← Book details Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 12

Sashe 8

Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk wannan kyawon naki amman kina zaryar neman admission ai yanzun ba marks ake dubawa ba iyawarka da kyawon mutum ne yake bashi damar cigaba da karatu ki bani hadin kai ki gani kowanne irin karatu kike so a makarantar nan zan nema miki shi cikin sauki "

Ni kam murna na ringayi don har a lokacin ban fahimci manufar ta ba, ganin yadda nake murna sai ta zubamin ido tana kallona ta sani na juya taci gaba da kallona.

.
Duk sai jikina yayi Santiago ina mamakin me yasa take kallona Alhalin ita mace ce y'ar uwata da na fito sai wannan dan uwan namu yace min,

"Safiya kar ki kara zuwa makarantar nan kiyi zamanki a gida zan nemomiki admission saboda bana son ki kuma haduwa da matar nan"

Mamaki ne ya kamani nace,

"Saboda me baka son na kuma haduwa da ita ?"

Ya numfasa sannan yace,

"Daman nasan baki fahimceta ba don kuwan matar nan da kika gani y'ar lesbians ce kuma idan tasa daliba a gaba bata gyaleta sai ta cika burinta ta lalata mata rayuwa kuma bana fatan hakan ya kasance akanki"

Nan jikina ya fara rawa na tuno tambarin da akayi min na y'ar iska atake na shiga addu'ar Allah ya tseratar da ni nace masa,

"Insha Allahu bazan kuma dawowa ba "

Shi yayi ta min wahala ni kuma ina gida kuma yayan nawa bai sani ba na samu ko ban samu ba tun ranar da ya turani bai kuma yi min zancenba.

Dakyar dan uwan nan namu wato Nazir ya sama min admission, sannan mukayi screening anan ne fa suka kafe cewar waec dina printing ne dole sai naje kaduna na dauko original din kuma gashi bani da ko ficika .

Naje gida na samu yayanmu na fada masa nan ya rufeni da fada son me zan tawo karatu na bar documents dina a gida nace masa,

"Ai ni bansan suna da amfani ba secondary school na gama bansan yadda abin yake ba ballantana nasan abinda ake bukata a jami'a ba"

A take yace shi bashida kudin da zai bani na hau mota hakan yasa na kira mamana na fada mata ina son zuwa gida don naje na samu papers dina tace,

"Zansa kanin ki ya amso miki su dukka kafin kizo" nace,

"Toh goggo kudin mota fa don ni bani da kudi a hannuna kuma bana son na takurawa yaya"

Sorry fans😴

.
Daga Alkalumman:

Maman nurul huda 👄
And
Maman ihsan😍

Pls comments and ahare
[7/5, 4:14 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 23/24

Sai tace min

"Kanwata tana nan kusanku zanyi mata magana sai ta baki dari biyar "

Na amsa mata da Toh ana gobe zantafi gashi wato weekend sai na samu murja nace mata

"Aunty murja gobe zanje kaduna"

Nan ta fara balbaleni da masifa tana cewa,

"Kenan tun yanzun zaki fara zaryar yawo zuwa kaduna ko?"

Nan nayi mata bayanin muhimmancin zuwana sai ta tabe baki tace,

"Allah raka taki gona sai kin dawo"

Naje gurin kanwar mamana nayi mata bayani tayi mamaki cewar ina kaduna nan tayimin addu'ar Allah yasa na kammala a sa'a ta bani kudin motar dari biyar.

Na hau mota muka isa kaduna aka ajiyeni a NDA gashi bani da kudin motar da zan karasa kuma da nisa zuwa unguwarmu na dabi sayyada har gida na amso result dina kuma ban fadi cewar yaya bai nemomin admission ba har na koma zaria.

Muka fara karatu gadan gadan a duk ranar da na fita makaranta sai naji sunana ya harba har gida cewar naje yawo daga makaranta.

Ina shiga zata fara balbaleni da masifa wai yawo nake zuwa gashi ko kudin mota basa bani ballantana kudin abinci in wuni da yunwa in dawo da yunwa in naci sa'a ina da naira ashirin shine zanci garin kwaki nan fa ulcer ta sako ni gaba har saida na kwanta a school ne nake zuwa ake bani magunguna,

Abinda ban saniba ina tafiya makaranta Aunty iklima take zuwa ta fara tsarawa murja tana cemata bamuda lecture ranar yawona kawai nake zuwa daman tunda kuka tawo da ita nasan ta samu lasisin gantali kafin na dawo ta tafi.

Wata rana dai Allah ya hada mu ina shirin shiga gida sai gata tana sauri zata fito na kalleta nace,

"Aunty iklima kece yau a gidanmu?"

Nan ta shiga kame kame tana cewa,

"Yau na gama lecture da wuri ne shi yasa na zo nace bari na gaida Aunty murja" nace,

"Amman ai mun hadu a masallaci shine baki fada min ba sai mu tawo tare?" sai tace,

"No ai lokacin banyi tunanin zuwa ba sai daga baya don lokacin muna da lecture teacher din ne bai zo ba"

Nan dai ta gama kame kamenta mukayi sallama.

Ina shiga na iske Aunty murja ta murtuke fuska ta hade rai na gaidata na wuce kitchen tsaye nayi da mamaki ganin dan abincin da aka ajiye min wanda inda za'a bawa yaro dan shekara uku tsaf zai cinye ya tashi watakil ma yace bai koshi ba amman wai shine abinci na.

Haka nan naci dan abincin nan kuma da dare ba'a tashi abinci ba sai tara tace na dafa indomie.

Haka nan dai nake tare da su da dadi ba dadi har muka tafi wani dogon yajin aiki tsayin six months nayi nayi su barni naje gida suka hana ni dole na zauna ina musu bauta gashi kullum diyarta sai tayi fitsarin kwance nike yi mata wanka na wanke kayan na shiryata ke duk wata hidimar su nice daga wanki har guga da shara da mopping duk ni kadai yadda kikasan jaka amman dole nake jurewa saboda mamana ta riga tayimin fada.

Idan nayi musu maganar xuwa kaduna sai ayi ta min fada wai ban isa naje kaduna ba ko gidan kanwar mamana sun hana ni zuwa balle naje na huta dole zan zauna tare dasu ina musu bauta.

Ni zanyi girki amman dana zubo abincin zanci zata fara yada min magana,

"Uhm su safiya an cika ci babu aiki saina cika ciki"

Ta ringa complain kenan wata rana har kuka nakeyi wani lokacin kuma nayi murmushi don gani nakeyi da kanta take don kuwa ita ke cin abinci tayi chatting tana gamawa ta hau barci.

Ashe ciki ke gareta ni bansani ba don kuwan ita irin matannan ce mai kiba kuma bata laulayi shi yasa ban sani ba don inba ita ta fada maka ba bazaka ganeba kuma ya girma.

Cikin lokaci kankani wahala tasa na fige na rame inkikaganni sai kice nice y'ar aikin gidan nan ba kanwar miji ba.

Ga y'an uwanta suna yawan zuwa daga katsina kuma ni ke hidimarsu su baje suyi ta barci ni kuma inata aikin gida tare da dora musu ruwan wanka.

Kadan kadan wani kanin ta da ya dawo daga maleysia ya ringa jana ajiki tun bana sakewa har na saba dashi muyi ta hira lokacin nan inya tambayeni me na karanta sai nace masa English geography.

Nan fa ya samin suna *English geography* na nuna mata ina son inje islamiyya da kyar suka sani islamiyya na dora daga inda na tsaya a gida da yake daman mun kusan yin sauka lokacin saukar makarantar mu ya kai na ce musu zanje kaduna zamuyi sauka tunda nima na hade karatun nawa anan.

"Aw wai daman ke kinsan Allah har da sauka amman kike da shegen son maza kina aikata alfasha"

Nan dai tayi min tas da kyar suka barni naje kaduna mukayi bikin saukarmu na dawo gidan bauta.

Sati biyu da yin saukarmu Abubakar ya kirani cewar yana zaria inyi kokari mu hadu kafin ya wuce kaduna don tare yake da y'an uwanshi, na tambayeshi inda yake yacemin,

"Ina kofar doka gurin gidan mai"
Nayi mamaki nace masa "Ai kaf kofar doka babu gidan mai, sai dai ko makarantar Alhudahuda nan ne akwai gidan mai ko gidan yari kake nufi"

Yace sam shi gidan mai na kofar doka yake na amsa masa da toh ina zuwa, naje gurin Aunty murja na shirga mata karya nace,

"Aunty anyi wa Jamilar nan ta unguwarmu rasuwa kakarta ta rasu shine suka zo ina son inje inyi mata gaisuwa" tace,

'' Ayya wannan matar da take aikomana kosai ko?" na amsa mata da Eh tace,

"Toh ga naira dari kije kiyi mata gaisuwa motata babu mai da nima naje don matar tana da kirki"

Na amsa nayi mata godiya na shirya na fita na kira shi nace masa ganinan zuwa

Cikin sa'a na hadu da wani dan uwanmu ya rage min hanya zuwa kofar doka muka zagaye kaf kofar doka banga ko kyallin abubakar ba nace masa ya ajiyeni a round about na kofar doka tunda kaduna zasuje dole zasu bi ta nan.

Bayan na sauka na kirashi na fada masa inda nake wai sai ya shiga yimin fada me yasa naje round about sai dai in dawo baya naje dai dai kofar dokan.

"Haba Abubakar yanzun ya zanyi na tsallaka wannan makeken titin kai fa hanyar ku ce ka biyo mu gaisa sai na wuce gida"

Nan ya kafe sai dai na tsallaka na tarar dasu haka na hakura na tsalla titunan nan naje na samesu ya wani hade rai kamar wanda akayiwa sakon mutuwa muka gaisa da y'an uwanshi cikin mutunci sukayita yabona suna cewa ya dace ya samu kyakkyawa,

Shi ko kokim bai ce ba har suka shiga mota sannan ya yi tsaye jikin motar na kalleshi nace,

"Abubakar lafiya naga ranka a bace?"
Ya wani kauda kai yace,
"Ba komai yanzun ina zaki ?"nace

"Ni daga nan gida zanje "

Daga cikin mota 'dan uwanshi yace,

"Tunda gida zakije ki shigo mu rage miki hanya" nace,

"Ku da zakuje kaduna sai in maidaku baya kuma kuyi tafiyarku zan hau mashin"

Nan dai suka kafe akan lallai sai na hau sun kaini sai na hau suka kaini har unguwar kaya na sauko shima ya sauka muka tsaya a jikin motar ya fara fada,
Chapter 8 · 0% Book details