← Book details Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaban Ramu ne ya bada rass ,tsohuwa dake tsaye hankali a tashe tace "ni anya ma kinci abinci kuwa ?dan nasan Lami muguwa ce "Ramu dake raba idanu ta kalli likita tace "kawo kunnenka in faɗa maka wani abu "ɗan hararata yayi kana yace "ke inada abinyi fa ba wasa nazoyi ba "riƙe ciki Ramu tayi zata dararar ihu tsohuwa tace "haba likita kayi mata a hankali ta jigata ka tsaya kaji mai zatace "likita da yaga hankalin tsohuwa ya mugun tashi ya sashi matso da kunnensa dai-dai saitin ta ,Ramu tace "nama naci wlh shine ya sani gudawa ,dan girman iyayenka karka faɗawa tsohuwa wlh zata yimin dukan mutuwa "likita daya jinjina kai tare da ɗagowa yaga babu tsohuwa a gurin yace "ina tayi ?Ramu da ta ɗago kai itama tace "oho "ganinta sukayi ta fito hannunta riƙe da kofin silba mai murfi ta miƙawa likita tace "gashi ai gani nayi kun dace da Ramu insha Allah ka sami matar aure "likita bai san lokacin daya ɓarar da ruwan bunun dake cikin kofin ba duk da zafinsa bai hanashi bawa tsohuwa amsa ba yace "ba amin ba wlh ,da nasan abin da zan tarar a gidannan kenan wlh da ban zo ba "Ramu ko duk daɗi ya suka haɗa ido da likita tayi masa murmushi ,likita dayaga ana neman ɓatar masa da hankali yace "zan tafi shago anata jirana tsohuwa kizo ki karɓi magani "tsohuwa da ta saki baki ganin yayi mata ɓarin ruwan shayi gashi yazo da abin gwaji bai gwada Ramun ba ,ya sata cakumo gaban rigarsa tace "mutuwa kakeson tayi ?likita dake shirin tafiya babu hali yace "dan Allah ki sakeni inada tarin aiyuka a gabana "sakeshi tsohuwa tayi kana tace "ni da nasan asalinku ,dan dai zumuncin yanzu daya zamo abin wasa ne amma da kakarka da tawa uwa ɗaya uba ɗaya kuma zani gidanku yau in tabbatar maka mu danginku me ,haka mahaifinka ƙani ne a gurina auran zumunci akayi musu da mahaifiyarka "ba tare da ya tsaya jin surutun nata da take ko haɗiyar miyau batayi ya fice da sauri ,yana cewa "Allah ya kuɓutar dani kaji wai in auri wanan yarinyar "yarinyar da kwata-kwata shekararta bai fi sha huɗu ba wlh an cuceni "yana komawa kemis mutane suka fara yi masa masifa akan ya biyewa tsohuwa sun tafi gashi  bai dawo da wuri ba ,ci gaba yayi da harkokin gabansa ba tare da ya basu amsa ba dan yasan yayi laifi .

Likita na fita Ramu tace "tsohuwa nima ina sonshi "murmishi tsohuwa tayi da bakinta da yake ɗan lomawa alamar wasu haƙwaran sun fice tace "ai banga uban da zai hana wanan auren ba ,dan nima ƴar uwarsu ce ,bari idan kika ƙara samun sauƙi zuwa jibi zani gidan kici kwaliya kinji ?"har Ramu na tsalle kamar ba itace mai ciwo ba tace "to "riƙe mata hannu tsohuwa tayi suka wuce ɗaki domin karyawa.

GIDAN SU SAIDAT
Saudat nata murna yau Abdull zai dawo kuma ya faɗa mata zuwan dare zaiyi , tana daga ɗaki misalin ƙarfe sha biyu na rana 12:pm taji yaro yayi sallama ,ƙin amsawa tayi sbda ta ɗauka tela ne ya aikoshi , Umma dake tsakar gida ta amsa tare da cewa "ya maman naka ?lafiya lau yaron yace "wai ga kuɗin adashi , to Umma tace "ta ciro naira goma taba yaron yace "yasi alewa "godiya yayi mata ya fice .
Saudat naji ance kuɗin adashi ta buɗe ragar wundonta tana taya Umma ƙirgar kuɗi , Umma dake shirin tashi ta shiga ɗaki tace "wai ashe mutane sun daɗu kuɗin har yakai dubu goma ?Saudat tai tsalle a fili tace "hhh anjima zan aresu kafin Abdull yazo ya bani.
Umma na zaune a inda take tun ɗazu bata tashi ba ,dan kuɗin ma a cikin kwanon gabanta ta ajiye , Saudat ta fito da ɗaurin ƙirji tace "Umma akwai ruwan zafi ne ?"eh Umma tace "ɗibi na waccar tukunyar "bayan Saudat ta ɗauko bokiti ta ɗiba ta shige wanka ,kasancewar sosonta da sabulu a leda suke ta maƙaleshi da hannunta , ta daɗe tana cuɗa jikinta daga ƙarshe ta kwara ruwan ta fito , samun Umma ta shiga ɗaki tayi itama tayi nata ɗakin , bayan ta shiga ɗakinta ta janyo jakar kayan kwaliyarta tana shafa mai ,tana shirin shafa hoda ne taji Umma ta fito tana ce mata  "Saudat zani gidan mai adashin nan inji inda akayi dan Allah karki bari awakan nan su shigarmin ɗaki ,keda idan kika shige ɗaki kamar bakya gidan "to Saudat tace "tana dariya ƙasa-ƙasa tasan kafin Umma ta dawo ta riga da ta fice a gidan, da sauri-sauri ta shirya ta sanya leshinta baƙi mai adon fulawa ruwan tasa tare da sarƙa da ɗankunne ,kasancewarta wankan tarwaɗa bata cika fari sosai ba ya sanya kayan yi mata kyau , yau kam haɗa sallah zanyi Saudat ta faɗa tana juyi sbda ita kanta tasan tayi kyau (niko nace mai yasa bakiyi alwalar tun kafin ki fara kwaliyar ba ,dan wanan kuskure ne babba).

Tana gamawa ta fito hannunta riƙe da wayarta ,kai tsaye ɗakin Umma ta shiga ta fara dube -duben inda kuɗin suke , har ta fitar da rai da ganinsu tana ɗaga filo taga kuɗaɗen a nannaɗe ta zari dubu biyar tabar dubu biyar ta fice tare da saƙalo ƙofar gidan , ƙasan anguwarsu ta gangara naga ta tsaya a wani ƙofar gida tare da danna wata number , rin ɗaya aka ɗauka Saudat tace "Karima kina gida kuwa ?lalle zakiyimin "wacce aka ambata tace "wlh nayi tafiya ina Kaduna anyi mana rasuwa "cikin rashin jin daɗi Saudat tace "ayya Allah yaji ƙan rai Allah kuma ya dawo dake ɗafiya "amin Karima tace "Saudat ta juya ta nufi shagon mai ɗinkin ta , tana zuwa ta samesa   yana aikin nasa wato ɗinki , yana ganinta ya washe baki tare da cewa "hajjaju kenan kina wuta,sallama Saudat tayi ta shiga cikin shagon tace "afuwan Habu wlh ba haka naso ba kasan gari yaci wuta "Habu na dariya yace "ai nayita aiken yaro wai baki da lafiya "cikin alamun rashin gaskiya Saudat tace "am eh wlh zazzaɓi ne "mai ɗinki yace "Allah ya ƙara lafiya "Saudat tace "amin.

Neman guri tayi kan kujerar dake gefe ta ɗinki ta zauna tare da buɗe ƴar jakarta ƴar mitsi tsiya ba lallai kasan tana tare da ita ba ,ta ciro dubu biyar ɗin hannunta ta miƙa masa ,tela yace "to ai ni dubu huɗu zakibani "Saudat tace "kayimin kirarin da nake mutuwar so shiyasa na baka kyauta "Habu tela yasa dariya yace "tabbas zanyi tayi inci gaba da samun kuɗi a gurin matar governor  Allah yasa mafarkin da nayi jiya ya tabbata "Saudat na dariya tace "amin nagode "tayi masa sai anjima
Hanyar gidansu ta nufa dan tama mance da ta ɗauki kuɗi a ɗakin Umma ta shiga da sallama kamar anyi mata albishir da gidan aljannah tana shiga tace "Ummana yau ina cikin farinciki "Umma dake rataye mayafinta a bakin ƙofa tace "to mai yafaru ne ? Saudat tace "anyi min kirari sosai "dan karta gwaleta Umma tace "kaga matar gwamna "tsalle Saudat ta doka tana murna .

Zuwa yamma wajen ƙarfe bakwai ,Saudat ta sake yin wanka tare da yin sallah tayi kwaliya wacce tafi ta ɗazu ta feshe jikinta da turare masu ƙamshi , ɗakin Umma ta nufa ta sami Umma na rabon abinci tace "Umma yau Abdull zai zo kuma yace "daga wanan zuwan sai maganar auranmu "cikin farinciki Umma tace "to ki zuba shinkafa da miya ko zai shigo "yamutsa fuska Saudat tayi kana tace "kalan ya raina mana wayo miya babu ko nama a ciki "Umma da abin ya bata mamaki taja baki tayi shiru ba tare da ta ƙara cewa "uffan ba , ƙarfe takwas wayarta ta fara ring , babu ko jan ajin nan ta ɗauka da sauri har hannunta na rawa tace "babyna har ka iso ?"  sai kuma ta fice zuwa ɗakinta.
Chapter 5 · 0% Book details