← Book details Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saudat na shiga gida ta sami Ummanta na tuƙa tuwo , tsaki tayi kana tace "kullum tuwo kullum tuwo wlh dole ciwo ya dinga kama mutane ,ayi abin arziƙi baza'ayi ba sai tuwo "zaro ido Umman tayi tare da cewa "gidanku nace , anyi miki dole kici ?to tun wuri ki rufamin baki "Saudat na tafe tana bubuga ƙafa ta shige ɗakinta dake ɗake ɗauke da tabarma babu katifa sai tulin tsummokara tai tsaki ,ta nemi kujara ƴar tsugunno dake gefe ta zauna tare da rafka tagumi tace "ni Saudatu na shiga uku ,mai zan cewa Habu tela oho ,ya bani bashin kaya gashi nayi masa alƙawari "faskekiyar wayarta ta ciro infinix hot 10 ta nemo number Abdull ring ɗaya ya ɗauka tare da sallama , cikin rage sautin muryata tace "babyna ka isa gida lafiya ? Abdul dake zaune a makeken palon su ya amsa da cewa "eh har na huta ma ga hajiyata ku gaisa "miƙawa mahaifiyar tasa wayar yayi ,hajiya ta ƙarɓa ta kara a kunnenta tare da cewa "ƴata ya gida ya sanyi "lafiya lau Saudat tace "ta kuma gaisheta sukayi sallama , tare da taɓe baki hajiya ta miƙawa Abdull waya ta miƙe tabar gurin , baki sake yake kallon hajiya har ta ɓace wa ganinsa ,sanan ya nunfasa tare da miƙewa ya wuce bedroom ɗinsa , zama yayi kan bed tare da cusa hannunsa cikin yalwataccen sumar kansa yana huci , a fili yace "nasani tabbas akwai gagarumin matsala a gabana ,hajiya bazata amince da auran Saudat ba sbda dalilin da bazan iya amincewa dashi ba , gagararsa zaman yayi ya miƙe tsaye yana zagaye ɗakin hannunsa na haɗe ta baya yana lanƙwasasu suna ƙara ,wata dattijiwa ce ta bankaɗo ƙofa cikin zafin rai tace "Abdull gobe zaka koma egypt wlh gara zamanka a can da tayar mana da habkalin da kakeyi ,wanan wace irin rayuwa ce minyi maka zaɓi tun kana ƙarami amma yanzu wuyanka ya isa yanka shine kake neman bijire mana ko ?"ran Abdull yakai ƙololuwa gurin ɓaci sbda ji yake kamar ya ɗora hannu a kai yana tsala ihu ko ransa zai yi masa daɗi , yana jin daya auri Fati gara ya zauna baiyi aure ba , sbda abubuwan da ya taɓa gani ido da ido har yanzu ya kasa ɓace masa ,wanan shine ruwa biyun tabbas ta zamo (zulwaja haini) ,dattijuwar dake tsaye tana balbala masa masifa , sai da ta gaji sanan tayi shiru tana jiran abin da zai ce , kusam mintuna wajen goma Abdull bai yi magana ba ,can kuma ya juyo ya fuskanci dattijuwar yace "Anti Ummi bance muku bana son Fati ba "nidai ku barni in auri wacce nakeso "au iyee ma ,ni zaka kalla kace wani wai inbarka ka auri.. to ka daɗe baka mutu ba ,aure babu fashi nan da sati biyu kai nan da kwana goma ma wlh auranka da Fati ya ɗauru "cikin matsanancin firgici Abdull ya kalli Anty Ummi dake faman sababi yace "anty kiyi haƙuri ki...,ficewa daga ɗakin tayi ba tare da ta kuma sauraronsa ba tace "sauran shawar wari ya rage gareka Abdullahi.
Tashin hankali iya tashin Hankali Abdull ya shiga har ma yake jin inama mahaifinsa na raye babu wanda ya isa yayi masa haka.

Ganin zaman da yayi ba shine mafita a garesa ba yasa shi miƙewa ya shiga toilet ,ruwan sanyi ya sakarwa kansa kasancewar garin da zafi ,tunda ruwan ya fara sauka a jikinsa ya lumshe ido hoton fuskar Fati yake gani da abinda ta aikata runtse idonsa yayi yana mai cewa "wlh an cuceni "lokaci ɗaya kuma ya kashe shower ɗin ya ɗaura tawul ya fito , zama yayi a kan gadonsa yana lanƙwsa hannayensa , jiyo rurin wayarsa da yayi ne ya sanyashi miƙewa a hankali ya isa kan tebur ɗin da wayar take , Sis Fatima ,sunan da yayi saving number ta kenan a wayarsa ya gani , ɗagawa yayi tare da kara wayar a kunnensa yace "ina jinki "Fati dake zaune a gurin cin abinci ta ajiye cokalin dake hannunta cikin siririyar muryarta mai ɗaukar hankali tace "brother na da fatan ka wuni lafiya ?"cike da miskilanci ya fara magana kamar an shaƙesa yace "Tima kizo gidanmu akwai maganar da zamuyi "cikin jin daɗi ta miƙe tare da ture kujerar data tashi a kai ta wuce gurin biyan kuɗi ta biya tabar gurin , motarta dake pake a gaban gurin cin abincin ta shiga tare da yi mata key tabar gurin , tuƙi take tana tunani iri-iri ,ta wani ɓangaren hankalinta na titi a fili tace "Allah yasa kalmar dana daɗe ina tsumayi zai faɗamin da wlh yau bacci sai Allah "tana isowa bakin tangamemen get ɗin gidan tayi horn mai gadi dake zaune ya leƙo tare ɗaga mata hannu ya buɗe ta shige , kai tsaye gurin ajiye motoci ta nufa tana ajiyewa ta wuce side ɗin su Abdull , Anty Ummi ta samu a palo sai hajiyarsa , har ƙasa ta tsuguna ta gaishesu kana ta koma kan kujera ta zauna , murmishi anty Ummi tayi kana tace "Fati ai mutumin naki yana ciki "cikin jin kunya fati tayi murmishi tare da miƙewa tace "shine ma ya kirani a waya "sai tayi gaba .

Anty Ummi ce ta kalli Hajiya tace "kinga munafukin yaro yana so yana kaiwa kasuwa ko ?"uhm ai yaranan sai Allah nifa dama nasan yana sonta gulmace kawai "Hajiya ta faÉ—a tana turo É—aurin É—ankwali gaba .

Fati na shiga ta tarar da Abdul zaune a palonsa hannunsa riƙe da kofi mai ɗauke da lemun karas , yana sha yana juya kofin ..

Uwar gida ga yadda zaki haÉ—a lemun karas da kanki .

ABUBUWAN HAÆŠAWA

Karas
Citta
Sugar
Flavour

Da farko zaki wanke karas ɗinki ya wanku sai ki yanka karas ɗinki ƙana na ,ki markaɗashi a blanda sai ki wanke cittarki ki yanka ƙanana ki markaɗata a balanda tare da karas ɗinki , sanan ki tace kisa sugar da flavor sai kisa a frij yayi sanyi sosai , karas yana da amfani musamman ga lafiyar ido ma.

Sallama tayi a hankali kamar ba ita ce ta shigo da kuzarinta ba ,amsawa Abdull yayi tare da ɗago kai ya kalleta ,kallon shigar da tayi yayi riga da wando ne a jikinta na jins sai t-shet mai ruwan ƙwai tanada adon duwatsu a jiki ,a zuciyarsa yace "mtsew wanan rashin ɗa'ar har ina ?sai kuma ya nuno mata kusa dashi yace "ta zauna , zama tayi tare da kwantar da kanta a cinyarsa , cikin sairi ya ɗagata tare da cewa "bana son raini fa "muyi abinda ke gabanmu "kallonsa tayi da fararen idanunta alamar tana jinsa ,Abdull dake kallonta yace "dama abin da nakeson faɗa miki shine kicewa anty Ummi bakya sona "wani rass gabanta ya bada ta miƙe tsaye da sauri tare da cewa "na shiga uku brother dama kiran da kayi min kenan ?"cikin nutsuwa yake kallonta yace "eh sbda bana son ayi mana auran dole ke bakice kina sona ba nima bance ina sonki ba so mu yanke hukunci tun kafin a cutar da zuciyoyin mu "ido waje Fati ke kallon Abdull a zuciyarta tace "wai bana sonsa ?"sai kuma tayi murmishin yaƙe tace "babu damuwa yayana indai dan wanan ne zan faɗa musu insha Allah ta juya ta fice zuciyarta kamar an sheƙa mata ruwan zafi ,har ta kawo palo batasan tazo ba sbda tuƙuƙi da zuciyarta keyi , Anty Ummi dake zaune tana jiran fitowarta ta miƙe da sauri ta dafa kafaɗar Fati tace "ya akayi ne Fatima ?"murmishi ta gayyato ya ziyarci fuskarta kana tace "wlh lafiya anty "mai Abdull ɗin yace "miki ?"anty Ummi ta jefo mata tambaya ,Fati dake tunanin abin da zatace ta wuce kan sofa ta zauna tare da sauke nunfashi tace "wai wai... Hajiya data fito yanzu itama ta iso gurin anty Ummi tace "mai ke faruwa naji tana ta cewa "wai "a tare suka iso gurinta kamar sun haɗa baki sukace wani abun yayi miki ?"a'a Fati tace "lokaci ɗaya ta tsinci kanta da faɗar abinda zuciyarta keso tace "cemin yayi wai ya daɗe yana sona kuma nice matar da zai aura amma kar in faɗa muku "murmishi ne ya ziyarci fuskar Hajiya da anty Ummi tace "amma naji daɗi ashe Abbdul bazai watsan ƙasa a ido ba "ta ɗaga hannunta sama tana godiya ga Allah , tsabar farinciki Hajiya ta kasa magana ,sai jinjina kai da takeyi alamun daɗi ya kamata , miƙewa Fati tayi ta fice a dole wai kunya ce ta kamata , tana zuwa gurin da ta ajiye motarta ta ciza yatsa tare da cewa "nako shiga uku tabbas nida gidansu Abdull sai an kuma ganina ƙila sai ranar da aka kaini faɗa idan na zamo matarsa , kai tsaye ta shige motarta tana jimamin ɓaran ɓaramar da tayi .

Gidan su Saudat.
Saudatu dake zaune tunanin duniya ya isheta har an kira sallahar magrib tana zaune taji an turo ƙofar ɗakinta , Ummi ce hannunta riƙe da kwanon tuwo da miya ta ajiye gaban Saudat tare da cewa "tunda sallah ta gagareki to kici abinci " rai a ɓace ta kalli tuwon dawar dake gabanta tayi tsaki tare da cewa "nifa bazanci ba wlh da inci gara in kwana da yunwa bakina duk yai ta wari "Ummi bata ce komai ba ta fice tare da barin tuwon a ɗakin ta jayo ƙofa , Umma na fita yaro ya shigo tare da gaishe da Umma yace "wai Saudat na nan ?"eh Umma tace "yaron yace "wai tazo inji Habu tela "Saudat dake ɗaki ta zaro ido kamar an tare ɓera a rami tai sauri ta haye katifarta tana shirin janyo bargo tayi ɓarin miyar kuka , bata tsaya kula miyar ba ta luluɓe jikinta ta fara rawar sanyi , Umma dake waje tace "kai ka shiga tana ciki "to yaron yace "ya kama hanyar zuwa ɗakin Saudat , yana isa ya buɗe labule ya ganta kwance da alamun bata ada lafiya ,bai tsaya kulata ba ya fice , Umma ko sai kallonsa take
[29/01, 10:10 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

    *NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib/Mom islam_

Page 3-4
Chapter 2 · 0% Book details