← Book details Sahra Hot Love Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Sahra Hot Love Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama yayi kan kujera ya rike kansa da duka hanu biyu har lokacin gumi bai dai na yanko masa ba duk da ruwan daya zuba.

Tashi yayi ya leka bedroom ya hangeta kwance cikin bargo tana baccinta cikin kwanciyar hankali..ajiyan zuciya ya sauke yashiga dakin a hankali yaje yayi alwara a bayi yafito yadauki sallaya yakoma falon . rinka jera salloli yayi saidai akayi kiran assalatu yatafi masallaci.

Karfe tara da rabi yagama shirinsa cikin farin kananun kaya ya zauna falo yana jirin fitowanta, tunowa da mafarki jiya yayi yamike da sauri yafara zagaye dakin saboda har cikin kwakwalwarsa yakejin wani abu inya tuna.

A hankali tafito tana sanye cikin daguwar riga tayafa vail din rigan a kanta ta tsaya dan nesa dashi. ...baice mata komai ba yatashi yay gaba tabi bayanshi.

Washe gari da yamma tayi wanka tasa riga da skart yan kanti tana zaune falo taji karan bel,,, Bude kofar taje tayi taga baby ne ta sakar mata murmushi tace "shigo sister!." Murmushi baby ta maida mata tashigo ta zauna kan kujera,, zama sahra tayi gefenta tace "ni kadai i'nata zaune!

Yace karna fita!." Meyasa?." Baby ta tambayeta , bude hanuwanta biyu tayi tace "nima bansani ba!." Kafin takara magana aka turo kofar aka shigo, wara idonsa yayi yay murmushi yace "sweetheart kece!?" Murmushi baby tayi tace "eh fa yaya." Tafada tana tashi tsaye.

Rike hanunta sahra tayi tace "i'na zakije sister!?." Kallon aliyu tayi takara kallon sahra tace "uhm!

Zantafi mana , dama nazo duba lafiyanki..gakuma yayana yadawo!." Batajira cewar ta ba tazame hanunta tafita.

Dan satan kallonshi tayi taga i'ta yake kallo ta maida kanta kasa cikin sanyin murya tace "sannu da dawowa!." "Yawwa !." Yace yana zama kujeran dake kusa da nata ya dauki remote yay powering TV.

Tagefen ido ya kalleta yaga kanta na kasa tana wasa da yan yatsunta yadan hadiye wani abu yace "kin i'ya hada coffee!?." Juyawa tayi ta kallesa taga i'ta yake kallo ta gyada mishi kai tace "eh!." Hanyar kitchen ya nuna mata yace "akwai komai ciki, kihadomin yanzu!." Tashi tayi tabi hanyar shikuma yabita da kallo har saida tashige snn ya dauke idonsa daga hanyar.

Dafe kansa yayi da duka hanna yensa ya jijjiga kan sai kuma yatashi ya shiga bedroom.

Minti shabiyar tagama tajuye a tea flacks bayan tazuba mishi wanda zaisha, dauka tayi tadawo falo taga bai nan ta ajiye ta samu guri ta zauna.

Har bayan minti goma tana zaune bataji motsinsa ba sai tayi tunanin yafitane tatashi tashiga bedroom da niyar kwantawa.

A gaban mirror ta ganshi tsaye daure da towel tai saurin juyawa zata fita ya dakatar da i'ta..tsayawa tayi batare da tajuyaba kirjinta yanata sama da kasa saboda bugawan da zuciyarta keyi, Juyowa yayi yana kallonta lokaci daya matarkin jiya ya fado masa ya rinka ganinta kamar yanda ya ganta cikin mafarkin daure da karamin towel ga gashinta dayake har gadon baya jike ruwa yana disowa.

Takowa yafara yi inda take tsaye ya janyota ta baya tafado jikinshi ta fasa ihu don ba karamin tsarata tayi ba.

Daura bakinsa yayi kan nata amma bayyi socking ba yarinka kallon cikin idonta dasukayo waje tsabar tsoro.

Banko kofar falo sukaji anyi bashiri yasake yakoma baya.

Direct bedroom din ta nufa ta hankade kofar tashiga tana watsawa aliyu kallo daya gwalalo ido yana kallonta.

"Granny!?." Watsa minshi hanu biyar tayi ta dankwale sa tace "eh nice don ubanka shege gantalalle, wato daga kai har i'yayen naka kun raina min hankali baku dauke ni bakin komaiba da har shi wancan uban naka na borno zai maka aure arasa wanda zai sanar dani sai wnn yarinya yar albarka samhatu taje tasanar dani dayake i'ta tadaukeni a mutum." Dafe goshinsa yayi yace "OMG!

Haba hajja wai mekike shirin yine haka!?." Dan kwalonsa takarayi tazo gabanshi tazuba masa rankwashi tace "uwarka maryama nake shirin yi dan ubanka mahammadu...wato Aliyu kaima kazama dan iska ko?, da badawanda nake shiri a duk jikokina kamar kai, amma yanzu kaima tunda kabi sahun sauran zansa kafar wando daya dakai . murmushi yayi ya sosa gyeya yarike kafadun hajja yace " hada durling meyayi zafi haka kinsan ba'ajin kanmu..zomuje falo kifadamin duk laifi na inbaki hakuri." Yakarasa maganar yana kama hanunta sukafita ya kashema sahra ido daya.

Zaunar da hajja yayi shima ya zauna yace "haba amaryar duk kishine yasaki haka kinzo kinata hayaki kamar wuta." Tabe baki tayi tace "yo akwai wata shegiya dazaka aura ta hadamin hankaline , ainice farko nice karshe sauran duk bayine.

Kuma ma ba wnn ba ..don wulakanci da cin mutunci aliyu har kaine zakayi aure bansani.." Sai kuma ta fashe da kukanda ba hawaye tana cewa "wllh kunci mutunci na kun watsamin kasa a ido kun daukeni banza wanda batada mutunci."Gimtse dariyar datake neman kufce masa yayi ya rungumeta yana rarrashinta "haba hajja na, nima sokike nayi kukanne?..kinsan nima auren dole akayimin bansani ba kawai sai matar nagani!." Zamenewa tayi tafara salati tana tafa hanu tana cewa "ni nasan zaa rina. kai amma mutanen nan akwai marasa mutunci wllh, i'nba rashin mutunci ba shine zasu maka auren dole da wayonka da hankalin ka.

Kuma nasan da kanason auren dani zan fara sanin matar kafin wani." Langwabar dakai yayi kamar zayyi kuka yace "kingani ko hajja...ba laifina bane da ba'a fada mikiba." "To yanzu ita yarinyar tana i'na?." Tafada tana mikewa tsaye, shima mikewa yayi yarike hanunta yace "kibi a hankali hajja tana cikin daki ..amma narokeki karkimata masifa.

Hararata watsa masa tace" munafiki ,,kace basonta kakeba kuma kana cewa kar aimata masifa." Sosa kai yayi yace "hajja!

Nifa basonta nake ba kawai banaso ki tada mata hankali ne!." Tabe baki tayi tashige dakin taga sahra zaune bakin gado ta takure.

Washe baki tayi tace "kai tufarkAllah masha Allah ashe kishiyar tawa mai kyauce gaki yarinya mai hankali wllh dagani kinada tarbiya.

Kai alhmdllh jikana yayi dace duk da yace basonki yake ba amma ki kwanta da hankalin nizan shawo maki kansa sai yazo yanabin gindinki ." i'tadai gagara cewa komai tayi har hajja takarashi surutunta tatafi dacewa zata dinka zuwa tana duba lafiyar ta kuma kowaye yamata ba dai2 ba ta dauki wayar aliyu takirata zatai maganin koma waye.

Yana ganin fitowan hajja yamike tsaye hajja ta karaso ta buga masa duka a bayansa tace " wllh kayi asara, kadubi wnn tsaleliyar yarinya kabudi baki kace baka sonta saboda
rashin hankali ya sameka?..." Sassauta murya kasa2 tayi tace "kasan Allah kamaida hankalin ka kan wnn yarinya ka kula da i'ta don ina mai tabbatar maka idan karasa wnn yarinka to wllh kayi asaran zuwanka duniya baki daya.

Nidai nafada maka idan kadauka kanka idan baka dauka bama kaikasani dan uwarka kuma kaga tafiyata.

" tai ficewarta tana gyara zaman mayafinta . ajiyan zuciya ya sauke sai yanzu yatuno ashe towel ne jikinsa yace "hajja problem!." Kofar falon yaje yasawa ke don karta dawo yashiga bedroom don sa kaya.

Idan nasamu lokaci zaku jini da dare.

Love u all
View wattpad @habiebahlurv
Beenaf/beurv
[9/3, 8:51 PM] prince_s_square:
SAHRA
Hot love
22....

Rakub'e ya ganta bakin gado ta tallabi fuskanta da duka hannayen ta,,, murmushin da baiyi zatoba yaji ya kubce masa yawuce wardrobe dinsa yadauko wani farin yadi mai kyan gaske da farin hula da takalmi.

A gefents ya ajiye kayan yace "zoki tayani dressing!." Wara ido tayi ta kallesa ganin har lokacin towel ne jikinshi yasa ta dauke kanta tatashi tafita daga dakin duka.

Akaro na biyu yakara yin murmushi yafara shirinsa.

Sosea kayan yay mishi kyau ya dauran hulan saman kansa yasa takalmi yafito falo hanunshi rike da vail maidan girma,, Akan cinyanta ya ajiye mata yace "taso muje!."yay gaba.. bamusu tabi bayansa sukayi parking lot .

Dakatar da securities da suke shirin hada masa motoci yayi yace baya bukatar tafiya da kowa shikadai zai fita, nuna mata dayan site din yayi tazaga tashiga shima yashiga yama motar wuta suka fice daga gidan .

Babban kanti sukaje yasai mata hijab kusan kala ashirin dinkakku sabbin design masu stones, haka ya dinga yawo da i'ta har sai kusan magrib suka dawo haka kuma ba wanda yay ma wani magana cikin su . dadare a main house sukaje yin dinner kowa ya hadu suka fara cin abinci. samha ko inda suke bata kalla ba i'ta kadai tabarwa kanta shirin datake yi akansu.

Murmushi abba yayi daya tuno drama dasukayi da hajja dazu yace " Aliyu, kasan dazu hajja tazo?." Murmushi shima yayi yace "eh abba, tashiga gurina." "Alryt..kakula dai sosea.. don kasan halinta.

Har suka gama cin abincin ba wanda yakara magana naja ta tattare dishes din kowa yay nasa guri . mami kama hanun sahra tayi suka shiga falonta basu tsaya nan ba suka wuce bedroom ta zaunar ta bakin gado ta dauko wani abu a fridge cikin kofi yayi sanyi tamika mata" daughter ki shanye wnn!." Amsa tayi cikin ladabi tai bismilla tafara sha . ...sosea abun yay mata dadi gazaki don haka nan da nan ta shanye sa ta ijiye kofin.

Kallonta mami ta rinka yi tunda taji labarinta da abbey yafada abba takejin tausayinta sosea sonta na shiganta . shiru ba maicewa komai mami takatse shirun ta hanyar cewa "SAHRA sunanki yake ko?." Gyada kai tayi tace "eh..." Murmushi mami tayi tace "suna mai dadi.

Inaso ki kwantar da hankalinki ki daukeni kamar uwa ...kirinka cemin mami kamar yanda sauran suke fada kinji ko?." "To mami." Kad'a kai mami tayi tace "gud gal." Tashi tayi tabud'e wani karamin bag ta dauko wani roba tamika mata...hanu biyu ta amsa robar kafin mami tace "zaki rinka diban spoon daya kina hawada da madara kinasha ,,,kullum zaki rinka yin hakan.

Bude fridge tayi ta dauko wani dogon gora da wani abu ciki shima ta mika mata tace " kirinka shan wnn koda yaushe idan yakare ki fadamin karkiji kunya..kuma kirinka shan fruit sosea karkiyi wasa dashi kinji yata?" Gyada kai tayi tace "to mami...nagode." Turo kofar baby tayi tashigo tazauna hafara musu hira hakama mami don ita macece wayayya wanda ba ruwanta , hira suka rinka janta dashi harta dan saki jiki dasu sai karfe goma aliyu yazo suka tafi.
Chapter 10 · 0% Book details