Sashe 75
Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Good girl, ki cigaba kinji?"
"Tam."
"Me zan samu?" Yace yana mata wani shu'umin kallo, irin kallon da in dai yayi mata shi toh fa shikenan. Wasa da yan yatsun ta da suka sha gyara dazu ta hau yi ya kalli hannun da suka kasance dogaye zara zara ya rik'e su yana shafa fatar hannun da yaji tana wani irin sulbi da taushi. Gefen wuyan ta ya shafo a hankali ya yi baya da jikinsa suka fada saman gadon yana rik'e da ita. Batayi yunkurin tashi ba dan tasan ba zai taba bata dama ba, sannan a k'asan zuciyar ta tana son abinda yake wakana a tsakanin nasu sai dai ba zata nuna ba saboda kunya irin ta mace wadda shi namiji babu ruwansa da wani abu wai shi kunya musamman sababbin auren nan. Yau ya lura duk karantun da ya biya mata jiya ta dauka dan har wani bashi support take yi duk da tana cike da tsoro amma ganin ko kama hanyar abinda bata so din ma bayayi yasa ta saki jikinta sosai har ya samu damar yin yadda yaso da ita. Burin sa kenan dama, ta saki jiki dashi ko babu yawa domin yasan a duk ranar da me gaba daya ta faru akwai aiki babba.
Kamar jiya yau ma da asubah ya tafi sai dai basu hadu da Dr Farouk ba dan ko jiya yaji nauyi da kunyar sa sosai shiyasa ya fito yau da wuri akan sanda yake fitowa ya kuma chanja masallaci ba wanda Dr Farouk din yake zuwa ba. Daga nan ya wuce main house dinsu wanda daga chan ne zai karasa shirin sa kafin lokacin da za'a shiga court din yayi.
Sanda ya koma Adam baya gidan, be san ko be kwana a gidan ba ko kuma ya fita da wuri bane saboda shari'ar oho, shirin sa kawai yake a tsanake ba tare da ya saka kayan su na lauyoyi ba, dan ba shi da plan din halartar zaman kwata kwata. Bayan ya gama shiryawa ya dauki motar Daddyn wanda ta jima ba'a hau ta ba, ya fice daga gidan.
**RM**
Page 51
***Daga chan nesa da harabar wajen yayi parking din motar ya kwantar da kansa a saman sitiyarin kunnen sa dake makale da airpod yana sauraron duk abinda yake faruwa a kotun baki daya. Kusan mintuna arbain aka shafe tsakanin su Barr. Awais da lawyer me kareta, kafin Justice Fatima ta dan bukaci zuwa hutun minti goma sha biyar. A tsakanin minti goma sha biyar din nan ya sake tabbatar da abinda ya kuduri niyyar yi a yau din dan haka ne ma ya kara shiri sosai ya matso da motar kusa da kofar fitowa daga kotun ya samu k'asan bishiya yayi parking sannan ya maida kansa ya dora akan sitiyarin. Kasancewar tinted glass ne motar yasa ba ka ganin na ciki, sannan kuma pcap ce a kansa da ta sakko saman fuskarsa sosai. Abinda ya yi tunani shine ya faru bayan an dawo hutun da aka tafi. Murmushi yayi me ciwo sanda yaji justice Fatiman tana jaddada rashin tabbacin hujjojin da su barrister Awais din suka gabatar sannan a take ta bada belin Hajiya Zeenat din sannan tace za'a cigaba da sauraron shari'ar bisa wasu sharudda da ta gindaya. Be gama ji ba, ya zare airpod din ya wurga shi cikin dan wani box dan baya bukatar karasa jin komai, bayan abinda yaji din ya kuma san dama abinda zai faru kenan.. Duk da kwararan hujjoji da suka tabbatar da komai amma suka chanjaa komai suka nuna kamar ma shaidun ba gaskiya bane ba, anyi amfani da fasahar zamani wajen tabbatar dasu. Yanayin sa da yadda yake a nutsen sa ba zaka gane yadda yake cikin tsananin bacin rai ba. Wayar sa ce ta dan yi kara kadan alamun shigowar kira, a very low volume ya sakata sai vibration din saboda baya son wani distraction. Dagawa yayi muryar sa a chunkushe saboda tsabar yadda wani abu me girma yazo ya chunkushe masa a makoshin.
"Ok." Kawai yace bayan wanda yayi kiran ya gama maganar sa. Ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya bud'e dashboard din motar ya sakata sannan ya gyara zaman sa sosai. Yana zaune ya soma jin hayaniya alamun an fara fitowa daga cikin wajen. Tun zuwan sa dama yaga motar Adam yasan kuma yana ciki sai gashi sun fito tare da wani mutum suna magana suna dariya ya rakashi har gaban motar sa da driver sa yake zaune yana jiran sa. Adam din ne ya bud'e masa ya shiga ya zauna sannan ya rufe masa suka fice daga wajen. Ciki ya koma suka kara daukar lokaci sosai kafin su fito tare da Hajiya Zeenat din da su Barrister Awais da Adam din suna magana. Har wajen motar suka rakota Aryan yayi saurin cire lock din Adam ya bud'e mata bayan ta shiga ta zauna sannan ya rufe mata yace zai biyo bayan su a motar sa. Ok kawai tace masa dan a wani irin matukar gajiya take ga wani duhu da tayi duk da a prison din ma a VIP take amma still dai babu wani sauki. Ba karamin mahaukatan kudi suka fitar akan case din nan ba, wanda dama kowa ya sani a k'asar nan idan har kaga ya zauna ka dade a prison toh fa baka da gata ne ko galihu. Dan jinginar da kanta tayi a jikin kujerar Aryan na hangen ta, ta mirror ya kara kure mata AC motar wadda yasan tayi missing sosai hakan yasa jikinta kara saki sosai ya danna lock din motar ya take ta sosai ya dauki hanyar barin garin da ita baki daya.
Da farko Adam na biye da motar da Hajiya Zeenat din take ciki har aka zo wata danja ta saida su. Waya aka kirashi ya d'aga daga nan Aryan ya bace masa kwata-kwata. Be kawo komai ba, ya chanja hanya dan da gidan zai je amma kuma kiran wayar da ya samu ya sakashi kyale zuwa gidan ya koma baya.
Sai yamma likis sannan ya gama dasu ya dauko hanyar gidan, hold up ne ya rike shi sosai saboda yan siyasar da suka cika garin. Da k'yar ya samu ya yanke ya isa gidan bayan magriba sosai. Falon ya shiga kai tsaye da tunanin ganin ta sai dai yadda falon yake dim an kashe duk wani bulb me haske alamun babu kowa a gidan. Kunna hasken yayi ya nufi bedroom din Hajiya Zeenat din ya murd'a amma sai ya jishi a rufe. Mamaki ne ya kama shi, ya nufi hanyar kitchen yana kwalawa cook din gidan kira wadda yasan tana dadewa a part din nasu kafin ta wuce bq. Shiru bata amsa ba har ya karasa kitchen din ya tarar babu kowa alamun ta dade da kammala aikin ta, ta wuce bq. A kaida idan ace Hajiya Zeenat na nan ya kamata yaga mutane sun kusan cika gidan musamman kawayen ta amma ko a gate be ga alamar ta dawo gidan ba. Da sauri yayi hanyar waje ya fito compound din ya shiga kwalawa gate man din kira da karfi. Yana toilet yana uzurin sa ya jiyo kiran Adam din ya fito a guje dan ko karasa saka wando be yi ba, sai a wajen.
"Sannu da dawowa ranka ya dade." Yace gaba daya ya manta ma shine ya budewa Adam din ya shigo.
"Hajiya bata dawo bane ko ta fita?"
"Hajiya, wacce Hajiyar?"
"Ban sani ba." Ya daka masa tsawa
"Gaskiyar Allah Hajiya bata dawo gidan nan ba."
"Ina driver Daddy?"
"Yaje ganin gida,tun tafiyar Alhaji ya tafi gida shima yaga iyalin sa."
"Waye ya hau Babbar motar Daddyn a dazu?"
"Motar sa? Anya? Gaskiya dama bata gidan nan tun kwanaki aka fita da ita."
"Damn it!" Ya dunkule hannun sa kamar zai nashi gateman din sai kuma ya fasa, ya juya da sauri ya koma cikin gidan ya dauki key din motar sa da ya ajiye a saman kujerar ya sake fitowa yace ya bud'e masa gate ya sake ficewa daga gidan a haukace yana kokarin kiraye kiraye waya.
***Abby na zaune a falon sa bayan fitar Sadeeq, Raihana ta kira shi. Tun da aka kaita basu yi magana ba sai yau da ta kira shin yana sane kuma be kirata ba ita kuma nauyin sa ya hana ta kiran shi. Murmushi yayi ya d'aga wayar tata yana jin soyayyar yar tasa tilo a cikin ransa. A kunyace ta gaishe shi ya amsa zuciyar sa fes sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsaala. Girgiza kai tayi kamar tana gaban sa sannan tace babu, ya saka mata albarka sosai tayi masa godiya sukayi sallama. Dawowar su kenan daga wajen gyaran jiki tare da Khadija yau Ya Nabeela bata je ba tana da baki a gidan dangin Dr Farouk shiyasa ta hada su kawai da driver tace ya kaisu. Khadijan na falo ta shigo daki ta kara duba wayarta ko Aryan din ya kirata amma be kira ba, gashi ta gwada wayarsa a kashe tun rana. Komawa tayi falon ta zauna suka cigaba da hira da Khadija Amna na zaune a cinyar ta tana wasa da wayar tata har magriba tayi suka tashi don yin sallar magriba.
Ya Nabeela ce ta shigo dakin tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana istigfari. Zama tayi a gefen gadon ita kuma ta gyara zaman ta tana duban ta.
"Wai kuwa kunyi magana yau da Aryan?" Tace cike da kulawa dan rashin zuwan nasa ya fara damunta sosai
"Wayar sa a kashe take."
"Toh, yau ma? Dan sake gwadawa ko lafiya. Na kirashi dazu ma switch off. Bakin da nayi ne suka sa na sha'afa wallahi."