Sashe 10
Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abu kuma da yake kona min rai kullum na fita naje makaranta sai an zazzage min jakata na rasa me ake nema acikin jakar makaranta ta, ni a tunanina yara ne suke min haka amman daga baya na fahimci ba su bane tunda kullum sai hakan ya faru kuma wani lokacin nakan ajiye jakar inda yaron bazai iya dauka ba amman still sai an zazzage.
Wani abin haushi ko ince na dariya ana zazzage jakana ne don a gani ko akwai condom a ciki tunda ansan y'an iska da yawo da condom saboda gudun ko ta kwana.
Ban taba korafi ba saboda nasan ina da gaskiyata rannan dai abun ya ciyo ta da kanta ta fadi kanta.
Ta ringa fada wai ita bata yarda dani ba" ba kya dawo wa gida da wuri kina famar bin maza a titi wallahi kicigaba dai ga HIV nan tana yawo a gari"
Ranar naci kuka ba kadanba daga karshe na lallashi kaina na fawwalawa Allah lamurana, ana haka muka fara exams mai zafi lokacin barcina na ke ajiyewa nayi karatu saboda da rana bani da lokacin da zan dauko littafi,
Rashin barci ya sako ni gaba duk jikina ya daina yi min dadi ga babu isashshen abinci, in wuni a school in dawo gida na tarar da ayyuka suna jirana.
Wata rana paper hudu mukayi har sai da nakai magriba bamu gama ba kuma bani da credit a wayata bamu taso ba sai 7:30pm ga hadari ya hado yayi baki kirin kuma banida kudin mashin ballantana na samu na isa gida da wuri.
Ina cikin tafiya ruwa ya tsuge da karfi har wayata sai da ta fadi screen ya dagargaje nayi sauri na dauka ina sauri in isa gida da wuri don hanyar bata da kyau idan dare yayi har raping din y'ammata ake yi ko kuma wani lokacin a tsinci gawar mutum an yanka shi.
Haka na daure ina addu'a nabi hanyar nan ina sauri don Allah Allah nakeyi na isa gida ruwa yayi min dukan tsiya da kyar a tsorace na isa gida.
Ina shiga gidan tun daga tsakar gida ta tsayar dani tana cewa,
"Kar ki kuskura ki shigo min daki har sai kin fada min daga inda kike gidan ubanwa kika je?" nace,
"Wallahi Aunty daga makaranta nake kuma wayata babu kati shi yasa ban kiraki ba, kuma wayar ta fashe"
Sai tayi kwafa tace,
"Humm Ki fadawa wanda bai san hali ba amman ni kam ko duk jikina kunne ne bazan yarda ba idan yayanki ya dawo kyayi masa bayani"
Na cire kayana na nufi daki na shanya takarduna na koma kicin tsaye nayi ina kallon kular abincin da dan abincin da ke ciki bai fi cokali daya ba.
Gashi na kwaso yunwa tun tea din safe ne a cikina haka nan na lomace dan abincin na side hannu na, naje nayi alwala nayi sallah na kwanta.
Washe gari haka yayana ya tsareni da tambaya shima yadda nace mata haka nace masa yace,
"Toh wallahi zanje na bincika idan na ji akasin haka ranki sai yayi mugun baci don na fara gajiya kullum ke sai an kawo karar ki anganki anan an ganki acan"
Na shaki kukana na shirya na wuce makaranta, a ranar aka sanar damu sai bayan sati biyu result zai fito, naje na fadawa Aunty murja sai tayi murmushi tace,
"Allah ya nuna mana don result dinki shine zai baki lasisin zama kici gaba da karatu a gidan nan ko kuma akasin haka"
Na ja jikina na koma daki ina addu'ar Allah yasa naci exams din.
Sati biyu yana cika naje ganin result abun farin ciki five point na samu nayi murna sosai da fara'a ta na nufi gida naje na nuna mata ita da kanta sai da tayi mamaki don bata zaci haka ba.
Daga Alkalumman:
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan 😍
Please share and comment
[7/9, 1:09 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*
*True life story*
Story by : Maman Nurul Huda👄
Written by: Maman Ihsan😍
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !
🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟
🌟G. W. F🌟
Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.
Page 29/30
Shiru tayi tana mamakin result din sai juyawa takeyi tana tabe baki tace,
"Ah lallai uwayen yawo sunci exam amman nayi mamaki kwarai da gaske wanne lokaci kika samu kika yi karatun har kika samu wannan result din ko da yake ba abun mamaki bane"
Ni dai murmushi kawai nayi bance komai ba, yayana yana dawowa ta nuna masa shima yayi mamaki sosai don cewa yayi,
"Ni lokacin da nayi karatu kaf department dinsu babu wanda ya fito da five points Lallai yarinyar nan Allah ya taimake ki ashe dai kina karatun zan tsaya miki kici gaba "
Nayi masa godiya sosai Mamana ta kirani tace,
"Safiya zan biya miki jamb kiyi sai ki zo nan kaduna kicigaba da karatun" nace,
"Ni ba ma jamb bane yafi damuna illah WAEC don bani da maths kuma kinga dole sai na canza ko five credits ne in samu" tace,
"Hakane kuma to Allah ya baki sa'a yasa ki samu"
Na amsa da "Ameen"
Mamana ta biyamin kudin waec naje na samu Aunty murja nayi mata bayani kawai sai ta hauni da fada tana cewa,
"Wanne waec kuma kawai dai kice kina son tafiya gidane kije gurin samarin ki toh babu inda zaki je"
Har tayi shiru ban tanka ta ba na je daki na kira mamana a waya nace,
"Goggo kiyiwa Aunty murja bayanin zanje kaduna gurin jarabawa"
Ta amsa min da toh ta kirata ta fada mata bata nunawa mamana komai ba tace,
"Ai ba komai Allah ya kaimu lokacin"
Ranar da zan tafi kaduna nasha habaici kala kala dole na naji nayi kamar banji ba harda mugun fata wai
" Allah yasa na fadi a waec din inje inta biye maza tunda bin mazan nafi kwarewa"
Ni dai bance komai ba haka na nufi kaduna naje nayi jarabawa ta abin farin ciki dukka papers din naci illah Accounting shi kadaine na samu pass na dawo zaria da farin cikina.
Ban dade ba kuma da dawowa lokacin jamb yayi nace mata zan koma nan ma da kyar ta barni kuma ta bini da mugun baki.
Kuma ta hanani kudin mota alhalin tana da shi gurin classmate dina na ari dari biyar da magriba na tafi kaduna karfe takwas na isa kaduna.
Haka na samu nayi jarabawar nan kuma Alhamdulillahi shi ma jamb din naci.
Nan Mamanmu tace za'a mai dani ABU amman yayana da Aunty murja suka kafe akan sam tunda na fara FCE to sai dai na hakura nacigaba anan,
Haka suka sa mamana asarar biyamin jamb tunda bazanyi amfani dashi a FCE ba mamana ta bani hakuri tace nacigaba anan din ba komai.
A wannan karon yayana ya dan taimakamin tunda ya biyamin wasu kudi da aka bukata lokacin neman admission babanmu bai ma sani ba.
Duk da hakan na wahala sosai don baije da kanshi gurin neman admission ba ni nayita fafutuka sai da aka fara karatu na samu.
Kuma yaki biyamin kudin registration mamana ce ta aikomin da rabi babana ya biya rabi, ga kuma kudin register makaranta shima bani da shi naci kuka na na koshi.
Daga baya na yanke shawarar kiran yayata wadda take tudun wada nayi mata bayani tace,
"Wallahi safiya nima bani da kudi naira dubu biyar kawai zaki samu a gurina don duk kudin hannuna na tattara na biya kudin cs dasu "
Na yi mata godiya nace,
"Nagode Aunty zama su isheni Allah yasa ayi miki cs din a sa'a ubangiji ya baki lafiya "
Ta amsa da ''Ameen" ai kuwan ta turomin dubu biyar din nan naje nayi registration na cikin maka ranta na samu canjin dubu biyu da dari uku.
Tsautsayi mun gama lecture sai na manta jakata a class kafin naje har na samu wata ta zare kudin ta barmin dari takwas kawai gashi ko handout ban siyaba kuma bani da wani kudin.
Har semester din nan ta kare ban samu kudi ba ballantana na siya handout sai da exam tazo a lokacin mun saba da wani classmate dina shi nake bawa kudin photocopy yayi min daga baya da ya fahimci banida kudin sai ya fara siyan guda biyu sai dai kawai naga an bani handout nayi masa godiya wani lokacin harda hawaye nakeyi a boye.
A wannan lokacin da karatu yayi zafi idan kikaga yadda kafata ta tsattsage saboda tafiyar kafa wallahi sai na baki tausayi amman ko daga kai Aunty murja da yaya basa yi ballantana nasa ran za'a bani na ocada, haka zan tafi a kasa na dawo a kasa kuma idan ban dawo da wuri ba masifa ga aikin gida a gefe guda.
Idan na samu na siya takalmi ko wata biyu bayayi ya lalace saboda tafiya, ina cikin wannan halin kuma ciwo ya sakoni gaba
Daga Alkalumman :
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍
Please share and comment
[7/9, 3:59 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

Page 31/32
Ciwo ya sakani gaba wato appendix daman na taba yinshi tun ina secondary amman yanzun yafi takuramin don inya rikeni bana iya motsawa sai in ya sakeni.
Nan fa Aunty murja tace batasan zancen ba don bata ragemin aiki ko daya ba haka ina cikin aiki zai tashi na sandare a gurin ina hawaye ko kallona bazatayi ba ballantana na samu arzikin sannu ko ta ragemin aiki ba.
Sai dai ta shiga fadan naki nayi sauri nayi mata aikinta ita babu ruwanta da wani karyar ciwo da nakeyi kuma dole kiyi aikin nan.
Tun in ya tashi daga tsaye nake sandarewa har ya kai inya tashi dole sai na kwanta a gurin ko inaso ko bana so, gashi a lokacin mamana ta tafi saudia na kira mamana na sanar da ita halin da nake ciki.