Sashe 2
Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dedicated to my forum Gorgeous Writers Forum Allah ya kara hada kanmu ya kuma daukaka mu Ameen
Sai baban mu ya dauko takarda yace,
"Toh kowa ga takarda ya karanta "
Ni nafita kokari a boko, ita kuma tafi kokari a islamiyya, dukda nima ina kokarin amman tafini sai yace mu karanta.
Kasancewar bokone sai na karanta ita kuma ta kasa nan yayi mata fada yace ta ringa zuwa gurina ina koya mata, don itama ta iya a daina yi masa asarar kudin shi.
Ashe taji haushin zancen tana fita ta fashe da kuka, ta sanar wa mahaifiyarta abinda ya faru nan fa wani sabon masifar da bala'in ya barke a cikin gidan, ta fara cewa,
"Daman baka sona baka kaunar y'ay'ana a kullum sai ka nuna mana kiyayyarka kafi son hajiya Maryam da y'ay'anta to wlh ahir dinku ku dukka don nafi karfinku kuma Allah zai saka mana"
Nan tayita ruwan bala'i baji ba gani har cewa takeyi ya saketa ta huta, ganin haukan nata yayi yawa ya shuri takalmansa yayi waje yana mai yi mata addu'ar shiriya.
Haka nan rayuwar ta ringa tafiya yau dadi gobe akasin hakan, har gobe uwargidan babana tana kulle kullenta shi yasa basa kwana biyu sai sunyi fada.
Acikin wannan lokacin Naziru ya kammala karatunshi ya bar makarantar, tunda ya bar makarantar sai firdausi ta sarara min da bakaken maganganu da yimin sharri a gida.
Ana haka Abubakar ya kara bude huta gurin kafa soyayyar shi a zuciyata, shi lallai da gaske yake aurena zai yi babu wanda yasan da maganarshi a gidanmu sai Firdausi,muna ta soyayyarmu duk da babanmu ya nuna bazai yi mana aure ba har sai mun gama makaranta saboda shi mutum ne mai son karatun boko sosai.
Tun muna soyayya a boye har dai avun ya bayyana yana rakani makaranta haka idan an tashi yaje ya tarbeni, hakan yasa duk y'an unguwarmu sunsan muna soyayya amman banda mutanen gidanmu idan kika cire Firdausi, yayanmu wanda suke uwa daya da firdausi ana kiranshi *Musa* suna hira a majalisa sai yake tambayar *Abubakar* yace,
"Abubakar wai ina kake zuwa ne da safe bana ganin ka haka kuma da rana ko ka samu aikin yi ne ? "
Budar bakin Abubakar sai cewa yayi,
"Ai Kanwarka safiyya ce muke soyayya shi yasa da safe nake rakata makaranta haka da rana sai naje mu dawo tare"
Murmushin mugunta musa yayi ya gyara zama don ya bugi cikin Abubakar yace,
"Da gaske kake kana sonta kuma zaka aureta?"
"Eh mana sonta nakeyi kuma ina fatan ta zamo matata ku taimaka ku bani aurenta"
Sai musa yayi dariya yace,
"In dai auren safiyya kake so to mun baka sai ka shirya"
Cike da farin ciki Abubakar yace,
"Don Allah da gaske kakeyi?"
Musa yace,
"Eh mana da da gangan nakene? Ko ana wasa da maganar aure?"
Abubakar yace,
"Nagode dole na turo manya ayi magana"
Musa yana tashi daga gurin gida ya nufa har dakin mamana budar bakinshi sai cewa yayi,
"Nazo gurinki ne goggo maryam kuma nazo sanar miki wani mummunan labari"
Mamana ta dafe kirji tace,
"Mummunan labari fa kace Musa wannan wanne labari ne?"
"Wallahi goggo Maryam sai kin mike tsaye inba haka ba zaa lalata miki rayuwar y'arki"
Da mamaki ta kalleshi tace,
Bangane za'a...................✍
Alkalumman:
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍
Comments is needed pls
[6/23, 4:50 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*
*True life story*
Story by : Maman Nurul Huda👄
Written by: Maman Ihsan😍
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !
🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟
🌟G. W. F🌟
Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.
Page 7/8
"Bangane za'a lalata min rayuwar yarinya ba ?"
Yace,
"Kwarai kuwa don kinga safiya din nan taki ta taso da farin jini a unguwar nan kowanne saurayi ya taso sonta yake yi kinsan mene babbar matsalar?"
Cikin jimami da takaici tace,
"A'a sai ka fada min"
Yaci gaba da cewa,
"Duk samarin da suke cewa suna sonta ba don Allah bane, suna yaudarar ta ne kawai don su lalata mata rayuwarta"
Atake gaban maman mu ya fadi ta fara fadin
"Innalillahi wa'inna inna ilaihir raji'un"
Taci gaba da cewa,
"Lallai kam wannan mummunan labarine dole in hana safiya fita"
Yace,
"Kwarai kuwa dole ki hana ta fita kafin a rabata da darajar ta tare da tarbiyyarta"
Ya mike zai fita sai kuma ya koma yace,
"Kuma duk wanda yazo yace da gaske sonta yake to wallahi karya ne ba son ta yake yi ba zai yi muku wayo ne yayi duk abinda yaso da ita"
Nan mamana ta shiga yi masa godiya tana cewa,
"Nagode musa lallai ka cika dan uwa kuma mai kaunar kannen shi insha Allahu zan kula da ita sosai Allah ya taya mana"
Yayi murmushi ya fice a dakin.
Tundaga wannan lokacin Mamana tasa min ido fiye da da duk wani motsina akan idonta yake haka tana sane da duk lokacin tafiya da dawowata daga makaranta, Nan mamana duk ta canza min idan na sake yaran gidan suka rigani dawowa sai tayi ta hantarata tana fada hakan yasa na fara shiga damuwa babu wani fuska ga y'an uwana haka ga mahaifiyata.
Wata rana na dawo daga makaranta muna tafe nida Abubakar sai ga Mamana ta dawo daga unguwa, ta kallemu suka gaisa ita da Abubakar da fara'ar ta ta wuce gida.
Aikuwa ina isa gida na cire kayan makaranta na kenan sai gata da bulala ta fara tambayata,
"Me ya hadaki da Abubakar da har kika jera tare da shi kuna tafiya?"
A take kirjina ya fara dakan tara tara don nasan bani da gaskiya na fara kuka ina bata hakuri kar ta dokeni.
Amman ina sai da Mamana tayi min dukan kawo wuka har saida ta gaji don kanta tun ina kuka da ihu har muryata ta dishe ina bata hakuri.
Tace dole sai na rabu da Abubakar Amman na kasa furta mata zanyi don ina matukar son Abubakar kamar raina kuma nasan bazan iya rabuwa da shi ba.
Babu wanda yayi yunkurin bata hakuri a gidan mu sai ma dariya da wasu suke yi mana.
Dukan da mamana tayi min bai hanani kula Abubakar ba don ban ma fada masa ba ballantana na bukaci ya rabu dani, don a tunani na mama bazata sani ba tunda tana gida don bansan ana kai mata gulmata ba.
Ashe ranar da aka dakeni Yaya Musa yana nan yana cikin daki yana kallinmu ta window.
Wata rana ya shiga dakin uwargidan baban mu suna hira sai yake cewa,
"Ai in fada muku safiya ta lalace ta zama y'ar iska don Abubakar take bi"
Suka hada baki gurin cewa,
"Wanne Abubakar din?"
Yace,
"Abubakar na unguwar nan mana wanda muke zama tare a majalissa"
"Tab lallai yarinyar nan ta bata wayonta"daya daga cikin su ya fada.
Musa yace,
"Ai don baku sani bane amman iskanci ko babbar karuwa Albarka don ance har hotel yake kaita bata zuwa makaranta, idonta ya riga ya gama budewa"
"Ko shi yasa goggo Maryam tayi mata duka kwanaki?"yaya Rabi'u ya tambayeshi, yace
"Eh mana dalilin dukan kenan bata fada bane don kar zancen yaje kunnen babanmu"
Kadan kadan magana ta fara zaga cikin gidanmu cewar na zama y'ar iska daga yayyena mata har kanne aka fara janye su daga jikina wai kar na lalata su, ko tambayar su wani abu nayi sai iyayensu su bata rai su kirasu.
Haka a unguwa ma..........✍
Alkalumman:
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍
Pls your comment is needed
[6/25, 4:42 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

Page 9/10
Haka a unguwa ma kowa kallon y'ar iska yake min, amman ni bansani ba kowacce uwa tana janye diyarta daga gareni wai kar na lalata musu y'ay'a.
Shi kuma Abubakar kanwar mamanshi gurinta yake da zama kuma makotanmu ne, da ta samu labari sai tace ya daina tsareni a hanya muna hira ya ringa kirana cikin gidanta muna hira domin ita Allah ya dora mata kaunata tamkar y'arta kuma tana farin ciki da alakarmu tsakanina da dan yayarta dake wajenta wato Abubakar.
A lokacin mahaifinmu duk cikin gidanmu yafi son aike na musamman da safe inje in siyo masa kayan breakfast, sai dai in ba na nan sannan ya aiki wani cikin y'an uwana,
Kuma kanwar Maman Abubakar itace take saida kosai, da yake har tasan na nawa yake siya sana je zan tarar ta zuba ta ajiye mishi, shi yasa idan naje siyan kosan sai na tsaya muyi hirar mu ni da Abubakar sannan in dauko cooler kosan in tawo gida .
Kullum haka nakeyi tun babanmu baya fahimtar na dade har ya fara ganewa rannan dai ya tambayeni yace,
"Safeeya wai me yasa y'an kwanakin nan idan na aike ki ki ke dadewa? Bakya kawo min kosai na akan lokaci?"
Nan fa duk na rude da kyar na fizgo magana nace,
"Kayi hakuri Baba insha Allahu bazan karaba, zan ringa dawowa da wuri"
Na fadi haka ne kawai don na kare kaina tunda ni nasan inda nake tsayawa wato hira da saurayi.
Da yake Maman mu ma'aikaciya ce, sai na bari sai ta tafi gurin aiki sai na fice a gidan muje mu hadu ni da Abubakar a wani gurin muyi hirar mu.
Abinda bamu sani ba musa yafi kowa sa mana ido don ko mamana bata kaishi samin idoba don tun kafin tafiya tayi nisa ya gane ina fita idan mamanmu ta fita, shi yasa duk inda muke zuwa muyi hira ya sani duk wani AP din da muka hada sai yasan yadda ya bugi cikin Abubakar ya fada masa inda zamuyi hirar.
Shi kuma Abubakar kwata-kwata bai gane manufar Musa ba, don yana mishi kallon mai son alakarmu tunda yana nuna ya bashi goyon baya 100%.
Hakan yasa ya dauki dabi'ar kiran mamana ya fada mata cewar na fita tare da Abubakar, ita kuma tana dawowa zatayi min matsiyacin duka kuma hakan bai hana ni fita ba na rasa wa yake fada mata duk randa na fita.