← Book details Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 16

Sashe 8

Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau akayi sadakar bakwai na tsohuwa har mutane zasu watse ,alhaji wato mahaifin Zaiyyan ya kalli baba dake zaune yace "dama yau juma'a inason a É—aura auran Zaiyyan da Rahma "cike da farinciki mutanen gurin suma amince hatta shi baban yaji daÉ—i sosai sbda burin mahaifiyarsa kenan kuma an cika mata shi , cikin ikon Allah aka fara shirye shiryen aure ,dama mutane na kusa dana nesa sun halarci gurin taron ,aka biya dukiyar aure cikin ikon Allah aka É—aura auran Zaiyyan da Rahma akan sadaki mafi albarka dubu hamsin .

A take a gurin alhaji yace "bama buƙatar komai daga gurinku dama munata yi masa shirye shiryen aure to wacce yake son ma ba sonsa take ba ,jiya tazo har gida taci mana mutunci ,mun gama kayan aure har gidan ma duk an kammala gyara sa gobe insha Allah sai kawo amarya "kowa ya tashi da tsananin farinciki baba ko baki yaƙi rufuwa haka ya shigo gidan ya dami ƴan uwansa mata da suka zo yake sanar musu da Lami , duk sunyi farinciki Ramu dake rakuɓe a gefe sai binsu take da ido ta miƙe ta fice , tana fita taga dandalin sa'aninta a ciki ,ƙawarta mai suna Khadija tace "shikenan Ramu gobe sai gidan miji "dariya Ramu tayi kana tace "ni so nake ma ana kaini wllh in dafa shinkafa da miya mudu ɗaya in cinye ni kaɗai ,tunda nake ban taɓa ƙoshi da shinkafa a gidanmu ba in kunga abin da naci na ƙoshi sai dai tuwo "dariya suka sa wata a gefe tace "shikenan zaki dinga kwana a bayan ƙato 😂"Ramu tasa dariya tace "ke ai ba ɗakinmu ɗaya dashi ba ,kin mance abin da malam yace "?dariya suka saka dukkansu tare da cewa "wa gaya Ramu da ciki "Ramu ta hau shure shure tace " ai bazai naje naci dankali ba shine cikin mutum yake ƙato ai "daga nan dai ko wacce tayi gida Ramu ma tayi gidansu .

Zaiyyan da yaji wanan maganar ta auransa ya tsorata ,sbda a inda yake da wanan rayuwar tasa yana ganin Ramu tayi masa yarinya ace NIDA YARINYA zanyi rayuwa ?wlh zan cuceta ko kuma ta cutar dani....!

Afuwan fans yauma babu yawa fa 😂naga comments a grps grps ina godiya insha Allah na gobe sai ya baku mamaki 😍.

Tofa ga littafin daya doke na NIDA yarinya daɗi ,sunsn littafin MACEN SIRRIN  kunsan akwai cakwakiya fa ,duk wanda ya nuna min soyayya ta  hanyar siyan littafina bazaiyi nadama ba ,littafan guda biyu ne ,da ƳAR DAMFARA da kuma MACEN SIRRI .

MACEN SIRRI 300 Vip 500
ƳAR DAMFARA 300 tabbas inason ganin yawanku masoyana karku manta akwai cakwakiya ,littafan zasu fara zuwar muku idan har akayi rabin payments wayo biya .
Domin neman karin bayani 08141799224  abari ya huce duk wacce bata karantaba ina tayata da jimami aradu 😂.

Mom Islam
[29/01, 10:12 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

    *NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib/Mom islam_

P 11-12

Washe gari bayan anyi sallahar asbha ,iyaye suka duƙufa aikace -aikacen biki , Lami kam komai ya cukurkuɗe mata sbda babu abin data siya duk da ance iya amaryar ake buƙata amma ai gara dai ace akwai nata ,zuwa ƙarfe tara maƙota sun shigo aka fara yanke yanken kabeji dasu karas da sauransu , masu ɗora tukunya nayi masu gyara shinkafa nayi , amarya kam Lami ta kaɗata gidan wata mata ana ce mata Hajiya Nafisa , Hajiya Nafisa gogaggiyar yar duniya ce sana'arta shine sai da magungunan mata  a garuruwa da dama , kasancewar ta fara manyanta yasata dena yawo amma ana zuwa gida ana siya , kuma ƙawar Lami ce sosai , shiyasa ta turo Ramu , tunda Ramu tazo gidan ake dirka mata saiwoyi na tsarki daban na tsugunno daban ga ɓarin turaruka da hajiyar take mata , koda Lami ta shigo ɗazu da safe tace "ayi mata na dai-dai kuɗi "Hajiyar tace "wanan aiki na ne ai ƴata ce bana buƙatar ko sisinki abu namu ai zakisha mamaki inhar ji da ita ne tofa an gama dole ta shige ransa babu boka ba malam , amma bana son sanar da ita rayuwar aure da wuru sbda tana da ƙarancin shekaru tabbas zata iya zaƙewa a waurarta "tafawa sukayi da Lami tace "baki da dama hajiya , Lami ta koma zuciyarta cike da farinciki .

Ramu tayi haske duk da iya yau aka fara amma ta dirxu hhh harda su emergency aka bata wai duk dan ta rikita Zaiyyan ,

Ƙarfe bakwai na dare aka kawo kayan akwatuna,  ƙanwar Lami tace "abun da akayishi na gaggawa har da yin akwati ?yayar Hajiyar Zaiyyan tace "ai sun rigada sun gama haɗawa tun sati uku da suka wuce Allah dai yayi rabonta ne "akwatunan da suka shigo dashi wajen guda bakwai ne ko wanne shaƙe yake da kaya na birgewa ,ganin akwatunan mutum yayi yamasan kayan cikin bana kushewa bane .
Zuwa ƙarfe takwasa da rabi iyayen ango suka wuce bayan iyayen amarya sunyi sallama aka turo ɗaukar amarya , zuwa gidan Hajiya Nafisa akayi aka ɗaukota aka sanyata a mota tana kuka Lami na kuka haka suka rabu , kasancewar gidan daga nan akwai nisa sosai dan zaiyi naira saba'in idan mutum zashi ,daga gidan tsohuwa yafi kusa .

Kasancewar gudu suka sharara yasa su isowa da wuri suka iso ɗan gidan nashi madai daici gunin sha'awa ,gidan yasha fenti ga tangamemen get baƙi , mai gadi ne ya buɗe musu suka shiga tare parking a gefe , dama motocin guda hudu ne  , fito da amarya akayi sauran ƴan uwa ma suka fito ,aka kama hannun amarya aka shiga da ita ciki kai tsaye ɗakinta aka kaita aka zaunar da ita a kan bed , ƴan nasihohi akayi mata masu shiga jiki kana aka fara hidimar tafiya gida , tunda Ramu taga an fara shirin tafiya take rera kuka har da kamar zata shiɗe ,kwalliyar fuskarta ma duk ta dame , haka Hajiya Nafisa tace "ku tafi zan biyo motar haya in dawo "to sukace aka tafi aka bar Hajiya Nafisa da Ramu , abinka da yarinta Ramu ta ɗauka hajiyan zata zauna ne har tana sakin ji ,hajiya Nafisa tace "Rahma inaso ki zamo mai kunya da jan aji yanzu dai tashi muje toilet kinji "miƙewa Ramu tayi suka shiga toilet ta haɗa mata ruwan wanka ta ɗibo wasu turaruka masu ƙamshin gaske kuma masu tafiya da hankalin wanda ya shaƙesu ,rufo mata ƙofa Hajiya Nafisa tayi ta buɗe jakarta ta ciro wani riga da wando mai bala'in kyau rigar pink wandon black sai hular kayan itama black ,rigar ta matse daga ƙirjinta daga ƙasa kuma ta buɗe ,wandon ma haka daga sama har gurin cinyoyinta ya matse daga ƙasa ya buɗe dama Allah ya yalwata Ramu da hips da boobs babu laifi .

Tana gama wanka ta É—auki towel ta share jikinta ta fito É—aure da towel wanda ya rufe mata har cinya ,zama tayi a kan bed Hajiya Nafisa tace "É—auki wanan man ki shafa "babu musu ta É—auka ta shafa hajiyan tayi mata kwalliya ta bata kayan tasa .
Suna haka har ƙarfe goma tayi lokacin Ramu ta gama sauya kaya tayi kyau sosai ,Hajiya ta ɗauki jakarta tare da ajiye mata wani turare a kan mudubi tace "wanan duk lokacin da zaki kwanta zaki dinga shafawa ki kula sosai kinji ni zan tafi kiyi ta haƙuri "hajiya bata tsaya jin mai Ramu zatace ba ta fice tana fita ta haɗu da Zaiyyan shi da abokansa a jikin motarsu ,gaisheta sukayi kana ɗaya daga cikin abokan yace "ta shiga ya kaita gida , babu musu ta shiga suka tafi .
Chapter 8 · 0% Book details