← Book details Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Sanadin Gidan Aiki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"gudu sukeyi ba kakautawa kamar wanda sukaga dodo sosei suke falfala gudu _(nikwa nace seikace dole ko fadar allah🤔😏allah ya shirya)_ seida sukayi 3hours suna gudu tukunna suka fito titi wanda lokacin kusan karfe tara da mintina na dare daker suka samu mota tafitar dasu cikin kauyen"suna hawa suka fara haki zufa sei karyo musu takeyi duka sunfita haiyacinsu kamar mahaukata"gorar faro lubnah ta daga seida ta shanye ta tas ta ajiye tana sakin ajiyar zuciya akai aka! faiza kuwa kwance tayi kamar mataciya tana haki gawata uwar yunwa datake kwasarta"lubnah kuwa farin cikin datakeyi bai mistaltuwa ita kadei tasan irin iskanci dazata zuba inta auri *ASHMAN*

"sei gabanin asuba suka iso garin kano wanda ba karamar galabaita sukayi ba tunda motar haya suka hau"direct gidan lubnah suka nufa dan daidai dashi yana da kyau ba leifi zaman mutun daya"cika ke rijif sun zube kan gado suna nunfashi,seida suka dau 5minutes ahaka faiza ta mike ta bude firij din dakin ganin da kayan makwalashe ta jido harda su kaza,apple,exotic,da sauran kari kice ficewa tayi ta numama kazar a oven ta dawo tafara ci kamar mayunwaciya hannu baka hannu kwarya.....kallanta lubnah tayi ta kece da dariya tace acici babu a hause gidan miji batabbas tafada tana fadawa toilet itakwa faiza banza tayi da ita domin lokacin cikinta ne yanzu....

"seida suka nutsu kowa yadawo normal lokacin 6:00pm seide baccin dake kwasarsu"lubnah ce tayi tafi tayi shewa ahaiyeee nakusa zama Amaryar *ASHMAN* kawata kina ganin aikin boka bawasa ko?dariya faiza tayi tace"ke ai kisa aranki bukatarki tabiya zuwa anjima komai yazama daidai boka boka bawasa yarinya aikinsa yafi yankan wuka sauri ai boka *SAMMARABU* kat ne wallahi......hhhhh ai tuni na yarda dake kawata nasan boka bawasa daga ganin yanayinsa seide fa musha wahala kuma naga abin mamaki jifa daka ajiye kudi suka bace fitsarine kawai bansaki ba......dariya faixa tayi tace"farar kura kawai,nidai yanzu kudin wahalar danasha zaki biyani kona dawo daidai kafin kishiga daular mutumin naki,karki damu kawata bara mu kwanta muhuta inmun tashi zakiji dumus inkwa nashiga gidansa aikema seikin huta tafada tana dariya.

"bangaran ammi kuwa shirya *ASHMINAL* takeyi sosei gashi tadauko mai gyaran jiki tana ta gyarata"wanda yau akafara mata dilka da halawa(fans zanso kuga yanda lady din taku tazama dagayin nakwana daya tayi fes da'ita) baiwar allah tana bin umarnin ammi ne kawai anma duk bansan rantaba domin maganganunsa sunki barin brain dinta takuma rameiwa anma jikinta yayi kyau kuma takara haske"zaune take adakinta na part din ammi tazuba tagumi…Aysha ce tashigo takura mata ido taji dadi sosei ganin *ASHMINAL* cikin kyakyawar shiga dama yanda zata kasance ahaka harkarshen rayuwarta inji Aysha"ganin batasan tashigoba ta dafata tare dacewa kawata"firgigit ta dawo haiyacinta murmushi tayi wanda iya face yatsaya tace "aysha yaushe kikashigo?murmushi aysha tayi tace"yanzu nashigo domin naganki kinyimin nisa akusadani,murmushi tayi tace nima haka nayi kewarki sosei saikuma tafashe da kuka!aysha kukan takeyi domin tasan dalilin kukanta basai ta tambayeta ba tabbas rayuwar baiwar allah nan nabata tausayi tsayar danata kukan tayi tafara lalashinta tare dabata shawarwari masu anfani da kwantar mata da hankali.

"ayau dai din dad yawari wani bangare cikin gidansa agafara kerawa *ASHMAN* gida naban mamaki tundaga farkon gidan zakasan bakaramar dukiya za'azubaba"shikwa gogan ko ajikinsa face tunanin lubnah daya kwana yanayi yanajinta cikin ransa sosei ganin abin nakara yawwa yakirata yace suhadu gidan Ahmad.

"ihu ta zuba tare dataka rawa wanda seida tatashi faiza abarcin datakeyi"tsaki faiza tayi tace,kekuwa kalau kike?dalla qaleni *ASHMAN* ne yakirani yace muhadu gidan abokinsa yanzu dama kinga nayi wanka magani so biyu daya yarage yanzu shima zanyishi saina tafi ke wallahi nasha mamaki dan baitaba kiranaba sai yau da alama aikin boka yafara aiki......dariyafaiza tayi tace seiki harama kuwa muji yaxata kaya...yanzuma kuwa tafada toilet cikin zumudi dafarin ciki "bata dade soseiba tafito tafara shiryawa cikin shigarta data saba ta tsara make'up ba leifi tayi kyau sosei tasabi jaka cikin murna tayiwa faiza sallama tafice"tana fita faiza taja tsaki tace"zakici ubanki ne nima zanfara shiri akanki seinan gaba nawa zaifara aiki kudirina natafe gareki sokuwa kawai shiga daular dai alokacin zanfara cima burina akanki _(tofa fans gawata nanmafa🙆🏻🤔wani burine dake kwa faiza? seinan gaba maji komaine)_

"direct gidan Ahmad tanufa wanda tuni *ASHMAN* ya'isa "tanazuwa saida ta tsaya cikin kofata hangoshi sannan takoma dabaya ta zizara abin da boka yabata ta mayar jaka! cikin salamar jan hankali tashiga karaf kuwa suka hada ido dashi wanda yaji yakasa dauke idonsa"murmushin jin dadi lubnah ganin komai natafiya daidai "shigowa dakin takeyi shikwa sai kallanta yakeyi! zama tayi tare da kashe masa ido daya tace!my man barka da rana hope kana cikin koshin lpy dai takara cikin shagwaba maijan hankali.

"wani kayataccen murmushi yayi tare dajin wutar son lubnah nawani fuzgarshi yace"lafiya qlau my baby kina lpy nayi miss dinki shine nace

*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION🖊*
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌹🌹🌸🌸🌼🌼🌺🌺
🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀😭🙆🏻🙆🏻
*"SANADIN GIDAN AIKI"*
🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀😭🙆🏻🙆🏻
🌹🌹🌸🌸🌼🌼🌺🌺

~Written by saleehat {s&s beauty}~

*Assalamu alaykum ina maineman afuwarku na rashin jina 2days am busy anma yanzu komai yazama dai-dai*

_page 70-75_

.........shine nace bara mu hadu anan...wani sanyi dadine yasake rufeta jin abin yake fitowa abakinsa domin shine karo na farko dataji yace my baby dakuma nayi miss dinki jitakeyi kamar tatashi tafara tirkar rawa agabansa tsabar farin ciki...katse mata tunaninta yayi dacewa!koke bakiyi miss dina baneba?murmushi tasake saki bakinta har sauri yakeyi tace,nayi mana my man aikai nadabanne acikin zuciyata inaji dakai,dadi ne yasake rufesa yana ganin lubnah kamar wata star yanda yakejinta azuciyarsa.

"ajiyar zuciya yasaki tare dacewa baby natambayeki mana!ok my man inajinka fadi kanka tsaye....kina sona kuwa kuma zaki aureni?tsabar murna har dan ihu tayi tace!soseima wallahi ko yanzune ma adaura dan yanda nakesanka yawuce misali my man....murmushi yayi yace ok badamuwa gobe zankiraki awaya seikibani adrees din gidanku zanzo,zanwuce gida yanzu tunda naga farin cikina!murmushi tasakar masa tare da kashe masa ido daya tace to nima tafiya zanyi dan ina farin ciki yau sosei kalamanka sunsani nishadi....murmushi yayi sukafice atare suna firar love ko sallama baiyi da Ahmad dan shima yanacan yana sharholiyarsa.

"direct gida yanufo yanazuwa yawuce part din dad dinsa domin fada masa bukatarsa domin yanaji inbai auri lubnah ba zai iya shiga wani halin......da sallama yashiga...dafara'a dad ya amsa yanacewa my son sannunka dan albarka!murmushi yayi yakarasa kusa da dad dinsa yace!yawwa dad!murmushi dad yayi tare dacewa naga kamar kana da magana fadamin kaji.....yes inada ita kuma mai muhimmanci ce sosei!fadi kanka tsaye dan albarka kazo inda za ayanke maka damuwarka.....dad dama kamar yanda momy da warce tsohuwar suka zage sei andaura min warcen yarinyar to na amince don bayanda zanyi ne anma nima ina dawarce nakeso kuma zan aura sunanta lubnah dan nima nayi auran soyayya kamar kowana yaro mai gata!saida gaban dad ya fadi jin abinda dansa kefada kawar da damuwarsa yayi cikin fara'a yace,to Alhamdulillah haka akeso dama kaga bikin naka shingin kwana takwas imyaso sai ahada da warce kakeso din ko?sosei yaji dadi tare dayin na'am da hakan!dad ne yace,ita yarinyar a'ina take inyaso gobe sei muje neman auranta agama komai ko?eh dad yar nan garince anma kubari sei zuwa jibi inaje nagaya mata sei kuje!ok badamuwa allah yayi maka albarka yasa alkairi a auran…murmushi yayi yamike yanacewa ameen yayi gaba yana maijin farin ciki aransa.

"bangaran lubnah gida tawuce itama ta saki kida tana carkewa tsabar farin cikin da take ciki!faiza ce tace,waike kalau kike tundazu kike turkar rawa kamar sabon kamu?hmm aike bari kawata nasamu nasara ne dole na carke aikin boka na kyau domin kuwa *ASHMAN* natafin hannu na yanzu haka yace yana sona kuma da aure,murmushi faiza tayi tace a dole ki carke ai nace miki boka ba wasa inde kikaje wajansa bukatarki tabiya!kashe kidan tayi tazauna tana hakki sei murmushi takeyi,itama faiza zama tayi tana cewa,kaga Amarya bakya leifi.....murmushi tayi tace fadi ki kara fada da babbar murya nice din dai…bata'idarba taji wayarta na ruri acikin bag dinta da sauri ta dauko wayar ganin number dake kan wayar tasaki murmushi tace lallei aikin boka yayi kyau tayi picking call din cikin yanga da yauki dajan hankali tace!barka da yamma my man nayi miss dinka,murmushi yayi yace!yauwa babyna albishirinki?cikin yanga tace goro fari tas my man!murmushi yayi yace!nafadawa dad dina kuma ya amince jibima zasuzo anemamin auranki nan da kwana takwas zaki zama mallakina..........kirjinta ne yabada dammm jin yace nan da kwana takwas dakewa tayi tayi murmushi tace to my man nayi farin ciki seikazo goben mayi maganar yanzu ina dan aikine kaga seina sanarwa dasu momyna ko?yawwa baby byee......sauke wayar tayi tana dafe kirji tace nashiga uku ni lubnah…da sauri faiza tace lpy kawa?hmmm wai turowa zasuyi kuma nan da kwana 8 za ayibikin......mtwsss to maine daidai kenanma!ke faiza kinsani fa bani da iyaye gashi manyansa zai turo kuma kisan dole saina samu manyan mutane yanzu yaxanyi kwata-kwata banyi tunanin hakaba wlh!mtwss dalla ke kinfiya shashanci wlh hayar iyaye kawai zamuje muyi masu kudi wa'anda jikinsu zainuna tunda ke shegiya ce iyayenki sun mutu kikafaso bariki anma baki da fahimta!duk abin dazakice nidei kifada abin dake gabana yanzu ina zamuje musami hayarsu?ba'abubane mai wuya zuwa zakiyi kawai muje wani guri yanzu munazuwa bukatarmu tabiya inde kina da money!bani da damuwar kudi konawa ne zanbiya tasabi jaka tanacewa!zo muje yanzu......dan karamin gyale faiza tadauka tanacewa muje ficewa sukayi sukanufi unguwar rijiyar zaki zuwa wanjan wata mata mai hayar iyaye da sauran harkoki.
Chapter 11 · 0% Book details