← Book details Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 16

Sashe 3

Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tasan baya wuce cin bashin taje tayi ,Saudat na jin yaron ya fice ta yunƙura ta miƙe kana tace "Allah ya taimakeni wlh da an ritsani " miƙewa tayi ta fito tsakar gida tare da ɗaukar buta ta shiga bayi ,tare da alwalah ta fito tana shirin shiga ɗakinta babanta ya ƙwala mata kira yana tsaye a bakin ƙofar dakin mamanta , amsawa tayi kana ta nufi inda yake , kanta a sunkuye tace "baba gani "mahaifin nata dake tsaye hannunsa riƙe da redio ya miƙa mata yace "ki ajiyemin a ɗaki "to tace "dan ta ɗauka wani laifin tayi , tana shiga ta sami Umma na sallah ta ajiye ta fito.

Bayan rabuwar Ramu da Saudat bata zarce ko ina ba sai gidansu , tana shiga ta sami Lami tana tuyar waina , dama sana'arta kenan kullum da yamma tana yin mai ƙuli , da rawar jiki Ramu ta ƙarasa tare da kallon  Hajara dake riƙe da ƴar ƙaramar roba ,da alamu talla zata ,hararta Ramu tayi kana tace "Lami ance akai da dubu guda inji wani mai kuɗi "cikin farinciki Lami ta hau sauri har tana ƙonewa ta fara zubawa a wani babban baho   nata sabo ,tanayi tana ƙirgawa har ya kai na dubu ɗaya tasa gyaran guda biyar tace "Ramu ta ɗauka ...

INDA AKE YIN WAINAR FARAR SHINKAFA.

•Farar shinkafa
•Yis
•Sikari
•Gishiri
•Albasa

Da farko zaki wanke shinkafarki ki jikata a markaɗa ,amma ba lallai sai ta jiƙu ba ,sai ki zuba yis da gishiri dai dai misali ,sai a kaɗashi sosai ki sanyashi a rana ya tashi ki yanka albasa ,idan kinaso tayi miki ja tayi kyau zaki iya sanya suga ,sai ki nemi tandar suyan waina ki soya bayan kinsa mai.

Tana fita waje ta dire bahon ta fara kiran yara tana cewa "kowa yazo ya kaɓi ta annabi "dama yara kamar jira suke suka rugo da gudu wanan yana cewa "baki bani ba ,da haka har waina ta ƙare , kowane yaro murna yake yau anyi sadaka abin da basu taɓa gani Lami tayi ba ,Ramu ta ɗauku ɗan bahon data kawo musu waina ta wuce gida ,tana shiga Lami ta fara ɗura mata zagi tare da cewa "dan kutumar ubanki waye ya bani jarin ko ubanki ne ya bani da har zaku fitar min da abin siyarwata kimin sadaka ban san dai-dai bane ?.
Baki sake Ramu ke kallon Lami bata ce komai ba sbda tasan tayi laifi kuma idan sukayi laifi zama take a kansu dan haka ta fice da gudu.

Zuwa dare Lami ta huce da asarar wainar da tayi ,suna zaune a ɗaki , Mariya dake  riƙe da kwanon tuwo a hannunta ta kalli Ramu da ta shigo yanzu tace "Ramu babu miya ki daɗo mana "wata uwar harara Ramu ta galla mata kana tace "kinga nayi kama da sa'arki wlh zanci ubanki "baba daya idar da sallah yana ajiye carbi yace "gara kici ubanta tunda bashi da ƙafar tashi yaci naki uban "Lami dai bata kulasu ba ,sbda lokaci zuwa lokaci tunanin asarar waina yana faɗo mata, sanin yau tun da taga Lami na cije baki inba sa'a ba sai ta duki mutane yasa ta zuwa gurin kayanta ta zauna ,jira take Lami tabar gurin ta fice da kayan ,a cewarta gara gidan tsohuwa dan bata takurawa mutane ,cikin sa'a Lami ta miƙe tana harar baba dake kai lomar tuwo a fili tace "ba'a iya aikin komai ba sai mugun cib,anji kunya ka zauna ka naɗe ƙafa mata ta ciyar dakai "kallonta baba yayi yace "ke Lami iskancinki ya fara yawa fa ,da ban barki kiyi sana'ar ba zakiga dai-dai ne ?Lami na kaɗa ƙugu tace "wlh ka kuma magana sai na zauneka ,kai har kanada bakin yin surutu mtsw" yasan ba ƙaramin aikinta bane hakan ya sashi cewa "yi haƙuri "yaci gaba da cin abincinsa , Lami na fita Ramu tace "baba gidan tsohuwa zan koma "waro ido baba yayi kana yace "zaki janyo mata abin zagi ko ?shigowar Lami ne yasa su yin shiru , Lami ta wuce uwar ɗaki tana ci gaba da mita , sai da ramu ta tattara kayanta duka sai da takai bakin ƙofa tace "wlh baba kishiya zakayiwa Lami haka matar gidan su Bashari ma ta....da gudu Lami ta biyota tana cewa "matar gidan ubanki ce marar hankali ,idan ma anyi min kishiyar kune a wahale wlh banda ina da ku bazanyi sana'a ba "ta koma ciki ta gyarawa su Mariya gurin kwanciya .

Cikin duhu haka take tafiya babu batun tsokana dan babu haske a gari ba'a kawo wuta ba , tana cikin tafiya taci karo da wani abu mai gashi , da farko dai ta tsorata ,cikin sa'a wani yaro yana tafiya da fitila a hannunsa tace "kai haska min "haska mata yayi yaron yana kallon inda take kallo , doll ce irin ta wasan yara ta ɗauka tare da cewa "ungo fitilarka ta ranƙwasheshi ,yaro daya ji zafi yace "shegiya ƴar Lami mai waina "harta zuba da gudu zata bisa ya arce  dawowa tayi taci gaba da tafiya har ta iso gidan tsohuwa ,bubuga ƙofa ta fara tana cewa "tsohuwa nice ramu ki buɗemin "tsohuwa datayi bacci akan sallahaya bata ma san ana buga ƙofa ba , duwatsu Ramu ta tsinto ta dinga wurgasu jikin ƙofar tana ƙwalawa tsohuwa kira ama ina bacci yayi daɗi.
Da Ramu ta gaji da kira ta zagaya baya inda windon ɗakin tsohuwa yake ta, buɗe Allah ya taimaketa a buɗe yake kuma babu abin da ya tare sa zata iya shiga ta ciki , tana shiga ta dira tare da ƴar bebinta  ta rufo wundon ,sai a lokacin tsohuwa taji motsin mutum kasancewar duhu daya gauraye ɗakin  ,tsohuwa na daga kan gadonta mai rumfa murya a hankali tace "dan girman Allah waye ya faɗo min ta wundo ? Ramu da ke kiciniyar lalubo ƙafar tsohuwa ,cikin sa'a ta sami ƙafar ta haɗa da ƴar bebin hannunta ta matse , a zabure tsohuwa ta fara kiran ya hayyu ya ƙaiyumu bi rahamatika astagis , dariya ce ta kuɓucewa Ramu ta sauya murya i'zuwa ta maza tace "adu'ar masu naƙuda ce fa "tsohuwa data kiɗime batajin abin da Ramu ke cewa "sai uban kwararo adu'oi take ,tsawa Ramu ta dakawa tsohuwa da muryar maza tace "ke tsohuwa ina naman da ɗanki ya kawo miki jiya ?jiki na rawa tsohuwa tace "a haska fitila wlh Allah yana nan a ƙasan gado a kwano ɗan caina "murmushin mugunta Ramu tayi kana tace "ki rufe idonki ko kuma in harbeki "sbda tsoro daya gama kama tsohuwa babu shiri ta rufe ido har da sakin fitsari, sakkowa Ramu tayi a hankali ta lalubi aljihunta  sbda bata rabo da fitila irin wacce ake samu a jikin leta ,kunsan haskenta kaɗan ne ,ta haska ta janyo kwanon har ta juya zata dira ,ta dawo da baya tare da kuma dakawa tsohuwa tsawa tace "wlh kika buɗe ido sai nasa an markaɗe min ke anyi man shafawa "dama bata buɗe ido ba har Ramu ta dira ita da kwanon sbda ta mance da ƴar bebinta a ɗakin, tana fita ta zauna a tsakar gida dama garin akwai yawaitar zafi a haka wasu na kwana a waje , bayan ta shimfiɗa tabarmar da take zama idan tazo gidan ta kunna ƴar fitilarta tana haska kwanon ,cikin rashin sa'a murfin ya faɗi ƙasa tasss  tsohuwa na daga ɗaki ta kuma firgita a fili tace "in buɗe idona sun tafi ne ? babu mai bata amsa hakan ya sanyata buɗe ido  tana shirin gyarawa ta zauna kan bebi , jin laushi sosai ya sata kurma ihu tana cewa "Bashir kazo ka taimakeni wlh aljanu a gidannan suna neman ganin bayana "matsawa tayi gefe ta kwanta a takure cike da fargaba .
Ramu kam an sami duniya , tsire ne a cikin kwanon da yawa yaji ƙuli ,ta haɗiyi miyu tare da jefawa baki ,tanajin ihun tsohuwa ta ƙi kulata a zuciyarta tace "maganinki kenan ai tunda ke kinzamo masifaaffiya "taci gaba dacin naman , sai da taji tayi nak sanan taja kwanon gefe ragowar naman bai fi guda uku ba ,tana shirin miƙewa zuwa fitsari taji ana buɗe ƙofa ,tsorone ya kama Ramu sbda tasan inhar tsohuwa tasan itace ta shigo wlh ta mutu ,da gudu Ramu ta shige kicin tare da tsugunawa tana jiran tsohuwa ta wuce ita kuma ta kona ɗakin , tsohuwa da taji alamun motsin mutum ya sata komawa ta danna saƙata tare da janyo po ta tsuguna tayi fitsari ,tana gamawa ta janyo buta tayi tsarki ta koma kan gadonta ta kwanta , Ramu najin tsohuwa ta saka saƙata ta dawo tsakar gida kan tabarma ta kwanta a zuciyarta  tace "ga ƙoshi ga kwanan yunwa wayo Allah na , tana tsaka da tunani bacci ɓarawo yayi gaba da ita .
Chapter 3 · 0% Book details