Sashe 36
Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abu ne ya sake taba ta, a tunanin ta Aryan yazo ya bata hakuri ne, yazo ya janye kalaman da ya faffada mata dazu, sannan ya kaskantar da kansa ya nemi afuwarta kuma yaji ta bakin ta, sai dai tsananin mamakin sa ya hanata cewa komai, ta dinga kokarin hadiye wani kukan bakin ciki da yake taso mata, tun da ta dawo ta kasa hada kayanta, ta kasa yin komai saboda yadda zuciyar ta, take a chunkushe. Akwai tarin bakin ciki a zarge ga da cin amana bayan kasan ba hakan ka aikata kai tsaye ba, sannan a hanaka kare kanka ballantana a samu yi maka uzuri, sannan ayi maka kora irin ta Wanda bashi da wani amfani. Duk wannan be isheshi ba, shine sai ya biyo ta har gida ya dora a in da ya tsaya? Lallai.
Gefen Hijab dinta ta kama ta rufe fuskar ta dashi kawai tayi hanyar barin dakin dan idan ta cigaba da zama kukan bakin cikin da take ta dannewa sai ya fito. Da wani irin sauri ya riko ta, Hijab dinta yayi niyyar rikewa Amma sai ya samu kansa da damko hannun ta, wanda yaji tamkar an jona masa shocking sabida yadda yaji. Tsayawa tayi chak ta kasa yin gaba, shi kuma ya kasa sakin hannun ta, saboda wani irin bugawa da kirjin sa ya shiga yi tamkar zai hudo. Kusan minti daya yana rike da hannun ta, yaki saki sai sheshekar kukan ce take tashi. Kokarin kwace hannun ta hau yi,sai a lokacin ya tuna yayi saurin cikata yana kallon nasa hannun.
"Subhanallah." Ya furta a a hankali ya dafe kansa.
"I'm sorry."
Ya samu kansa da furtawa sai dai kamar iya saman leban sa maganar ta tsaya dan ko motsawa batayi daga wajen da take tsaye ba, bare yayi tunanin taji abinda yace
"Kiyi hakuri."
Ya sake furtawa wannan karon da dan karfi. Kamar mashi haka taji maganar tasa ta shige ta, kukan da take ta soma ragewa a hankali tana jan ajiyar zuciya.
Zuciyar sa ce ta dinga kokarin ingiza shi, ya dinga jin tamkar yaje ya rungume ta, tayi kukan a kirjinsa akan zafin da yake ji duk lokacin da sautin kukan nata ya shiga zuciyar sa. Gwara ya tafi, kar yaje ya karawa kansa zunubi bayan na rik'e mata hannun da yayi.
Gefen ta ya rabo yazo daidai saitin ta, a hankali yace
"Na tafi." Sai ya bud'e kofar ya fice ya barta a tsaye a wajen cikin wani irin yanayi.
***Ya dade a kofar gidan be tada motar ba, har sai da bugun zuciyar sa ya daidaita, sannan ya kunna motar ya bar unguwar cike da wasu irin tunani da suka cika masa kwanyarsa har yake jin kamar zasu fito waje. Gida ya wuce cike da son dauke hankalin sa daga kan abinda ya faru ya maye su da tunanin halin da Daddy yake ciki duk kuwa da Kamal yace zai duba, ya kamata suyi abinda ya kamata dan a yanzu ya kara samun tabbacin akwai babban al'amarin da yake faruwa da Daddyn.
Hajiya Zeenat bata nan, tana chan gidan da suka kai Daddy ta samu wani nurse ta sakashi duba Daddyn dan tana so ya dan yi regaining energy dinsa saboda ta samu damar da zai karasa mata abinda ya fara. Suna zaune a falo yana cigaba da aikin da yake mata sai sako ya shigo wayar ta, budewa tayi ba tare da ta bada dukkan attention dinta ba, sai dai abinda yake kunshe a sakon ya sakata mikewa tsaye ta dafe kirjin ta
"Na shiga uku."
Tace tana kokarin yadda wayar, video dinta ne da akansa ta salwantar da rayuwar mutane biyu, ta tura daya gidan yari, video da ta tabbatar sai da ya bata bat a doran k'asar nan amma kuma ta yaya? Waye yake dashi da har zai turo mata shi a irin wannan lokacin, babu abinda yafi tsorata ta, irin abinda yake rubuce a karshen sakon, abinda ya kara saka ta a matukar rudani, waye? Waye wannan? Wayar ya dauka da ta yar ya bud'e sakon sannn yayi kokarin daukar number ya hau duba ta, sai dai babu wani bayani da ya samu akan number din duk da ya riga dama yasan ba lallai a samu komai akan sako irin wannan ba.
"Me nake dauke dashi? Me na samo a wajen Aryan kenan?" Tace a birkice. Gida ta nufa a matukar rikice, taje ta bud'e in da ta ajiye takardun nan ta fito da komai sannan ta sake fitowa ta dawo in da yake. Ta bashi ya karba ya hau dubawa sannan yasa cd din a cikin computer
"Babu komai a ciki Hajjaju. Empty disk ne."
"Na shiga uku."
"Sannan..." Sai ta durkusa a wajen
"Baki daya takardun nan fake ne, ba sune originals din ba, sannan takardun properties din Alhaji ma duk fake din ne."
"Shikenan, na gama, na gama." Ta zare dankwalin kanta ta dora hannu aka ta fara ihu, sai kuma ta tuno da wani abu, tayi wajen da daddy yake kwance da sauri ta kama jijjigashi
"Ashe tsawon lokacin da muka dauka yaudara ta kake? Cuta ta kake ban sani ba? Wallahi sai na ga bayanka, sai na karar da duk dangin ka, ba zan je kasa ni kadai ba, idan ma mutuwa ce sai dai mu mutu tare, bakin azzalumi."
Wayar ta, ta fara kashewa d sauri sannan ta saka shi ya kira gardawan nan suka zo suka dauke mata Daddy, suka saka shi a mota suka dau hanyar barin garin.
*RQ*
26
*TUNA BAYA*
Rayuwar gidan baki daya ta gama sauyawa, babu sauran mutuntawa da soyayya tsakani daddy da Mum dinsu Aryan, baki daya Zeenat ta chanja komai ita ce a gaba a komai duk abinda ya taso ita daddy yake sawa a gaba. A hankali ta dinga kokarin raba tsakanin sa da yaran sa ya zamto Adam ne kawai a gaban sa idan yana gidan suna tare tamkar shine kadai d’a a gidan. A gabansa tana kokarin jan Aryan a gaba duk abinda yayi amma sai ta kushe tana nuna tamkar bashi da wani wayo ko hankali kamar Adam hakan kuma ba karamin tasiri yake ba. Rabin rayuwar su sai ta zama tana gidan ammy dan duk wanda Daddy yake gida toh sai yayi ta musu fada yana kyarar su, Aryan da karacin shekaru be gane ba da farko Amma daga baya sai ya soma fuskanta. Dama miskili ne tun da aka haife shi, hakan sai ya kara taimakawa wajen sake janye kansa daga sabgar daddyn dan da yayi abu kadan sai ya hau shi da masifa wani lokacin har da bugu, hakan ya saka shi shima yake rayuwar sa a gidan ammy din musamman Yanzu da ta haifa musu kanwa mace sai ya zama na yana chan a ko yaushe yana dawainiya da ita shi da hydar har kwana a gidan yake yi. Rayuwar mummy gaba daya ta chanja ta lalace ga hawan jini da ya sako ta a gaba dan tunda Daddy yayi aure ta koma kamar mujiya a cikin gidan. Zeenat kamar zata bangaje ta duk sanda suka hadu ko kuma tayi ta mata habaici da bakar magana amma a gaban Daddy sai ta chanja ta juya zance tace Mummyn taki karbar ta ko hakura zasuyi? Saboda ita bata son damuwar mummyn, hakan da take fada ne yake sake tunzura shi Ya samu mummyn ya cimata mutunci yace tana da bakin kishi haka zatayi kuka ta gode Allah.
Watarana da azumi bayan Daddy da Abbyn sun tafi Umrah, da daddare gidan yayi shiru yaran sun yi bacci a gidan Ammy sai mummy ta sakko da nufin daukar abu a kasan. Motsi ta dinga ji a hankali yana fitowa daga dakin Zeenat din wanda yayi mata kama da na wani abu, da sanda ta karasa kofar dakin duk da babu ishasshen haske ita ma da wayar ta take haskawa ta karasa kofar dakin amma ga mamakin ta sai taga kofar a bude. Abinda ta gani yayi masifar daga mata hankali, zeenat ce haihuwar uwarta tare da wani abokin su Daddyn suna aikata alfasha sun manta basu rufe kofar ba. Kafar ta ce ta dauki rawa ta rasa me zatayi kawai sai ta danna wayarta ta hau daukar su video saboda ta samu hujjar da zata kawo karshen zaman zeenat din a cikin gidan wanda dama ta dade tana zargin ta amma bata taba da shaida amma Yanzu ta tabbatar idan daddy ya gani ba zai karyata ta ba. Dan short clip ta dauka wanda zai zama evidence sannan ta juya da nufin barin wajen sai ji tayi ta buge da kujera, tayi kara saboda zafi sai ta tuna da abinda tayi, sai tayi sauri ta juya ta bar wajen amma duk da haka sun riga sun ganta.
Dakin ta, ta koma tana haki cike da tsoro, dan tabbas zasu iya ganin ta, rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta shiga whatspp din Abby ta tura masa video din sannan ta goge na wayarta ta ajiye wayar ta zauna ta zabga tagumi, ta dade a haka kafin ta hakura ta kwanta a tsorace
Tana kwance cikin bacci sai taji kamar ana taba ta, ta ware idonta da sauri ganin mutum a saman gadon idon sa a rufe amma jikin sa babu ko kaya ya rankwafo kanta, yinkurin tashi tayi ya danne ta da karfi ya toshe mata baki, Zeenat da take tsaye a bayan su ta karasa daukar video din sannan Ya daga ta suka shiga jawota daga kan gadon suka buga ta da bango tayi wata irin kara sukayi saurin toshe bakin ta. Kokarin tashi take ta gudu amma sam sun hanata, suka dinga bugun ta ta kai da ko ina tun tana kuka har ta soma shidewa numfashin ta yana neman daukewa dan tuni jini ya fara zuba ta kanta da bakin ta da hancin ta, ganjn tana daf da daina motsi sai sukayi amfani da wukar suka dirza mata a wuyanta.