← Book details Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 108

Sashe 22

Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasan zaka iya, dan ban haifi rago ba, sai dai nine kadai nasan lagon ta, ni kadai take tsoro a duk duniyar nan, dan haka a yanzu ne zata fara girbi!"

"Kira Salihun!"

Wayar ya ciro ya shiga kiran sa, ya saka wayar a handfree

"Hello!"

"Hello sir, barka da wannan lokacin."

"Barka dai Salihu, lokaci yayi na cikar aikin mu tare, sai ka sanar da ita."

"Ok an gama sir."

Yana kashe wayar ya yi dialing number Hajiya Zeenat, a lokacin tana zaune kusa da Daddy tana murza masa hannun sa a hankali yana shan mixed fruit. Kamar ba zata dauki wayar ba saboda bata san abinda zai katse ta, sai kuma ta dauka din dan tana da abubuwan da bata son missing. Ganin Salihu ne yake kira ya sakata saurin janye hannun ta daga na cikin Daddyn ya kalle ta.

"Lafiya?" Yace yana kokarin kallon wayar.

"Salihu ne." Tace tana daga wayar sannan ta sakata a handfree

"Hajiya akwai babbar matsala."

"Hanzarta fada min."

Kasa yayi da muryar sa sosai, kamar me rada sannan yace

"Yau Barrister MATAWALLE ya shaki iskar yanci!"

Cup din dake hannun Daddy ne yayi wata irin faduwa ya tarwatse a wajen, kafin ya mike tsaye cikin tashin hankali suka hada baki shi da Hajiya Zeenat din wajen cewa

"WHATTTT!!!!"

*RUMBUN QAYA

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥777

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥
*RQ*

      Page 17

Hafsat Rano

••••••

"Me kake fada min Salihu? Yaushe ya fito? Yaushe akayi haka duk ban sani ba."

Karbe wayar Daddy yayi

"Kana jina Salihu? Yi min bayani dalla-dallah ina sauraron ka."

"Har yanzu ban samu dalilin fitar sa ba, amma tabbas ya fito, na kuma yi kokarin ganin na binciki lamarin sai dai ban samu dama ba, idan kuma na cigaba da kokarin bincikawa Zan samu matsala da Oga, dan da alama umarni ne daga chan sama."

"Daga sama? Gwamna ko shugaban kasa?Wa ya damu dashi har haka da zai fitar dashi, waye wannan ya shammace mu? Waye shi? Hajiya Zeenat tace

"Ban sani ba Hajiya, bari na koma bakin aiki kar oga ya lura bana nan."

Jefar da wayar tayi bayan daddy ya miko mata. Ta cigaba da zagaye tana son figuring ainhin abinda yake faruwa.

Babu wanda ya iya zama a tsakanin su saboda rud'ewa, dukkansu sun yi matukar shiga tashin hankali da gigita, shi Daddy har ya kusan d'ara Hajiya Zeenat a shiga yanayin tsoro da firgici ya dinga kai wa da komowa yana kokarin kiraye kiraye waye sai dai duk in da ya kira sai ya samu same labarin da Salihu ya bashi. Shugaban prison din baki daya ya yanke shawarar kira dan shima yaron sa ne kuma be kamata ace an yi irin wannan abun ya kasa sanar masa ba sai dai wayar sa ma a kashe.
Daidai lokacin waani abu ya taso ya daki gefen kirjin Daddyn ya rike shi yana yin kasa rike da kirjin . Hajiya Zeenat da take ta waya ta lura da halin da Daddyn ya shiga amma tayi kamar bata gani ba dan ba tashi take ba dan haka ne ma ta cigaba da kokarin ganin ta samu information akan case din ko ya ya ne, domin tabbas an mata shigar sauri kuma ko waye yana da kusanci sosai da ita da har ya san duk moves din ta.
Wayar da ta kira ta karshe ce ta tabbatar mata da komai zai soma budewa ne a wannan gabar, duk wani kulli da suka haka rami suke binne zai zama an tono shi ne. Duk kokarin ta na ganin ta batar da duk wani shaida a doran ya tashi a banza.

"An chanja shugaban wajen ne."

Shine abinda wayar da tayi a karshe ya tabbatar mata.
Iska ta shak'a me zafin gaske ta fezar, ta rik'e kanta tana kokarin saka bayanin a mazaunin tunani. A dan takin da be wuce sati biyu ba, ta shiga prison din kuma ta samu tabbacin komai normal. Babu yadda za'a yi har a chanja shugaban wajen a wannan dan lokacin kuma ya aiwatar da wannan babban aikin da zai zama babban dalilin da zai tarwatse koman da ta gina. Dole wani yaci amanar ta

"Ina ba zai yiwu ba!" Ta furta da karfi

"Zeenatu. Zeenatu."

Daddy ya shiga kwala mata kira jin abun na neman fin karfin sa, hannun sa na dafe da kirjin sa, matsowa tayi ta tsaya daga kansa a tsaye tana masa wani mugun kallo

"Me kika bani nasha?" Yace da k'yar muryar sa na sarkewa ganin yadda take kallon sa

"Abinda ya dace da kai."

Tari ya soma yi da karfi, ta dauki wayarta tayi kira, minti kad'an wasu kartin maza suka shigo dauke da wata katuwar jaka, lokacin ganin Daddyn ya soma disashewa, takardun dukkan kadarorin sa suka fito dasu, ta karba ta ajiye a gaban Daddyn, daya daga ciki ya kama hannun sa, ya danna akan paper bayan ya dora shi akan stamp, sannan suka tilasta masa yayi signing wasu daga cikin takardun amma wasu ya kasa, zuwa lokacin abinda yake ji ya riga ya rinjaye shi har idanun sa sun rufe ruf. Kafarta tasa ta bugi kujerar cikin tsananin bacin rai. Ta riga ta shirya wannan plan din sai kuma labarin fitowar MATAWALLE ya rusa mata kusan rabin plan din, gashi bata samu ya gama saka hannu a dukka takardun ba, wanda suka kasance mallakin Aryan da Nabeela

"Ku haura min dashi dakin sama."

Tace tana kallon takardun ranta a bace. Ciccibar sa sukayi suka haura dashi zuwa dakin sa, suka kwantar dashi sannan suke rufe shi da blanket suka kashe wutar dakin suka fito. Sakowa sukayi ta basu umarni sannan suka fita. Sune sababbin masu kula da gidan daga yanzu, bata kuma yarda su bar kowa ya shigo gidan ba.
Dakin ta, ta shiga rike da takardun ta daga wajen da ta ajiye na Aryan din da ko bude su batayi ba ta hade su, su kadai zata rike yanzu a matsayin makami, sannan samun da tayi wa disk din nan shine a yanzu garkuwar ta, dan ta tabbata Matawalle bashi da wani copy dan haka ne ma tasan bashi da wani abu da zai rike hujja akan ta. Shiryawa tayi cikin rantsatsiyar shiga, ta bulbula designer perfumes masu matukar tsada da kamshi sannan ta yafa dan mayafi a gefen kafadarta ta fito, a daren nan zata yi maganin Matawalle dan ko da ace ya fito va zata taba bashi damar da zai iya tabuka komai ba. Na farko yanzu girma ya kamashi, haka bashi da wani matsayi a hukumance dan a gabanta aka kwace license dinsa tun a wanchan lokacin. Ba ma wannan ba, yar sa mafi soyuwa a gareshi tana a tafin hannun ta ne, dan haka kome ma yake shiryawa da wanda ya saka aka fitar dashi daidai take dasu.
Sai da ta shiga mota ta zauna sosai sannan ta kira shi a waya, dama yasan da plan din haduwar su a daren yau din amma kuma tana so kafin ta karaso ya nemo mata in da Matawalle yake da abinda yake yi a lokacin. Tamkar babu wani abu da ya faru, haka ta nuna dan a tunanin ta, tafi karfin dukkansu musamman da tasan ta kama abubuwa masu muhimmaci a garesu.

***Yau baki daya baya jin dadin jikin sa, tun da ya gama da wajen Dr Ma'aruf ya wuce gidan Ya Nabeela daga nan yayi kwanciyar sa dan ko ta kan wayar sa be bi ba shiyasa ma be ga kiran Kamal ba. Tun da akayi bikin Ya Nabeela bayan an dan kwana biyu ya tattaro ya dawo gidan dan kusan rabin rayuwar sa ta baya a tsakanin gidan ta da gidan su yayi ta, tun suna tsohon gida har suka dawo wannan da suke ciki mijinta yayi masa daki a gidan shikenan ya samu lasisin zama musamman duk sanda rashin lafiyar sa zata tashi dole tana kusa dashi tana kula dashi. Alwala ya shiga yayi a toilet din dakin da ya zama yanzu na baki idan sun zo sai kuma shi idan yaji bukatar zuwan. Lokacin la'asar ta dan gota yazo yayi sallar sannan ya shiga ciki. Suna zaune ita da Mijinta Dr Farouk lecturer ne a Federal University dake Dutse suna hira Aryan din ya shigo bayan yayi musu sallama daga kofar sun amsa.

"Ka tashi kenan."

Ya Nabeela tace tana kallon sa,

"Eh bansan ya akayi nayi bacci haka ba."

"Maganin ne."

"Barka da warhaka Yaya Farouk."

Hannu ya mika masa suka gaisa

"Barka dai Aryan, ashe kana ciki."

"Eh na shigo dazu."

"Toh ya jikin?"

"Alhamdulillah, ciwon kan ne dai yake dan takura min amma Alhamdulillah."

"Toh Allah ya kara sauki, ka kula sosai ka kuma dinga ragewa kanka wasu abubuwan ba komai ake cewa dole dole sai an yi ba."

"In sha Allah."

"Gwara dai ka gaya masa zai fi ji, kuma kayi masa maganar aure dan zaman a haka ba zai yiwu ba."

Ta wuce kitchen bayan ta gama maganar. Murmushi Dr Farouk yayi dan yasan yadda Aryan din yake idan aka dauko maganar aure

"Rabu da yayar nan taka bata son zaman lafiya."
Chapter 22 · 0% Book details