← Book details Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 108

Sashe 68

Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace yana kama zip din gaban rigar ya rik'e, ya dan ja kad'an ya dauko zuwa daidai saman tudun abubuwan nata yadda zai iya hangen su ta hakan ma. Da farko ta zata dukka zai sauke amma sai taga ya barshi kad'an yana murmushi.

****Gaba daya Raihana ta kasa gane kan Aryan, kamar zai maida ita cikin sa haka yake duk da be mata wani abu bayan runguma da dan peck ba amma kuma ko kallon idon sa bata iya yi saboda yadda suke ciki sosai suke haifar mata da wani irin yanayi. Tare sukayi sallar magriba da isha sannan yace mata tazo su koma saman saboda chan ne main bedroom dinsa, marairace masa tayi tace zata kwana ita anan din duk kuwa da tasan akwai tsoro sosai, be ko tsaya jin me take cewa ba ya kama hannun ta, suka fito ya haura saman da ita ya kaita har dakin nasa ya dawo ya dauki wayoyin su ya kashe hasken kasan ya haye saman. Tana zaune in da ya barta duk tsoro ya cikata, ya shigo ya ajiye komai akan bedside ya zauna a gefen ta ya kunna wayar sa dake a kashe saboda yana son kiran Kamal da Ya Nabeela. Kamal din ya fara kira be dauka ba lokacin ya tsaya masallaci suna magana da wani neighbor dinsa ya bar wayar ya gida. Sai ya kira Ya Nabeela wadda dama tun dazu take neman wayar sa a kashe ta daga sukayi maganar yana son kaya tace masa sai suje gobe yace toh sannan sukayi sallama.

*__*RQ__*

      Page 46

****

"Kina da alwala?" Yace yana rike hannun ta cikin nasa. Da kai ta amsa masa yace ta tashi suyi raka'a biyu su godewa Allah. A take wani novel da ta karanta ya fado mata da irin hakan ta faru abinda ya biyo baya. Kasa boye tsoron ta tayi har sai da ya dakata da kokarin shinfida sallar da yake ya zuba mata ido.

"Raihana?" Ya kira sunan ta yana dawowa wajen da take tsaye.

"Menene? Me yasa duk kike a tsorace?"

"Ba..ba komai." Tace ba wai dan babu koman ba.

"Please ki kwantar da hankalin ki, ki saki jikinki dan Allah."

"Tohm." Tace da sauri

"Me kike tunani?"

"Ni ba komai."

"Tom, koma menene kike tunani ki daina, ki nutsu sallah kawai zamuyi mu godewa Allah, sai ki bani labarin abinda ya faru bayan na dawo, shikenan sai muyi bacci."

"Tom."

Ta sake cewa tana jin tsoron na raguwa zuwa kaso tamanin duk kuwa da tasan zai iya fada mata kawai dan ta nutsu amma kuma sai taji ta dan samu nutsuwa ko da babu yawa, saboda muryar sa da yayi maganar bata nuna da wasa yake ba. Daga gefen damar sa ta tsaya sukayi raka'a biyu sannan yayi musu addu'a sosai har sai da ya fara bata mamakin yadda yake zubo addu'oi babu kakkautawa wanda ya haifar mata da wata irin nutsuwa a tattare da ita.
   Bayan sun gama ta ninke abun sallar ta ajiye su a wajen da taga yana ajiye su sannan ta tsaya daga tsaye ba tare da ta cire Hijab din ba bata kuma zauna ba. Be lura da ita ba dan yana idar wa toilet ya nufa yaje ya wanko bakin sa da mouth freshner me kamshin mint bayan yayi brush sannan ya watsa ma jikin sa ruwa dan ba karamin jin zafi ne dashi ba shiyasa idan zafi yazo baya gajiya da watsa ruwa, ba kuma ya taba kwanciya da riga a jikin sa haka zai kure AC ya baje haka ka'idar sa take tun da ma. Yanzun ma hakan ce ta faru bayan ya watsa ruwan ya fito daure da towel din ta yi saurin janye idon ta daga kallon sa dan ta lura ko kifi ba zai nuna masa son ruwa ba. Taune leben sa na sama yayi ya nufo ta gadan gadan kamar wanda zai cike jikin ta, sai kuma ya tsaya a daidai gabanta ya yarfa mata ruwan hannun sa a fuska.

"Matsoraciya, jeki yi wanka kizo mu kwanta."

"Nayi dazu ai."

"Yen yen,dirty girl, na dazu ai ya yi expire."

"Allah be ba, ni bana son nayi yanzu."

"Kina so nayi miki?" Ya kakantar da muryar sa ya fada kamar rada.

"A ah, zanyi da kaina." Tace da sauri tana kokarin barin wajen

"No bari dai nayi miki,karki sha wahala."

Yace yana riko da jikinsa, rikon da yasa ta jin wannan abun da take ji a duk sanda suka samu body contact.

"Wallahi tallahi zanyi da kaina,."

"Muje toh kiyi na gani, na tabbatar kin iya din."

"Na shiga uku, dan Allah kayi hakuri."

"Ba zan hakura ba, komai sai ace na hakura ni yanzu dai bazan hakura ba, muje kawai."

Ya rike ta gam ya nufi hanyar toilet din da ita, kwalla ce ta fara sakko mata daga idon ta, ga wani tsoro da ya mamaye ta, ya bud'e toilet din ya shigar da ita, ya tura kofar da kafarsa. Rufe idon ta kawai tayi kam ya juyo da ita tana facing dinsa sosai, ya kama zip din rigar tata ya shiga ja a hankali yana kallon fuskar ta da ta soma hawaye. Sai da ya kawo zip din kusan kasan kirjin ta sannan ya tsaya chak yana kallon halittar Allah,a cike suke taf gasu farare ta saka musu white bra me adon lace a jikin saman.

"Beautiful."

Ya furta cikin muryar sa da ta soma shigewa ciki sosai saboda wani yanayi da ya shiga lokaci daya. Hannu ta saka zata ja rigar sama yayi saurin rike hannun nata abunda ya ja rigar ta subce daga hannun sa tayi k'asa gaba daya. Kicin-kicin kwatar hannun ta, ya hanata ta hanyar rike hannayen nata duk biyun sannan yace.

"Idan baki nutsu ba zaki jawo na karya alkawarin da nayi,."

"Dan Allah kayi h..." Bata karasa ba yayi mata wata irin runguma da karfin gaske, jikinsu ya hadu waje daya a tare suka ji wani irin abu kamar electric shocking, bakin ta ya laluba ya hade shi da nasa waje daya ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Kusan minti biyar ya dauka a haka yana jin tamkar notikan kansa na kukkuncewa, ya damtse idon sa sanann ya hau girgiza kansa. A hankali ya saketa tayi saurin daukar rigar ta hau kare jikin ta da yake rawa kamar mazari. Wajen shower din ya nufa ya kunna ruwan sanyi ya sakar wa kansa hade da sauke ajiyar zuciya da karfi. Fita tayi da dan gudun ta, ta yi saurin zura rigar ta koma jikin gadon ta tsaya kafarta sai wani irin rawa take kamar mazari. Fitowa yayi daure da wani sabon towel din idanun sa da suka dan yi ja ya zuba mata jikinsa yayi masifar weak a hankali ya motsa bakin sa yace

"Je kiyi wankan."

Wuce shi tayi ta shiga toilet din, shi kuma ya fice daga dakin ya sauka k'asa gaba daya. Da sanda ta fito da ta ga baya nan tayi saurin daukar rigar da ta cire ta mayar ta haye gadon ta dukunkune waje daya ta rufe idon ta. Ya Dade a kasan be dawo ba ya zauna zaman duba wani abu a system dinsa yana yi yana shan black tea ga wani irin dum da kansa yayi masa, abinda ya hanashi shigowa dakin kenan har sai da ta gaji da kallon hanya ta hakura tayi bacci a sake da tunanin ba zai dawo ba watakila. Ta dade da baccin ma sannan ya hauro saman ya shigo dakin ya hange ta kwance ta rungume pillown sa a jikinta rigar ta tattare har wajen cinyar ta a waje tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ma baki daya ta manta a in da take. Kashe hasken dakin yayi ya dan haska da flashlight din wayar sa ya karaso ya hawo gadon ya kwanta a gefen ta yana kallon fuskarta. Ta rame sosai ba kamar sanda tana zuwa aiki ba, sai dai ta kara haske sosai sannan tana dauke da wannan innocent look din da ya fara gani a tattare da ita ranar da ta kawo request letter dinta, da yanayin yadda tayi a lokacin da yace Kamal yayi rejecting dinta kawai. Murmushi yayi ya kai hannu ya gyara mata gashin ta da ya dan tattashi ya sakko saman goshin ta sai ya ji kamar zufa take yi, karo karfin AC yayi dan dama itace ta rage ya kwanta rigingine yana kallon saman dakin domin sam babu bacci a idon sa har lokacin. Ya dade sosai a kwance ganin yadda ta ke ta juye-juye yayi tunanin ko sanyin dakin ne yayi mata yawa kuma, sai ya mike ya jawo standing fan ya jona a jikin socket ya kunna ta daga dan nesa da gadon ya rage AC zuwa low sannan ya kwanta yana jawo ta jikinsa gaba daya ya rungume ta tsam tsam.
Ita ta fara tashi da asubah ta ganta kwance jikinsa rigar jikin ta a bud'e zip din har k'asa. Da sauri ta jawo ta ta gyara ta tashi ta zauna a daidai lokacin ya bud'e idonsa ya ganta zaune a gefen sa, ya mata murmushi bayan yayi salati ta mayar masa tana sunkuyar da kanta a kunyace. Tashi yayi ya zauna ya jingina da pillow kusa da ita.

"An kira sallah?" Yace mata ta daga kai sai ya hau sakkowa a hankali daga gadon sannan ya fita daga dakin bayan ya kunna mata hasken dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta mike zuwa toilet ta yo alwala hade da brush sannan tazo ta shinfida sallaya ya shigo yana gyara hannun jallabiyar sa fara kansa sanye da tashi kafiya naci yayi shirin zuwa masjid sai kamshi yake, ka'idar sa ce in dai zai je masallaci sai ya fesa turare ko da kuwa ba wanka yayi ba, shiyasa kullum cikin kamshi yake hakan kuma da yake sunna ce me kyau domin ba zai je masallaci ya cutar da wani ba.

"Ok na zata komawa kikayi, naje masjid toh."
Chapter 68 · 0% Book details