Sashe 11
Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace na amshi kudi gurin yayata da take tudun wada inje aaibiti don ayi min scanning, na amsa da toh haka kuwan akayi na kira yayartawa na fada mata ta aikomin da kudi naje gurin scanning.
Ashe inda naje basu iya scanning ba domin cemin sukayi su basuga komai ba, na koma gida ina zuwa Aunty murja ta amshe result din ta duba sai cewa tayi,
"Ai daman nasan karya ne babu wani ciwo a jikinki kawai salon ki barni da aiki ne"
Ina hawaye nace mata
"Wallahi Aunty inajin ciwo a jikina don ni kadai nasan azabar da nake sha idan ya tashi" sai tace,
"Me kike nufi kenan ko cewa zakiyi shima scanning din karya ne, ni dai nasan ko wanne ciwo gareka idan kayi scanning za'a gani matukar ba karya bane"
Ganin bazata fahimceni ba yasa na tashi na bar gurin.
Bayan sati biyu naji ciwon yaki ci yaki cinyewa sai na kara kiran mamana na fada mata cewa
"Nayi scanning sunce basu ga komai ba kuma ni banida lafiya har yanzun"
Tace ''toh bari zan kira Auntyn taki"
Da dare mamana ta kirata tace mata,
"Ina son safiya taje kaduna don nayiwa wani doctor magana zai duba min lafiyarta"
Ta amsa da toh, ai kuwa da safe ta fara sababi kamar me tana cewa,
"Eh kinji dadi burinki ya cika mamanki tana makka taje sauke farali kina ta faman kiranta kin tada mata hankali sai da kika sata kashin kudi saboda karyar ciwonki ki kyaleta tayi ibadarta lafiya amman kinki to ke kika sani ba dai kaduna ba Allah ya raka taki gona"
Gashi a lokacin mun fara exams dole na tsaya domin kar nayi missing a haka nake shiga aji bana iya yin komai sai dai nayi zaune ina jinyar kaina classmate dina kemin exams sai a mikomin nayi submit kamar ni nayi.
Washe garin ranar da muka zana last paper na kama hanyar kaduna lokacin kuwa babbar sallah ta kusa.
Tun zuwana kaduna na fara ganin doctor kadan kadan lafiya ta fara zuwarmin don a farko ance sai anyi min aiki sai naci sa'a maganin da aka bani yasa na fara warkewa.
Lokacin sallah ya zo tun ranar Arfa kishiyoyin mamanmu suka sakomu gaba da dariya da habaici wai naman da muke ci duk shekara bana bazamu samu kamar shi ba.
Shiko babanmu duk yayi sanyi don ya saba duk shekara mamanmu ke shugabantar aikin sallah har a gama amman wannan shekarar bata nankuma duk kishiyoyin ta sunja baya babu wadda ta kula da shi.
Ranar sallah Akayi yanka suka kime naman nan ko y'ar hantar da mamanmu take dafa masa bai samu ba don babu wacca tayi tunanin dafa masa har karfe biyu na rana ba 'a fara aiki ba.
Yaran gidan sai tsaki sukeyi suna cewa "Inda goggo maryam tana nan da tuni munci naman nan amman yanzun ko fara gyaranshi ba'a yi ba.
Yayan mu ya shigo yana ta fada " gida duk y'ammata amman ko wacce ta makale a daki kamar daddawa don karkuyi aiki"
Caraf uwargida hajiya Atika tace,
"Ai yau ba girkina bane girkin Amarya ne sai ta fito ta fara aikin ta"
Amman maman firdausi ko tari batayi ba ballantana asa ran zatayi, yayanmu ne ya takurawa y'anmatan dole suka fito suka wanke naman suka hasa wuta suka dorashi tare da zuba maggi da Albasa kowacce ta kara tayi gaba, tana zuba tsaki ni kuma suka ce naje na gasa nama abawa mazan gidan.
Suka hanani magi naje na tambaye su suka hanani ni kuma nace,
"Wallahi bazan dauki magginmu na gasa muku nama ba don haka ko ku kawo maggi ko naje na gasawa babana nama shi kadai"
Dayake lokacin bakina ya fara budewa naje na gasawa babanmu nama shi kadai na kai masa yayi ta shi min albarka ya cinye tas.
In kikaga gidannan sai ki rantse ba babbar sallah bace, aka bar nama akan wuta yana ta dahuwa ba a motsa ba, babanmu ya kira maman firdausi yace ta duba naman nan sai ta tabe baki tace,
"Allah ya kiyaye na zauna nayiwa kato aikin nama yaci toh wallahi ba da ni ba"
Ina zaune a gurin nayi murmushi nace,
"Allah ya jikan goggo maryam ba don ta mutu ba nasan inda tana nan da tuni naman nan ya zama tarihi kuma aci ana cewa nata yafi yawa"
Ai kuwa ta hayayyakomin kamar zata cini danya nace,
"Ah ah fa ni ba dake nake ba yadda kikayi maganarki nima nayi"
Taja tsaki ta koma daki tana fadan nayi mata rashin kunya
Nawa wo
Wai shin ya za'ayi da naman nan ? Zai lalace ko kuwa? Ni dai nace da sun bani in kaiwa y'an *gorgeous writer forum* nasan su da cin nama da kuma iya aikin shi masamman...............ba ruwana wlh kar tayi min duka
Daga Alkalumman:
Maman nurul huda
And
Maman ihsan
Please share and comments
Comments yasa nayi typing biyu yau😃
[7/10, 2:56 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*
*True life story*
Story by : Maman Nurul Huda👄
Written by: Maman Ihsan😍
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !
🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟
🌟G. W. F🌟
Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.
Page 33/34
Haka aka bar naman nan akan wuta kowacce shige da ficenta takeyi babu wadda take da niyyar kula naman.
Ganin naman zai lalace sai na dauko wayata nasa kati na kira yayata na ce mata,
"Wallahi Aunty za'a bar naman sallah ya lalace baba yayi asarar kudin da ya siyi dabbar gashi nan an dorashi kan wuta ko juyashi ba'ayi ba ballantana a soya shi"
Sai yayartawa tace gata nan zuwa don daman ta gama nata aikin mijinta bai yi yanka ba wanda makota suka bata ne kuma ta soye shi.
Cikin mintuna ta iso tana zuwa na kama mata muka fara aikin, tana dago naman gurin juya shi kasan ya dafe ya daddage kuma babu gishiri ballantana maggi sama kuwan danye kwata kwata bai dahuba sai uban maggi da gishiri da ya dan kale,
Haka tasa karfinta tayi aikin nan tsaf ni kuma ina tayata, ta soye naman nan ta ajiye, da yake kwana zatayi bata bar aiki ko daya ba,
Tana tafiya aka fara tsegumin tazo ta kwashe nama ta kai gidan mijinta, kuma fa ba ita tayi rabo ba su suka raba da kansu.
Matasan gida ko suma sai gunguni sukeyi an basu nama kadan ba kamar yadda mamanmu take basu ba, don daman mazan wadanda sukayi aikin yanka sai ta cika musu samira amman wannan shekarar cikin ledodi suka basu.
Haka dai akayi sallahr nan kowa yana tsegumi bayan sallah na koma zaria gurin karatuna don Alhamdulillahi naji sauki sosai.
Haka nan lokaci yake ta tafiya nima inata karatuna da dadi da babu dadi ina hakuri, wani hutu da muka samu sai mukaje katsina garin su Aunty murja y'an gidansu suna sona don har munyi sabo da su babu mai tsangwama ta.
Bayan mun dawo Aunty murja ta kwanta ciwo mai tsanani ni nake hidimarta da hidimar gida da kuma karatuna amman wadannan da suke zigata ko dubiya babu wanda yazo.
Ni din dai da take wahalarwa take wulakantawa ce a kanta da dukkan bukatun jinyarta daga nan fa jikinta ya fara sanyi ganin ban taba gajiyawa da hidimaeta ba nan fa ta fara tunanin
"Anya maganganun da ake fada a kaina gaskiya ne? Ko dai ana fada mata ne don ta cutar dani?"
Haka tayi ta sake sake a ranta, har ta samu lafiya a wannan lokacin ne na koyi hada room freshener.
Daman yanzun ina dan samun kudi gurin Ahmad ya kan aiko min kudi dubu daya biyu har zuwa uku, to a lokacin ya aiko min dubu biyu na dauki dubu biyun nan na fara hada room fresh dashi.
Maganar Aurenmu da Ahmad tayi karfi don har manya sun shigo zancen, nan fa mahasadana wato y'an ubana suka kara tsangwama ta ganin Ahmad ya fito daga babban gida suna ganin zan shiga gidan hutu, suka takuramin sosai don ko Aunty murja batayi niyyar yi min abu ba sai sun sata tamin.
Ina fara room fresh din na bawa Aunty murja na dauki wasu na kaiwa kanwar mamana.
Kwana biyu da bata room fresh ta duba bata gani ba sai ta hau bala'in wai na dauke roomfreshener na kaiwa kanwar mamana.
Ina dawowa daga makaranta ta tareni da tambaya
"Ina kikaje?" nace,
"Daga makaranta nake banje ko ina ba" tace,
"Ba naji kina cewa nusaiba zakije gidan kanwar mamanki ba?"
Na dafe kirjina nace,
"Ni ? Wallahi bance ba kuma banje ko ina ba kinsan idan zanje guri dole sai na fada miki ban taba zuwa wani guriba ba tare da na sanar miki ba"
"Toh naji ina airfreshener din" ta fada tana ballamin harara
Na dauko mata na nuna mata wanda na dauka zan kaiwa kanwar mamana, tayita y'an kame kamenta ta fice,
Bansan wa ya kawo mata gulmar karya ba wai an ganni na je yawo, matar nan ta daina yimin magana ko gaidata nayi bata amsawa sai da na rufe sati guda ba'a bani abinci a gidannan, biscuit shine abinci na da yake ana rabawa yara biscuit malam nasiru kuma yayana wato mijin Aunty murja malamin makaranta ne shine yake kawo mana sauran ya raba mana ni da nusaiba da mai sunan babanmu,
Biscuit din nan shi zanci da safe da rana da dare, ni kuma na fita hanyarta banje na tambayeta me nayi ba kuma ban bata hakuri ba.
Ranar ta sameni a daki ta zageni tsaf tare da cimin mutunci wai naki zuwa na bata hakuri ni kuma nace,
"Wanne irin hakuri kuma Alhalin ni nasan banyi miki komai ba inda nasan nayi laifine" sai cewa tayi
"Toh shi kenan sai kiyi hakuri nasan na horaki da yunwa je ki dibi abinci ki ci"
Tun daga ranar ta sassautamin daga horon yunwa, daya ke yanzun ina samun zuwa gurin kanwar mamana har nayi sati kadan kadan ta fara fahimtar halin da nake ciki sai cemin