← Book details Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 12

Sashe 12

Rayuwar Safeeya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

"Safiya ba wai zugaki zanyi ba amman gaskiya abinda matar yayanki take miki yayi yawa tunda dai ba uwarki bace karki sake yi mata kuka idan tayi miki ki rama idan kikaga tana miki fada akan laifin da bakiyi ba kar ki kara bata hakuri idan kuna Parlour to ki koma daki ki kyale ta kiyi banza da ita karta kuma ganin fushin ki"

Na amsa mata da toh na dauki shawarar ta idan tana masifarta ko daga kai banayi na kalleta ballantana na bata hakuri kuma bana nuna fushina ballantana kuka.

Haka muka ringa rayuwa kadan kadan sai ta fara canzawa idan aka kawo mata gulmata zata tambayeni idan na amsa toh idan ban amsa ba ta sa zancen a kwandon shara.

Zaman mi ya fara dadi muka fara fahimtar junan mu, muna mutunci sosai.

Tsautsayi rannan ta fita sai dawo da ita akayi tayi accident muka shiga tashin hankali ni nake jinyarta har ta warke wannan karon ma magulmatan ta ko leke ballantana tasa ran wata hidimar su.

Bayan ta samu sauki ta sameni ta bani hakurin duk abinda tayimin nace,

"Wallahi ni ban rike ki ba don kallon uwa nake miki tunda mamana ta mikani gareki don haka komai ya wuce Allah ya bamu hakurin zama da juna"

A lokacin sauran shekara daya na gama karatu sai aka fara maganar auren mu da Ahmad.

Nan fa tsegumi ya tashi sabo yayyena maza da zasu jagoranci hidimar duk suka janye jiki da kyar aka samu aka lallaba su harda rokon Allah Aka hada sannan zancen nan yasassauta.

Daga Alkalumman:
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍

Please share and comment
[7/10, 3:46 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 35/36

Akasa ranar mu ni da yayanmu na miji, kannen mamana suka sameta akan zancen tace zata yiwa yayyena magana tukunna gaba da gaba yayyenmu suka ce su baza suyi min kayan daki ba don basu sani cikin lissafin kannensu wadanda zasuyiwa kayan daki ba.

Mamana har kuka tayi ta kira kanwarta ta sanar mata yadda akayi nan ta kwantar mata da hankali akan zasuyi min komai.

Haka kuwan akayi kannen mamana su sukayi min komai na daki har kitchen, lokacin da aka kawo kayan lefena kaf mahassada na saida suka rude don kaya ne nagani na fada wanda akeyiwa y'ar gata.

Nan aka fara zagin Aunty murja wai da ita aka hada baki aka nemomin miji mai kudi ankawo lefen da babu wacce aka taba kawowa irin shi a gidan.

Nan fa suka yi fada uwaka ubanka ita da su ta tona musu asiri tsaf

"Duk hakkin yarinyar nan da kukasa na dauka bai yi muku ba so kukeyi bikin ta ma na nuna mata bakin hali to wallahi baku isa ba daman don ban san halinku bane amman yanzun anyi walkiya na ganku munafukai kawai mahassada wallahi sai na tona muku asiri na fadi duk abinda kuke fada min tsaf"

Lokacin biki yazo akaje ganin gidan Amare gidana yafi na yayarmu wadda za'a yimana aure tare kyau nan suka tuburewa mijin dole irin gidana zaiyi hakan yasa zancen auren ya watse aka fasa don shi bashi da kudin Ahmad don Ahmad iyayenshi ma masu kudine ballantana shi kanshi.

Nan fa maganar aurnta ya watse aka mai da masa kudin shi akayi nawa bikin ni kadai.

Munyi walima da yini don ba wasu kawaye gareni ba sai aboka nan karatu na Da Aunty murja akayi hidimar nan har da hawayenta tana bani hakuri tare da fada min duk abinda aka dhirya min Nace,

"Aunty ki daina damun kanki don komai ya wuce a gurina don kin tallafeni kika bani gurin zama har nayi karatuna na gama ba abinda zance miki sai godiya"

Haka dai daga mun kebe Aunty murja zata ta bsni hakuri har abin ya fara damuna na fadawa mamana tayi mata magana ni komai ya wuce bana son yawan bani hakuri da takeyi

Mamanmu ta kirata tayi mata magana tare da nuna mata mun riga mun zama daya yanzun.

Aka mikani gidan Angona kuma masoyina Ahmad ina kukan rabuwa da y'an uwana da kuma mahassada na domin na riga nayi imanin hassada ga mai rabo taki ce.

Bayan y'an kawo amarya sun watse aka barni ni kadai inata share kwallah cikin farin mayafin da aka rufe min fuska,

Can na jiyo zazzakar muryar angona yana yimin sallama na amsa a sanyaye ya karaso bakin gadon yana doka murmushi bakinshi yaki rufuwa yace,

"Alhamdulullahi the game is over now you are my wife my halal thank you god"

Ni dai shiru nayi ina raba idanu a cikin mayafin domin ina tare da tsoron nan irin na amare😉

Ya yayemin mayafin yana kallon fuskata cike da shauki farin ciki yana kara mamaye shi a yau gashi ya mallaki sarauniyar zuciyarshi.

Ya umarceni da na taso nayi alwala mukayi alwala tare da yin nafila raka'a biyu ya dafa goshina yayi min addu'a sannan ya fara jefomin tambayoyi game da addini na tsaf na amsa masa.

Sannan ya gabatar min da kazar amarci tare da freshmilk, girgiza kai nayi aikuwa take ya hade rai yadebo ya nufo bakina da shi a kunyace na bude bakina na amsa tare da taunawa a nutse.

_Maman nurul huda ya da hadiyar miyau kuma mu da muke dauko labari ko so kike a ganmu ? Ta harareni tace, Lallaima Maman ihsan din nan nasan ko kema ranki ya biya da kazar nan kallifa ko kashi babu a cikin ta tsoka zallah lol_ 😂

Bayan ya gama ciyar dani sai shima ya ci a hankali na zame na nufi dakina nayi wanka na dauko kayan barci nasa riga da wando iya gwiwa saboda tsaro na kwanta saboda ina tare da gajiya

_wai ita wayo safiya kenan🤭_

Can cikin barci na ji an rungumeni sosai kamar zai maidani ciki dif nayi kirjina yana dakan uku uku don tsoro a hankali ya ringa yawo da hannun shi a sassan jikina tuni notikan jikina suka kunce don sun fara amsar sakonnin shi.

Saida naga ana neman ciremin security sannan na nemi hanawa amman habibty yace bai san zancen ba dole na hakura ina y'an hawayen wahala da farin ciki Ahmad yayi nasarar mai da ni cikakkiyar mace,

Na sha wahala sosai shi kuma yasha sun batunshi don bazan iya lissafa alkawarurrukanshi ba da kuma shi min albarka da akayi tare da ambatar inasonki matata.

_Toh y'an mata sai a kula a rike mutunci domin budurcin ki mutuncin ki naga wani post yana yawo a media wai babu budurci mazan hausawa fyade suke yiwa mata shi yasa to wallahi karya ne zancen nan sai dai ko wacce macce da yanayin halittatta wata jini na zuba yayin fitar yanar budurci wata kuma babu jini amman mijin ta zai san budurwa ce wallahi babu maganin matan da zai dawo miki da budurcinki don haka kar kwadayi ya kaiki ya baro_

*Nasiha ce daga maman ihsan*

Bayan komai ya lafa barci ya kwashe ni hakan yasa yaja blanket ya lullubemu shi kam dakyar yayi barci don farin ciki, domin lokacin da yake neman aurena ansha tarar shi ace masa bin maza nake yi.

Tausayina ne ya cika shi sosai ya kuma dau damarar duk wanda ya kuma aibatani sai inda karfinshi ya kare.

Fans ku kawo ruwan zafi mu taya Ahmad gashin sahibar shi💃🏻

Daga Alkalumman:
Maman nurul huda👄
and
Maman ihsan😍
[7/12, 12:12 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH*

*True life story*

Story by : Maman Nurul Huda👄

Written by: Maman Ihsan😍

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM !

🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟

🌟G. W. F🌟

Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest.

Page 37/38

*Barka da juma'a y'an uwa Allah ya Hadamu da Alkhairin wannan rana Ameen*

⬅🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Sosai Ahmad yayi ta tattalina tamkar kwai ni ko ina zuba shagwabata son raina ina kuma kara godewa Allah akan ni'imar miji na gari da ya bani.

Bayan wata hudu wasu barayi suka shiga gidana suka sacemin kayan lefena kaf,mutane suka yita zuwa gurin yi min jaje amman y'an ubana ko sau daya basu tako gidana ba sai rade raden magana naji wai suna ta cewa Allah ya kara ba ina ta murna na samu miji mai kudi ba.

Sai da naje gida sannan suka tasa ni da tambayar wai sunji anyi min sata nace musu eh,

Wasu sukace "Allah ya kyauta" wasu sukace "uhmm" ni dai ban kulasu ba don nasan hassa da ce take cin su.

Na samu farin ciki a gidan aure na wanda a da bantaba tunanin samu ba babu abinda na nema na rasa komai mijina ya tsaya min don har mota ya siya min kaya kuwan mahassada na sai dai su gani a jikina suyita bakin ciki.

*NASIHA DAGA SAFIYA*

Yaku y'an uwana musulmai ina mai fatan kun karu da darussan da ke cikin rayuwata kuma zakuyi amfani da shi.

Idan zama ya hadaka da mutum kar kayi masa hassada acikin al amuran rayuwar shi ka rayu da shi da zuciya daya domin duk wanda kayi wa hassada karshe shine a sama kai kuma a kasa kaga kenan tamkar ka zuba masa taki ne a gonar rayuwar shi, idan ka kalli labarin rayuwa ta zaka fahimci hakan yadda y'an ubana suke nunamin y'an ubanci a fili da badini kuma gashi duk cikin su na fisu dace da miji na gari kuma mai arzikin da zai daukemin dukkan bukatuna.

Sannan kira ga iyaye da ma y'an uwa wadanda da zarar an sanar dasu magana zasu hau su zauna akai ba tare da sunyi bincike ba sai dai kawai su shiga yanke hukunci idan kika duba mamana da kuma Aunty murja a zahiri da badini su din masoyana ne amman makirai da magulmata sune suka shiga tsakanin mu wanda yanxun zance Alhamdulillah tunda sun ajiye dukkan dabi ar daukar zuga a gefe pls jama'a idan aka kawo muku zance ku danne zuciyar ku kuyi bincike sannan kafin hukunci.

A yanzun bani da abokiyar shawara bayan Aunty murja domin duk sirrina itace haka itama mun koma tamkar uwa daya uba daya.

Haka ban garen mamana da y'an uwana wadanda muke uwa daya komai ya dai daita a tsakanin mu.

Amman y'an ubana har yau sunki saduda don har yanzun basu bar yi min hasssada ba kuma kullum ni ce a sama.

Anan zan tsaya da baku tarihin rayuwata ina fatan zaku amfana da sakon da yake ciki.

Toh safiya mun gode da labarin rayuwarki da kika mika mana domin isar dashi ga Al umma ina mai godiya ga Allah da ya bani ikon sauke wannan nauyin fata Allah yasa mu amfana da darussan da yake cikin rayuwarki a madadin daukacin y'an Gorgeous writer forum da sauran fans muna miki fatan Alkhairi a rayuwarki ta gaba na barki lafiya.

*Alhamdulillah*

Daga Alkalumman :
Maman nurul huda👄
And
Maman ihsan😍

Please share masu rowar comment yau dai na kar kare muku buk din 🤪masu comment ana mugun tare😘

Maman nurul huda 👄
And
Maman ihsan😍

Love you fans
Chapter 12 · 0% Book details