← Book details Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duniyar ta kara yimin kunci, ada ina tunanin idan na rabu da Abubakar za'a sakarmin mara nayi fitsari ashe ba haka bane, wani ballin daban ne zai kunno kai.

Babban wana ya kamani yayimin dukan tsiya, na zamo tamkar jaka wannan ya daka wancan ya daka kullum cikin duka duk iya kokarin da nakeyi don na fahimtar dasu amman sun kasa fahimta ta.

Haka nan nayi ta rayuwata mahaifiyata bata bani fuska ba ballantana na sanar da ita damuwata ba har na gama secondary school, acikin yayyena mata wadanda suka yi aure yayarmu babba mace a dakin mu ita kadai ce take tausayamin.

Nan ta fara cewa inje wurin ta inyi mata hutu sai inje sati daya nake yi na dawo bazan dade ba zata kuma neman nazo, tana son zama dani don bani da k'iywar aiki domin a unguwarsu basu da ruwa sai kayi tafiya kafin kaje inda ruwan yake haka zan kwashi bokitai na tafi na debo mata ruwan.

Don nafi son zaman gurinta akan gidan mu duk da ina mata aiki amman nafi sakewa akan na zauna gurin da kullum ina cikin cin duka.

Kullum sai naje dibar ruwa hakan yasa na fara sabawa da mutanen unguwar muna dan gaisawa a tsakanin mu, wata rana naje dibar ruwa na dawo sai aka aiko ana sallama da ita sai ta fita don ganin wake kiranta.

Tana fita sai taga police a tsaye bayan sun gaisa yace,

"Don Allah yarinyar nan da take dibar ruwa kullum 'yar aikin ki ce?"

Sai tace masa

"A'a ba 'yar aikina bace kanwata ce mamanmu daya da ita baban mu daya tazo hutu ne"

Nan yayi mata fada akan don ba ita tahaifeni ba shi yasa kullum take aikana dibar ruwa, ta kalleshi da mamaki tace,

"Malam yarinyar nan fa kanwata ce uwa daya uba daya kuma bani da ruwan nan mene aibu don ta debo min ruwa?"

Sai yace, " wannan ne kawai matsalar?"
Tace masa "Eh "yace,

"Toh ni zansa a ringa kawo muku ruwa amman ta daina zuwa dibar ruwa"

Tace, "Toh" tare da yi masa godiya yayi tafiyarshi,

Haka ake kawo ruwa kura daya kullum, rannan ta fita unguwa sai wasu samari a unguwar suka gaidata tare da tambayarta

"Kwana biyu mun daina ganin kanwarki tana zuwa dibar ruwa "

Sai tayi dariya tace,

"Ya akayi kukasan kanwata ce?"

Sai sukace, "Ai daga ganin ta ansan kanwarki ce ba sai an fada ba"

Tayi murmushi tace, "Tana gida"

Sai suka ce," don Allah muna neman Alfarma a gurin ki?"

Tace,
"Ina jinku Allah yasa bata fi karfi na ba"

Sukace, "Dibar ruwan da takeyi muke so ta daina zamusa mai ruwa yana kawo miki ruwan"

Abin ya bata mamaki ya kuma daure mata kai tayi musu godiya ta je ta dawo ta sameni tace,

"Safiya daman irin farin jinin da kike dashi kenan? Gaskiya dole ki samu matsala a gida saboda ba lallaine aganki da irin wannan farin jinin ba ba tare da anbiki da mugun abu ba"

"Kinsan me yasa kika ga na daina turaki dibar ruwa?"

Na girgiza kai nace, "A'a" tace ,

"Rannan wani police ni ban ma san a inda yake ba shine ya dauki nauyin kawo mana ruwa kuma gashi yau wasu samari suma sunce na daina turaki dibar ruwa zasu sa a kawo mana"

Washegari na shirya zanje gida domin inje inga gida sai tace tare zamuje,

Muka je gida tare suna hira take cewa,

"Goggo Ki daina dukan safiya akan samari domin ba yin kanta bane Allah ne ya yita mai farin jini duk inda ta shiga saita samu masoya"

Nan mamana ta rufeta da fada sosai tana cewa,

"Karki kara fada min wannan maganar don kuwan safiya ta riga ta lalata kanta"

Ta fada mata cewar,

"Wallahi goggo ada ni nake zuwa na debo ruwa da safiya tazo sai na fara aikenta inta kaice miki yanzun kurar ruwa biyu ake kawo min kullum saboda safiya kuma bata san wadan da suke kawo waba"

Mamana ta kafe sam bata yarda ba wai hada baki mukayi ni da ita tazo tana mata dadin baki.

A bisa kaddara sai kariyar arziki ya samu mijin yaya Aisha da yake gidan haya suke sai aka koresu ta dawo nan gida dakin mamana ta zauna.

Kaf din gidan nan ita kadaice ke kwata ta a hannun mamana ta bata hakuri idan tana dukana kuma tayita lallashina.

Ana haka itama yayata wadda nake binta ta dawo gida nan itama ta matsamin tayita min fada har sai yayarmu Aisha ta tsawatar mata, don maman mu ko daga kai batayi ballantana ta nuna tasan abunda muke yi.

Ana nan sai naga zaman haka bazai yi min ba sai na fara hada sitati irin wanda ake sawa a shadda ina siyarwa duk yin da nayi saina saida kuma ina samun riba sosai na fara tara kudina don inason in yi waec saboda shekara ta zagayo ban samu nayi ba.

Ana cikin wannan lokacin irin y'an siyasar nan masu campain suka biya mana neco mukayi lesson sannan muka zana neco.

Allah ya taimakeni na fito da credit uku English, geograph da government amman bani da maths.

Yanzun kishiyoyin mamana sun kara matsa mata da gangan zasu kirkiri tafiya garuruwansu su kime mata aikin gida ga kuma tana zuwa gurin aiki hakan yasa ta fara sarara min tana dan sakewa dani wani lokacin har muyi hira.

A kwai wata sallah babba dayake baban mu ita yake dorawa akan aikin naman sallah haka zasu tsame hannun su su barta da aiki kuma in anzo rabon nama a shiga bala'i ana cewa duk ta handame naman daga ita sai y'ay'ata babanmu ne yake bata hakuri.

Wata rana muna hira take cemin,

"Safiya inda zakiyiwa kanki fada ki shiryu irin haka da yafiye miki"

Nayi murmushin takaici nace,

"Goggona" ta amsa da "Na'am"nace,

"Wallahi tallahi ni ba y'ar iska bace ko hannu na ban taba yarda wani namiji ya taba ba, amman ana hadani dake alhalin ni ko yawo bana zuwa"

"Munafuka ni zaki yiwa dadin baki ne zaki lallameni ko?"

Ta fada a fusace nace,

"Shikenan goggo Ina addu'ar Allah ya bayyana gaskiya kuma ko wane ne munafikin sai Allah ya sakamin"

"Safiya fito fili kice min Allah ya isa tunda ni sa'ar ki ce"

Ta fada a fusace tare da rufeni da duka naci kuka na nagodewa Allah.

Nawawoo this story make me cry sometime ooo, the star of this story i say sorry to you 😢 Allah is with you

Alkalumman:

Maman nurul huda 👄
And
Maman ihsan😍

Love you fans please what can i say next 🤔
Oo
Please share, comment and pray for us
[7/2, 3:33 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 17/18

Dedicated to Rayuwar safeeya fans duk da dai bakwayin comment sosai pls ku gyara.

Yawan dukana da akeyi yasa na fara sabawa da shi don nayi laifi ko dar banaji saboda nasan dukane kawai kuma ko banyi ba za'a yi min makircin da zai janyo a dakeni hakan yasa za'a iya yi min mugun duka amman ko ajikina ana gamawa zan share hawayena na yi tafiyata daga karshe ma ko da za'a yi min dukan mutuwa bana kuka saboda ya riga yabi jikina tamkar icce ake duka.

Kudin sana'a ta inata tara su domin bana kashewa wata yayarmu diyar Hajiya Aisha tana karatu a zaria data zo hutu ta sameni tace min

"Safiya naga kina son karatu kuma baba yaki biya miki mai zai hana kizo zaria dubu biyun ki ya sai miki form ki fara karatun ki tunda kina sana'a"

Nace mata,

"Wallahi inaso kuwan kuma ina da kudi a ajiye" tace,

"Toh kiyi shawara" na amsa mata da toh.

Naje na samu maman mu da zancen na sanar da ita inason karatu tace,

"Toh Allah ya bada sa'a yasa karatun ya zamo silar shiryiwarki" na amsa mata da Ameen.

Shima babanmu na sameshi nayi masa bayani cewar inason naci gaba da karatu kuma a zaria zan sayi form yace,

"Toh safiya ni dai gaskiya bani da kudin daukar karatun ki saboda yanzun ba kamar da bane" Nace,

"Insha Allahu Allah zai hore daga yanzun zuwa lokacin da admission zai fito" yace,

"Toh safiya amman a ina zaki zauna don bana son ki zauna a hostel don na riga nasan halinki" Nace,

"Wallahi baba zan iya zama a hostel kuma zan kare mutunci na"

A take ya kafe akan sam shi bazai yarda na zauna a hostel ba sai dai na nemi wani gurin,

Ina fitowa na samu yayar nan tamu iklima na fada mata yanda mukayi dashi tace,

"Toh ince masa zan zauna a gidan da take zaune gurin yayarta suwaiba"

Naje na sameshi na fada masa sai yace,

"Ina bazaki iya zama da suwaiba ba domin tana da zafin rai nasan halinta sarai tana da mugunta da bakar zuciya baza taso ki rabeta ba har ki zauna kiyi karatu a gurinta ba domin ko anan gida bata shiri da goggonki baxai yiyu ba ki canza shawara"

Nace masa Toh har na mike ya kirani yace,

"Ga ma babban yayanku tunda shima yana zaria kuma yafi kusa FCE bari na kirashi"

Ya dauki waya ya kirashi ya sanar dashi komai sai yace,

"Ai kuwa nan da wata biyu admission zai fito kuma matata taje ganin gida katsina idan lokacin yayi sai ta zo babu damuwa"

Cikin ikon Allah kafin watannan biyu mun fara jituwa ni da Mamana muna zaune muna kallo sai gashi an kirata a waya ta daga wayar bayan gaisuwa akace,

"Hajiya Maryam kina ina ne ?" sai tace,

"Bana gida ya akayi ne ?"
Kuma alhalin tana zaune a daki tare da ni sai akace,

" Ga y'arki safiya nan da wani a lungun bayan unguwarku yana lalata da ita" tace,

"y'ata fa safiya kace?" yace,

"Kwarai kuwa gata nan ina kallonsu bata san na gansu ba don suna ta aikata masha'ar su"

Tace masa,

"Na gode Allah ya biya insha Allahu zan sake kira" sai akace,
Chapter 6 · 0% Book details