← Book details Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzun kishiyoyin mamana sun kara matsa mata da gangan zasu kirkiri tafiya garuruwansu su kime mata aikin gida ga kuma tana zuwa gurin aiki hakan yasa ta fara sarara min tana dan sakewa dani wani lokacin har muyi hira.

A kwai wata sallah babba dayake baban mu ita yake dorawa akan aikin naman sallah haka zasu tsame hannun su su barta da aiki kuma in anzo rabon nama a shiga bala'i ana cewa duk ta handame naman daga ita sai y'ay'ata babanmu ne yake bata hakuri.

Wata rana muna hira take cemin,

"Safiya inda zakiyiwa kanki fada ki shiryu irin haka da yafiye miki"

Nayi murmushin takaici nace,

"Goggona" ta amsa da "Na'am"nace,

"Wallahi tallahi ni ba y'ar iska bace ko hannu na ban taba yarda wani namiji ya taba ba, amman ana hadani dake alhalin ni ko yawo bana zuwa"

"Munafuka ni zaki yiwa dadin baki ne zaki lallameni ko?"

Ta fada a fusace nace,

"Shikenan goggo Ina addu'ar Allah ya bayyana gaskiya kuma ko wane ne munafikin sai Allah ya sakamin"

"Safiya fito fili kice min Allah ya isa tunda ni sa'ar ki ce"

Ta fada a fusace tare da rufeni da duka naci kuka na nagodewa Allah.

Nawawoo this story make me cry sometime ooo, the star of this story i say sorry to you 😢 Allah is with you

Alkalumman:
[6/29, 7:40 AM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 13/14

Wani dare da zan kirashi daren bakin ciki wanda bazan taba mantawa da shi ba a rayuwata yayana Musa wanda muke uba daya ni da shi, ya shigo dakina ya tashe ni a barci na mike ina kallonshi da mamaki duk da banji a raina cewar nemana yazo yi ba tunda a ganina yayana ne dole ko yayane akwai so yayya da tausayina a ranshi a matsayina na kanwarshi yace,

" Safiya kinsan ko me ya kawo ni ? "

Na girgiza kai har lokacin ina ta tunanin me ya kawo shi nace,

"A'a yaya Musa sai ka fada"

Yayi wani murmushin gefen baki yace,

"Matso kusa in tabaki safiya"
Jikina ne ya dau rawa muryata tana rawa nace,

"Yaya Musa ka tabani fa kace, ban gan ka tabani ba ? "
Yace a dan tsawa ce

"Eh ki zo nace na taba kiiiii"

Nan fa muka shiga gardama ni naki bashi hadin kai shi kuma ya nace sai na yarda ana cikin haka sai ga Mamana ta fito yana ganin ta ya chanza akalar zance yace,

"Wai safiya ba cewa nayi ki saka min tuwo inci ba ? Kika tsaya kina kallo na"

Jikina har lokacin yana rawa nayi saurin dauko kwano ina cewa,

"Kayi hakuri don Allah yanzun zan zuba maka"

Na zuba mishi tuwon na mika masa ya amsa sai mamanmu tace,

"Wai daman tuwo yace kisa masa kika ki kika tsaya baki zuba masa ba ? "

Na girgiza kai alamar A'a, ta wucewarta daki bayan Musa ya fita.

Washegari bayan sallahr isha'i kowa ya dawo gida gashi an dauke nepa gidan dundum yana shigo a tsakar gida ya tarar dani ina zaune sai yace,

"Ke safiya zo nan"

Na mike na nufe shi naje har inda yake sai yace,

"Maza ki cire kayanki ki daura zani ki biyoni bayi"

Shi fa duk a tunanin shi Abubakar yayi disvirgin dina, na kalleshi da mamaki nace,

" Wanne irin in cire kaya na biyoka bayi"
Na yi tsaye ba tare da na tafi zuwa cire kayanba ai kuwa ranshi ya baci yace,

"Wai safiya ba dake nake bane da kika yi tsaye kika sani a gaba"

Rigar jikina daman jacket ce kunsan yadda jacket take tana bayyana saman Albarkatun kirjin mace ban an karaba kawai sai ji nayi ya kawo hannu yana taba min kirji ai a zabure na buge hannun shi nace,

"Wallahi kul ka kuma taba min jikina bana son iskanci me ka maidani ina matsayin kanwarka ne fa wallahi bazan dauki wulakanci ba"

Ashe dayan yayan namu sunusi yaga abinda ya faru ya hade rai yace masa,

"Kai lafiya ? "
Nan ya daburce ya fara kame-kame yana cewa,

"Abu nagani shine nake kakkabe mata"
Da mamaki ya kalleshi yace,

"Ya za'ayi cikin duhun nan kaga abu a jikin ta maza fada min abunda ka gani kuma ka nuna min shi"

Nan ya kuma rikicewa yace,

"Ai ni daman bayi zanje ba wurin ta nazo ba"

Ya dauki buta ya wuce bayi abinshi yaya sunasi ya ja tsaki ya wuce dakin Maman shi wato uwar gidan.

Yana jin tafiyarshi ya fara kirana yanacewa,

"Ke Safiya kikawo min ruwa ina bayi"

Nace,
"Wallahi bazan kawo ba ! Bazan kawo ba !!! "

Sai yayi shiru ya dade a cikin bayi sannan ya fito ya sameni a zaune lokacin ba kowa yace,

"Ke dallah y'ar iska waye bai san halinki ba to abunda kike bawa Abubakar yana ci shi nima nake so ki bani naci"

Sai kace wani abinci🤭

Sai nace,

"Malam wallahi ni ba y'ar iska bace ni ba karuwa bace abinda kuke tunanin inayi da Abubakar wallahi ba haka bane hasalima bai taba neman hakan a gurina ba, kuma kai da ka nema bazan baka ba na hana babban kwabo kawai mts"

Naje na samu mamana in fada mata duk yadda akayi gudun kar taji zancen a waje tayi zaton ko bani da gaskiya washegari ta daukeni ta kaini gurin kanwarta ta fada mata duk yadda mukayi da musa.

Kanwarta tace,

"Kin gani tunda kinsan yaron nan Abubakar yana son safiya ki kyalesu suyi soyayyarsu"

Mamana tace,

"Wallahi bazan bari ba ai nasan duk wanda zai ce yana son safiya a yanzun to ba sonta yake ba wayo zai yi mata ya rabata da darajarta"

Kanwarta tace,

" Daman ni shawara ce na baki don karki manta a yanzun Ss 2 zata shiga a ganina don ta tsaya da saurayi ba wani abu bane"

Mamana tace,

"A'a ita fa bata yarda da hakan ba a dole kanwarta ta kyaleta tayi min fada sosai akan na cigaba da kame kaina, nayi mata godiya muka nufo gida ni da mamana.

Haka rayuwar taci gaba da juyamin a kullum sai an shirya labari an fadawa mamana ita kuwa daman ba ruwanta da bincike zata nada min duka ne kawai.

Kuma babu mai kwata na agidan duk yawan gidan.

Daga baya ma mamana da kanta ta koreni daga dakin ta tace bazata zauna dani a daki guda ba, uwargidan Babana ita tace,

"Ai baza'ayi hakaba ki dawo dakina ki zauna ai nima uwace"

Na tattaro kayana na koma dakinta da zama kwata-kwata mamana ta fita har kata ta cireni a gabanta bata ma san Allah yayi ruwana a gidan ba, rayuwarta kawai take yi bata da damuwa don bata kaunar naje gurin ta.

Shekara ta zagayo kowa mahaifiyarshi tayi masa dinkin sallah amman banda ni kuma ga uwata a raye ubana a raye amman saboda Abubakar na rasa su tare da duk wata hidimarsu gareni.

Babbar matsalar Mamana rashin bincike komai aka fada mata ta zauna a kanshi kenan bata la'akari da halayyar mutum zai aikata ko bazai aikata ba, duk abinda akace mata y'arta ko danta yayi a gurinta ya aikata ne kawai bazata tambayeshi ba zata yanke hukunci.

Haka nan akayi sallah kowa yasa sabon kayansa ni kuma na wanke tsohon kayana nasa abina.

Haka nan nacigaba da rayuwar kunci a gidan mahaifina, ga kuma firdausi ta dawo da halinta a kaina ganin bana tare da mahafiyata tasani gaba, ta ringa hadani da jikokin hajiya rabi har sai da mukayi fada sosai hakan yasa itama ta koroni daga dakin ta tace,

"Bazan iya ba na taimakeki amman kina fada da jikokina ki koma dakin uwarki mai bakin hali kawai uwarki ta koreki ma ballantana ni"

Na kwashe kayana ina kuka na nufi gidan kanwar mamana na fada mata duk abinda ke faruwa mamaki tayi sosai ta kuma ce na dawo gidanta na zauna, na koma gidanta.

Wata na biyu a gidanta sannan ta samu ta shawo kan mamana ta hakura na koma gidanmu.

Alkalumman:

Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍

Pls share and comment
[6/30, 2:05 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 15/16

Na dawo gidan naci gaba da zama cikin kunci da matsi kowa ya tsangwameni magana daya biyu safiya yar iska.

Wata rana ina fita naje makotanmu a ranar banma hadu da abubakar ba amman mamana tana dawowa akace mata wai anganni da Abubakar yana latse ni, a take muna haduwa mamana ta dauramin wani gigitaccen mari wanda yasa na dauke numfashin wucin gadi na fara ganin juwa tana daukana,

Nan mama tayi min duka zancen duk ya karade unguwarmu dama family house dinmu dake zaria kasancewar y'ay'an hajiya Rabi sunfi rayuwa acan shi yasa suka kwashe karya da gaskiya suka fadawa dangin mu, cewar nazama y'ar iska bin maza nakeyi na zama karuwa harda ciki nayi aka zubarmin hakan yasa duk sukaja kunnen y'ay'ansu akan su daina mu'amala da ni.

Duk family din mu babu inda zanje na samu salama saboda anbata min sunana ako ina kowa gudu na yakeyi,

Kaf din yaran gidanmu mata babu wadda babanmu ya taba daga hannu ya daketa sai ni saboda makiya na da magulmata na da kuma *Sharrin y'an uba* sai da aka zigashi yayi min dukan tsiya.

Hakan yasa na fara kokarin cire Abubakar daga zuciyata duk da irin son da nake yi masa na fara ja baya daga gareshi.

A lokacin da na shiga Ss 3 sai kuma farin jini na ya karu masu kudi suna yawan zuwa gurina har gidanmu duk da bawai ni ke nuna musu gidanmu ba tambaya suke yi.

Nan fa zance yakara bin gari yanzun iskancin nawa ya karu gashinan harda alhazai masu motoci ke biyoni har gida.
Chapter 5 · 0% Book details