Sashe 84
Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take motar malam yahya yayi suma sai suka taka tasu, abinda ya bawa raihana matukar tsoro, tayi saurin riko shi tana matsowa jikin sa sosai. Riko ta yayi ya sakata a jikinsa ta makalkale shi. Hannun ta ya kama ya saka cikin nasa ya damke yana mata dariya.
Idan kana neman kwararre a tuki ka samu malam yahya ka gama, dalilin da yasa Aryan ya zabi tafiyar tare dashi kenan dan yasan dama hakan zata faru. Kokarin bace ma su Adam din suke amma suma sun rike wuta gashi dama hanyar ba kowa sai yan motoci jefi jefi.
Daf da zasu shiga garin ne wajen wani karkacewa da titin yayi Aryan yace malam yahya ya dauke hanya, abinda ya jawo suka bace wa su Adam, wani irin ihu Adam yayi kamar zai damki kan sitiyarin ya buga jikin dashboard cikin bacin rai yace driver ya sauka daga titin ya gangara kasa. Gangarawa suka yi ya hau duddubawa dan basu ga alamun hanya a wajen ba, sai wannan dai titin guda daya tal da suke kai.
Tafiya suka soma yi a cikin garin har suka iso garshen dan titin da babu kwalta akansa, parking sukayi daga chan gefe sannan suka fito, a kaida machine ake hawa daga nan sai a shigar da kai garin amma sai Aryan yace su taka a kafa har su karasa dan baya so raihana ta hau bayan machine din,
“Idan da nisa nake ganin gwara mu hau Aryan. “
“Daga nan zuwa gidan malam yakubu akwai nisa?”
“Malam Yakubu wanne?”
“Wani farin bafulatini, ya zauna a cikin gari kafin ya tattaro ya dawo gida.”
“Oh na gane, gidan Baffan Kudu yake nufi, da yar tafiya gaskia musamman Yanzu da tsuka tayi yabanya hanyoyin sun zama masu wahala dan idan ba kwakwaran sanin wajen kayi ba sai ka bata.”
“Ai ban ma san wajen ba, zuwan mu na farko kenan.”
“Ina ganin mu hau kawai su kaimu Aryan.” Hydar yace
“Ok, baba kai sai ka dauketa.” Yace yana nuna wani dattijo a cikin masu baburan. Girgiza kai hydar yayi, ya d’ane bayan machine dinsa. Taimaka mata yayi ta hau ya karbi jakarta ya saka a tsakiyar machine din tsakanin ta da baban sannan yace su yi gaba sai wanda zai hau yabi bayan su maana tana gaba yana bayanta kenan. Shi dai hydar be ce komai ba, burin sa kawai su isa, jikinsa yayi masifar sanyi ga wani irin tsoro, tsoron kar su tarar da labari mara dadi ko ace ba nan bane, duk da Aryan ya tabbatar masa da mutumin shine ya dauki ammyn kuma shine Hajiya zeenat take zuwa gani a lokacin.
***Babban gida ne da ya amsa sunan babban gidA, baki daya kauyen babu gida me girma da tarin mutane irin sa ba. Malam Yakubu shine Yanzu a matsayin babba a ahalin gidan kuma shine ya tatttara yanuwansa dukka ya hade kansu bayan ya tattaro ya dawo a lokacin da ake harin rayuwar sa. A duk safiyar duniya bayan sun dawo daga dubo gonar su su kan zauna a kofar gidan a shinfida babbar tabarma su zauna su sha fara ko kunu da gaya ko koko duk dai abinda ya sauwaka kafin kananan ciki su wuce zuwa aikin gonar na ranar zuwa dagawar rana su sake tattaro wa su dawo gida suci abinci tare. Babban abinda mutane da yawa basu gane ba shine cin abinci tare yana matukar kawo shakuwa tsakanin yan uwa, miji da mata da sauran su. Babban Dalilin da yasa suke da matukar hadin kai kenan suna kuma girmama Malam Yakubu a matsayin sa na babba suna kuma mutunta duk wani abu da ya jibance shi. Karar shigowar mashinan ya sa suka maida hankali wajen ganin su waye suka zo? Ganin baki ne yasa suka ajiye abinda suke a gefe. Gaban malam Yakubu ne ya fadi, daidai lokacin da raihana take sauka daga machine din, bata da maraba da Ammy sam, nan take ya gane su waye da kuma abinda ya kawo su.
“Sani matsar da kayan nan gefe, sannun ku da hanya.”
“Yawwa.” Suka amsa a tare sannan suka zauna a gefen tabarmar bayan sauran duk sun tashi, gefe Raihana ta samu ta tsuguna ya cigaba da satar kallon ta ganin tsananin kamar tasu. Gaishe shi sukayi sannan aka gaisa da sauran yan uwan sai malam Yakubu yace duk su koma bakin aikin su, su basu waje. Ba musu kowa yayi nasa waje ya rage sai su kadai.
“Yan samari ban gane daga ina ba.”
“Daga kano muke.”
“Toh toh Masha Allah, me ke tafe daku.”
“Munzo akan maganar mahaifiyar mu ne dama.” Aryan yace
“Madallah, jini na karya ba, tun da kuka nufo mu nake kallon fuskar innar yara da wannan Baiwar Allar, kamar ta baci matuka. Ya gida ya hanya?”
“Alhamdulillah.”
“Anzo lafiya dai ko?”
“Alhmadulillah.”
“Toh Madallah, me kuke son sani game da mahaifiyar taku?” Ya tambaya
“Munzo ne muji idan tana raye, muna so mu ganta.”
“Menene sunan mahaifiyar taku?”
“Aisha Nasir.”
“Madallah, tana nan da ranta kuma a yanzu haka ma tana cikin gidan nan.” Ya nuna gidan nasu da hannu.
“Alhamdulillah! Suka hada baki wajen fada. Kallon rashin sani da fahimtar abinda yake wakana raihana take musu dan Itafa bata fuskanci komai ba.
“Zamu iya ganin ta ?”
“Sosai, me zai hana? Sai dai wani hanzari ba gudu ba…”
Duk sai suka tsaya suna kallon sa cikin tarradin abinda zai fada
“Mahaifiyar ku na raya kuma cikin koshin lafiya, sai dai ta gamu da wani iftilai a shekarun baya in da mota ta kade ta har ta kai kan ta yayi mugun buguwar da ta manta komai da kowa da ita karan kanta. Bata san wacece ita ba bare tasan komai akan rayuwar ta. Anyi mata magani a lokacin daidai gwargwado sai dai duk lokacin da mukayi mata maganar gida da dangin ta takan birkice mana tamkar ana saka guduma ko karfe ana buga mata kanta. Haka zatayi kwana da kwanaki tana ciwo na fitar hayyaci, da muka gano haka sai muka daina yi mata maganar, tun daga lokacin shikenan ta samu sauki, muka cigaba da rayuwar mu tamkar babu abinda ya faru.”
Shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su, sai raihana da ta saka kuka a durkushen da take.
“Yanzu menene abun yi?” Aryan yayi ta maza ya tambaya
“Sati biyu da suka wuce na samu wani babban malami munyi maganar, domin tabbas ba kalou ba, anan ne yake tabbatar min ko dai anyi mata sihirin da aka raba ta da gida da danginta ne aka kuma saka mata tsanar su da tsanar waiwayar gida tunda bata shiga yanayin sai idan an mata maganar, dole sai anyi mata maganin sihiri idan har akwai shi toh sai an cire shi sannan zata iya dawowa daidai ta iya waiwayar danginta.”
“Ya Allahu!”
“Minti daya bari na daga waya.”
Aryan yace yana tashi ya matsa gefe shi kuma malam yakubu Ya cigaba da yiwa su hydar bayani. Kamal ne ya kirashi sukayi magana sama-sama sannan ya kashe, sakon ne ya sake shigo masa ya duba sai yaga yace sun samu shigowar garin gasu a inda ma sukayi parking din motar su. Komawa yayi ya zauna kusa da hydar sannnan yace masa
“Sun shigo suna wajen motarmu.”
Kallon sa Hydar yayi da idanun sa da suka dan chanja kala, gida masa kai Aryan yayi sannan ya kalli malam yakubu
“Baba dan Allah toh ko zaa shiga da ita ciki? Idan yaso ko maganar ce kar ayi mata tunda nasan ba gane ta zatayi ba.”
“Abinda zan ce kenan, taso yan mata muje ciki, ya sunan ki.”
“Raihana.”
Jerawa sukayi tare da Aryan din har kofar gidan
“Please karki yi kuka, komai zai wuce zamu san yadda za’a yi,just be strong kinji? For me.”
Gida masa kai tayi, ya tsaya daga kofar ita kuma tabi bayan Baba Yakubu zuwa cikin gidan kirjinta na dukan uku uku.
_*_*RQ_**
58
*****A tsaye take a gefen dakin ta, ba kasafai ta fiye fitowa a irin wannan lokacin ba, ta kan zauna a daki a mafiya yawan lokutan musamman idan gidan ya zama babu yaran duk sun fice. Yau tunda ta tashi gabanta ke faduwa kamar wani babban al’amari yana shirin faruwa da ita. Randar dake gefen dakin nata ta bude ta zuba ruwa a buta ta zagaya bayi domin kama ruwa sannan ta dan wasa kafarta ta dauke hankalin ta kuma daga tunanin dake bijiro mata. Fitowar ta kenan tana tattakowa a hankali zuwa kofar dakin nata tana kallon yanayin yadda rana ta bude kwal kamar irin azahar din nan sosai. Sallama taji ta Malam Yakubu yana shigowa cikin gidan, lullubin dake kanta ta ja ta gyara zuwa saman kafadarta sannan ta amsa masa jin kulin ta Ya shigo kai tsaye, a bayansa muryar mace taji da batayi mata kama da ta yan matan gidan ba. Amsa sallamar tayi tana sakè matsawa daidai kofar dakin nata kamar zata shiga. Kanta ne yayi wani irin sarawa tayi azamar dafe shi tana jin jiri na neman kai ta kasa. Da sauri cikin daga murya tace
“Dan Allah karta karaso nan, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.”
“Wacece ?” Malam yakubu yace yana nazarin yanayin da ta shiga ganin raihanan
“Ban santa ba, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.” Ta sake maimaitawa tana yinkurin juyawa ta shige dakin nata. Kukan raihana ne ya karu, ta durkusa a bakin simintin kofar dakin tana sakè fashe wa da kukan.
“Tashi tashi, ba kuka zakiyi ba. Abinda nake son ku gani kenan dama, nasan za’a yi hakan, amma ba wai yin kanta bane ba, an riga an raba ta da kowa nata ne, an saka mata wani ciwo me Zafin gaske akan duk abinda ya danganci gida.”
“Zata warke?” Ta tambaye shi cikin muryar kuka
“Sosai ma, ai maganin ne yazo, in sha Allahu karshen abun kenan.”
“Mike muje shashen Asiya ki zauna kinji? Yaran gidan sun tafi makaranta ne amma daf suke da shigowa.”