← Book details Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 108

Sashe 51

Rumbun Qaya Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ok, sai kinzo." Ya katse wayar ya shiga ciki ya nufi bangaren magunguna yana dubawa. Biyo shi ciki sukayi, biyu suka zauna a mota. Kamar masu siyan abu haka sukayi pretending suna dubawa har suka kawo saitin da yake suna kallon sa suna monitoring din sa. Sarai ya lura da yadda suke bibiyar sa a cikin wajen. Glass din da ya ciro a aljihun sa ya saka me dauke da camera da Kamal ya bashi yayi amfani wajen capturing abinda yake faruwa duk da ba komai ba amma yayi sa'ar samun hoton fuskar daya daga ciki.
   Cikin casual dress Habeeb suka shigo su ma wajen su uku, kunnen sa dake makale da Bluetooth ya taba yace

"Kana ina?"

"Wajen pharmacy, ina tunanin sun shigo ciki,

"Ok, ka shiga wani dan corridor haka muga"

"Okh." Yace ya juya ya hangi wani dogon corridor ya nufi wajen ya shiga, suna ganin ya shiga wajen suka rufa masa baya a daidai lokacin su Habeeb suma sun shigo. Su biyu suka yi wajen da Aryan din yake daya kuma ya tafi wajen receptionist din ya nemi office din manager ya nuna masa. Suna shiga lungun su Habeeb suka dirar musu, suka yi arresting dinsu a take.
  Tare wanda ya shiga wajen manager suka fito bayan yayi masa bayanin abinda ya kawo su wajen, godiya manager yayi musu suka fito har wajen da motar su take, suka tura su a ciki sannan Habeeb ya mikawa Aryan wata yar karamar na'ura ya shige motar.
  Tsaye kawai Aryan yayi cike da mamakin abinda ya faru just now, wato akwai mutanen da zasu iya goyan bayan duk zaluncin da hajiya Zeenat tayi kenan, har suyi kokarin taimaka mata da karfi da aljihun su. mutum daya ya rage DSS su kama shine SAN Mandawari shi kuma tun kama Hajiya Zeenat ya bi dare ya fice daga k'asar amma suna dakon dawowar sa wanda tabbas akwai saka hannun sa a harin nan da aka kaiwa Aryan din kuma shine mutumin da yake taimakawa Hajiya Zeenat din wanda suke da alaka me karfi tun da. Shine yayi shari'ar Abby kuma shine ya tabbatar da an tura shi prison.

***Kotun ta cika makil fiye da zaman farko, Adam na gaba dan da wuri ya iso kotun dan tun kafin a bud'e ma ya iso ya zauna a mota duk abin duniya yayi masa zafi. Tun da aka kama yaran nan da suka tura su tare Aryan yake cikin zulumi duk da kamasu ba bashi da direct alaka dashi sai na wanda suka tura shi, amma kuma idan har suka shiga hannu toh fa shima bincike zai iya zuwa ta kansa. Duk da ba lallai nasa yayi wani tasiri ba saboda su din manyan masu aikata laifi ne a k'asar kuma suna da daurin kafa shiyasa a sau da yawan lokuta Hajiya Zeenat din take having way din ta, wannan karon ne dai aka mamaye ta bayan ta gama sakankancewa itace da nasara domin ta samu duk wata hujja tasu a hannu not knowing that sunyi outsmarting dinta a matsayin su na yara matasa masu ji da zarra.
  Shigowar judge din ya saka wurin ya dau shiru daidai lokacin aka shigo da Hajiya zeenat ta saka gefen mayafin ta, ta rufe fiye da rabin fuskar ta. Aryan na zaune tsakankanin manyan lawyers tare da Barrister Awais da yake leading din su.
  Shi ya fara mikewa ya gabatar da kansa ga kotu sannan lawyer da yake kare Hajiya Zeenat din ya mike shima yayi introducing kansa sannan su Aryan da Barrister Hakim da Barrister Fatima suma suka gabatar da kansu. Cikin shari'ar aka shiga kai tsaye ba tare da bata lokaci ba, Judge din ta sake karanto tarin laifukan da ake tuhumar Hajiya Zeenat din dasu wanda suka hada da zargin salwantar da rayuwar Hajiya Khadija Mukaddas, Hajiya Aysha Matawalle, satar yaro jinjiri Ahmad tun yana zanin goyo sannan tayi yinkurin kashe mijinta Alhaji Mukaddas wanda yake kwance a asibiti yanzu haka da kuma sauran laifukan. Barrister Awais ne ya sake mikewa a isa gaban wajen da take tsaye saboda yana da bukatar ta amsa masa wasu tambayoyi.

"Sannu Hajiya Zeenatu, akwai wasu yan tambayoyi ba masu yawa ba, da nake so ki amsa min."

Idon ta akan Aryan da yake zaune daidai saitin ta yana facing dinta dan shi kadai kawai take gani a wajen.

"Kina jina? Da farko dai kotu zata so sanin alakar ki da wadannan mutanen, Aisha da kuma Hajiya Khadija."

"Kawaye na ne da muke tare tun makaranta."

"Wani abu na rashin jituwa ya taba faruwa tsakaninku? Ko sun yi miki wani abu da ya bata miki rai har kika ji bari ki salwantar da rayuwar su?"

"Objection My lord." Barrister Sule yace yana mikewa

"Me kamata Barrister Awais ya dinga jinginawa mata kalmar kisa kai tsaye ba, tunda har yanzu zargi ne ba'a tabbatar da gaskiyar ba."

"Barrister Awais ya kiyaye."

"Ok, my lord."

Komawa Barrister Sule yayi ya zauna ya yi folding hannun sa.

"Muna son sanin me ya faru ranar bakwai ga watan October, da daddare wajen asubah, a lokacin da aka samu gawar Hajiya Khadija a kwance cikin jini."

"Bansan komai akai ba, kamar yadda aka samu gawar ta haka nima na ganta,."

"Hmm."

"Abinda ya faru a ranar 7 ga watan October da misalin karfe biyar na asubah an samu gawar Hajiya Khadija a kwance a cikin jini, wanda barrister nasir Matawalle ya samu gawar tata bayan ta tura masa wani sako da misalin karfe biyun dare, in da be tashi samun sakon ba sai da asubah saboda ko a lokacin da ta tura masa sakon dare yayi, ga abinda sakon ya kunsa ya mai girma me shari'a."

  Ya mikawa daya daga cikin na zaune gaban wajen sannan shi kuma ya mika mata, ta karba ta gani sannan ta ajiye a gefe

"Kotu na sauraran ka Barrister Awais."

"Bayan Hajiya Khadija ta kama Hajiya Zeenat da abokin aikin nata sai tayi yinkurin daukar hoto a lokacin ne suka lura da ita, sannan suka biyo ta har cikin daki suka kashe ta."

"Objection My lord, ya za'a yi barrister Awais ya dinga jingina mata laifin kisa kai tsaye? Hakan yayi muni sosai, ina rokon da ya janye kalaman sa ya kuma tausasa lafuzan sa."

"Ko kana da shaidar abinda ka fada barrister?" Tace tana kallon sa

"Kwarai da gaske, ina da shaidu guda biyu, na farko shine d'an marigayiya Hajiya Khadija wanda duk da karancin shekarun sa a lokacin yana iya tuna abinda ya faru akansa, na biyu shine shaidar da aka samu a cikin CCTV camera din dake hanyar shiga dakin marigayiyar wanda ya dauki hoton hajiya Zeenat da abokin harkar ta wanda bamu iya ganin fuskar sa ba a lokacin da suke shiga cikin dakin."

"Kotu tana bukatar ganin shaidun a gabanta."

Aryan ne ya mike ya isa gaban wajen ya sake yin gaisuwa sannan ya gabatar da kansa a matsayin shaida duk kuwa da ba lallai shaidar tasa tayi tasiri ba sosai duba da karancin shekarun da yake dashi a lokacin da kuma kasancewar sa cikin lawyers masu kara. Yana maganar kirjin sa yana harbawa sosai saboda yadda a duk lokacin da ya tuna memory din yake shiga matukar tashin hankali, da kyar ya karasa maganar ya koma wajen zaman sa ya zauna dafe da kirjin sa. Ruwa Barrister Hakim ya bashi Yasha sannan ya dan samu daidatuwa. Shiru ne na dan sakannni ya bayan komawa wajen zaman Aryan din, sannan aka cigaba da sauraron karar. Sosai barrister Awais yayi kokari wajen bada hujjoji kwarara kafin ya gangaro laifi na biyu wanda yake akan batan ahmad ne. Hankalin Aryan gaba daya yana ga kofar yana lokaci zuwa lokaci yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, fatan sa shine Allah yasa su karaso a daidai lokacin da ake bukatar su.
  Ta kofar dake chan gefe Barrister Nasir matawalle suka shigo tare da Lamido sun samu delay na flight dinsu ne abinda yasa suka makara. Waje suka samu suka zauna a nutse aka cigaba da shariar.

   ***Tun da suka tashi Daddy yake faman rokon su akan su barshi yaje kotun amma suka ki, Har nurse din da ke duty yayi ma magana da ta shigo amma tace yayi hakuri Dr yazo. Hankalin sa baki daya yana wajen yana son sanin yadda zata kasance sannan yana so yaji komai game da hajiya zeenat duk da ya gano Wasu abubuwa masu yawa game da ita wanda sai lately ya gano dalilin da yasa shi shiga ya tsaya tsayin daka ya samu aka fitar da Abby, shine ya bada evidence din da ya wanke Abbyn sannan ya tsaya tsayin daka har aka fitar dashi da taimakon Kamal. Duk da ya san babu wani abu da zai fada masa ya yafe masa laifukan sa gare shi, amma duk da haka yana ganin yayi abun da ya dace, ko da ba zai yafe masa ba. Baba Rabi'u ne yazo gaban sa ya tsaya sannan yace

"Nayi magana da Dr sun yi discharging dinka, yanzu sai muje chan kotun saboda nasan hankalin ka Yana wajen."
Chapter 51 · 0% Book details