shashashan yaro mara tunani kaje ka bige gurin karuwa ko.....da sauri *ASHMINAL* tace a'a ammi ba haka banebafa shiya taramu jiya ya tambayeni ya za'ayi shine nace yafara kwana gurin 'yar'uwata kedaina fada bashi d laifi tafada bakinta na rawa wani kuka yataho mata daker ta danneshi....batare da ammi ta gamsuba tace shikenan anma ai basu da kirki kosu gaisheni wlh saina gyara muku zama.....tsaki lubna tayi tace!kafin ki gyaramin saina fara gyara miki tana fada tashige part dinta haka yatashi shima yabi bayanta sukabar ammi tana jaraba.

"bayan sati daya azabar da su lubnasuke bawa *ASHMINAL* tazarce misali dan asubar fari take wanke motocin *ASHMAN* ta gyara farfajiyar gida ta wanke ko ina na farfajiyar gida yanda babu wanda zaigani(da masuyi anma dan mugunta ita yasa takeyi)daga bisani saita dawo cikin gida tayi sauran 'aiyukan wuya dan kan tana shanta tazama kamar baiwarsu lubna iskancin ta take tata komai zatayi *ASHMINAL* take sawa daidai da iske bata daukewa saide ta sata ga duka da zagi da hantara da take sha agurinsu tayi baki ta ramai duk gyaran jikin nan wahala ta gogeshi mari kuwa shan shi takeyi ba adadi gashi tun randa ammi tazo bata dawo ba kuma suma basuje ba hakan yasa tazama baiwar karfi da yaji rashin imanin da *ASHMAN* yake nuna mata yayi yawwa bakowane mutun neba zai iya hakanba so biyu suna fita da lubna da shi da ita anma insun fita duk inda sukaje sai sun wulakanta ta cikin bainar jama'a sun zageta sun hattareta sunyi mata gori wasu su tausaya mata wasu suyi dariya saide tayi kukan ta ta koshi gashi tanason ganin Aisha kawarta babu dama dan yahana kowana dan aiki shigowa gidansa wanda ammi da momy har dad basusan da hakaba sbd nuna musu yakeyi suna zaman lpy sosei"yauma fita zasuyi wanda lubna ce ta tsara hakan tasha ado tayi kwalliya ta murje tayi kyau abinta uban gayama yayi kyau sosai *ASHMINAL* ma ba laifi anma sun hanata tayi kwalliyahaka tafito suka fita zuwa wani katafaran gurin shopping.

"suna zuwa gurin lubna taho zaginta dacewa!dan uwarki wazai riken jakar hannu na ni baiwarki ce komai? jiki na rawa ta amsa suna gaba tana binsu abaya! haka suka dunga lodar siyaya suna tila mata domin ita saide tazama 'yar kallo subulun goma *ASHMAN* baya siya mata"saida lubna ta daidaici daidai inda mutane sukafi yawwa ta zabgawa *ASHMINAL* mari cikin fada da masifa tace!waike wata irin daba ce mara hankali maiyasa baki da tunani ke jakar inace ina tafiya kina takani ta baya(tsabar makircine na lubna dan ta kaskanta ta agaban jama'a)koda yake shidama mara Asali haka yake duk hallacin da akayi miki saida kika watsa mana kasa a ido kika kashe mana uba kika yo cikin shege kikace wana ne yamiki babu yanda muka iya muka yarda wallahi baki da mutunci da adalci kuma saikinga sakaiya munafuka kawai......jitayi wutar kanta ta dauke da abin da lubna ke fada mata "duk ayaushe tayi hakan?tambayar da takeyiwa kanta kenan!aikwa batayiauneba taji mutanan gurin sun hau zaginta suna allah wadai da halinta harda masu cewa kyan dan miciji ashe muguwa ce zagi da tsinuwa ta shashi haka mutane suka hau saukar pic dinta su yada a social media kare fuskarta takeyi *ASHMAN* yabuga mata tsawa ta bude haka tabude suka gama dauka atake agurin mutane sukadau yadawa suna dogon sharhi kan abin da lubna tafada aikwa abu har yayadu kowa aibata baiwar allah yakeyi warce bataji ba bata ganiba.

"kuka tashashi babu adadi ga tambari na biyu da *ASHMAN* yayi mata wanda baxai taba goguwa ba azuciyar tatabbas wannan mugun tabone mai ciwon gaske da kunar zuciya!ran lubna da nasa fes ko dar basuji kuma baiji haushi kan abinda lubna tayi mataba saima dadin da taji"suna kammalawa sukayo gida,komai saida ta loda takai part din lubna ko tsinke babu nata shikuma ya shiga part din su momy.

"fadan ammi tajiyo tanayi tana kuka!tsaki ya buga yashiga cikin palour momy yagani tsaye da waya ahannu ta sai hakuri take bawa ammi......yana shiga momy tace!mai ka aikata my son?abin dakayi ya dace?wannan wana kalar kazafi ne kayiwa baiwar allah?wanda kayi mata babban tabo azuciyar ta!why my son?kana da imani da hankali da tunani kuwa?kasan mai zaga girba nangaba kuwa?kayi ahankali 'dana kasan mai kakeyi kaji tsoron wanda ya hallice ka wallahi inajiye maka tsoron ranar nadama lokacin dabata da anfani kadaina shigarudin shadan kayi tunani katuba kaji kan baiwar allah......gaskia momy kidaina min baki kuma bazanyi nadama ba ko kadan sannan ita yarinya aibata da hali yana fada yafice a part din! kuka momy ke sha tana tausaya wa baiwar allah anma ita fadawa dad bazai yardaba goyan bayan dansa zaiyi ardu'a ita kadaice mafita allah ya shiryi mata *ASHMAN* masu hali irin nasa yasa sudaina anma ita kanta batayi alfahari da tarbiyyar da yasamu ba kullin cikin nadama takeyi da biyewa dad datayi tasan rayuwar dansu naciki hatsari!tasan duk daran da dadewa zaiyi nadama lokacin daba da anfani gashi tanaso ta nusar dashi hanya anma yaki tankwaruwa yayi nisa bayajin kira allah shi kadaine zai shirya mata *ASHMAN* dinta................

_my fans kunajin dadin book dinnan ko kwa?barda sankai kojin kunya ta kufadamin gaskiya lbrn natafiya yanda kukeso"ko akasin hakan?domin inaso na fadakar yanda masu hali irin haka sucanja kamar yanda nafada da farko badan cin zarafin kowana rbuta ba saidan na fadakar har yanzu akan hakan nake🥰🥰_

_*more Comment more typing*_

~#pls share~

~Written by saleehat {s&s beauty}~
Chapter 14 · 0% Book details