← Book details Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Nida Yarinya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayafi ta ɗauka ta fice da sauri ta nufi ƙofar gida , tana fita ta gansa tsaye a jikin motarsa ,da murmishi ta ƙarasa inda yake shigar da yayi ba ƙaramin kyau tayi masa ba ji take kamar ta rungumesa , murmishi Abdull yayi yana dariya yace "wanan murmishin duk na farincikin ganina ne ?rufe fuska Saudat tayi da mayafinta tace "ba kayimin rowar zuwa ba sai yau "ah-ah Abdull yace "yana dariya kana yace "to yau ba gashi nazo ba " daga nan suka gaisa Abdull yace "ya su Umma ?"Saudat tace "lafiya lau wlh suna gaisheka "bayan sun ɗan taɓa hira Abdull ya buɗe motarsa ya ɗan shiga , fitowa yayi da bandir ɗin ƴan dubu ɗaya guda biyu , (a tunanina kuɗin zasuyi 100k ya miƙa mata , tsalle ne kawai Saudat batayi  ba tsabar daɗi tayi masa godiya tana kashe masa ido , fuskar Abdull ce ta sauya i'zuwa ɓacin rai kasancewar da hasken wutar lantarki yasa  Saudat kallonsa tace "baby lafiya kuwa ?Abdull ne ya kalleta idanunsa sun kaɗa sunyi jajir yace " mu shiga mota akwai maganar da nakesonyi dake "gabanta ne ya bada rass ,a zuciyarta tace "Allah yasa ba wani abun bane ya faru "shiga gaba yayi ita kuma ta shiga baya Abdull ya rufe ƙofar motar kana ya fara tafiya ,sai da suka kai bakin titi kana yayi tsayar da motar yace "SAUDAT !! a inda ya kira sunanta sai da gabanta yayi mumunan faɗuwa tace "na'am "Abdull yace "nasan kina sona so na tsakanj da Allah nima naso ki zamo matar da zan aure sai kuma Allah baiyi ba ,sakamakon zaɓamin ƴar abokin Abbana da akayi ,kuma a halin da ake ciki ma yau saura kwana bakwai biki "tunda ya fara magana Saudat tayi ɗiff bata ko motsi sbda gabaki ɗaya jikinta ya mutu ga kanta dake sara mata ,ganin batace komai ba yasa Abdull tallafo haɓarta yaji bata nunfashi ,hannunta ya kama yaji tabbas suma tayi , a firgice ya ɗauko ruwan gora ya kwarar mata kasancewar yana da sanyi ta motsa a hankali tana cewa "shikenan Abdull dama yaudarata zakayi ? nagode "zata fice ya riƙo mata hannu yace "haba Saudat ki fahimceni mana ,kamar inda kike sona haka nima nake sonki , ke bakisan halin dana shiga ba akan maganar auran nan ko ?"nidai ina mai baki haƙuri akan dan girman Allah karki ɗaukeni maci amana "Saudat da sai yanzu hawaye ya sami damar zubo mata tace "na yarda tabbas iyaye ba abin wasa bane amma ka sani soyayyarka na cikin raina har abada "kasa magana Abdulla yayi sbda tuƙuƙun da yaji zuciyarsa keyi masa ,daga ƙarshe dai yace "Saudat ina yi miki fatan alkairi dakuma samun miji wanda ya fini "Saudat data koma kamar wata zautacciya ta buɗe murfin motar tace "fatan alkairi zata tafi ya kuma kamo hannunta a karo na biyu ya damƙa mata 50k kuɗin ya koma dubu ɗari da hamsin yace "Allah ya baki wanda ya fini "ba tare data wai wayesa ba ta nufi gidansu tana shiga ta sami babanta a zaune kan tabarma shi da Ummanta , kurma ihu tayi sbda ta kasa samawa kanta nutsuwa dan batayi niyar tonawa kanta asiri ba ,tace "na shiga uku wayo Allah na "baba daya ruɗe ya kalli Saudat yace "lafiya kuwa "Umma ma tambayar da tayi mata kenan , sai da Saudat tayi kuka ya isheta sanan tace "Umma Abdull ya taƙaitani na shiga uku wai anyi masa mata shine ya bani waɗannan shegun kuɗin dubu ɗari da hamsin "zabura Umma tayi tare da dafe ƙirji tace "dubu hamsin kuma ?kai wanan wane irin dukiya garesu ?baba da yayi mutuwar zaune yace "ai ni wanan rabuwa tayi mana rana harda maƙudan kuɗaɗe ?Saudat kam babu magana ganin iyayen nata sun nuna son kuɗin dake hannunta , barinsu tayi a gurin ta shige ɗaki tare da faɗawa kan fale falen katifarta ta kuma fashewa da kuka , gashi bataci abincin dare ba haka ta kwanta bacci ɓarawo ne yayi awon gaba da ita.

Abdull na komawa gida kasancewar kowa da ɗakinsa ya sashi wucewa nasa ɗakin , zama yayi kan haɗaɗɗen gadonsa tare da zuba tagumi ,a fili yace "nayi dana sanin amincewa da auran Fati wlh nayi dana sani "sai kuma ya tashi ya fara zagaye ɗakin yana huci kamar zaki , ya daɗe a haka daga ƙarshe ya kalli agogo ƙarfe goma na dare dai-dai , alwalah yayi yazo ya kwanta tare da adu'a , washe gari da asbha Abdull yayi alwalah ya tafi masallaci ya gabatar da sallah ,ba shi ya fito daga masallaci ba sai ƙarfe bakwai na safiya ,lokacin gari yayi haske sosai , miƙewa yayi daga zaman da yayi ya shafa adu'a sanan ya nufi gidan su  ,yana shiga ya sami Abba da hajiya zaune a palo suna hira ,durƙusawa yayi har ƙasa yace "barka da safiya hajiya "kana ya kalli Abba ma yayi masa barka da safiya , bayan sun amsa ne Abba ya nunawa Abdull gurin zama , zama Abdull yayi tare da jiran zantukan da zasu biyo baya  "Abdull" Abba ya kira sunansa a hankali "na'am "Abdull yace "yana duban Abba ,Abba yace "kasan yau bikinku saura kwana shida ko ?"mudai ta ɓangarenmu an gama komai ,kaima ya kamata ka ƙoƙarta ka kammalah "eh na gama "Abdull yace "jiki a sanyaye ,Hajiya tace "to jeka auta "ya miƙe ya basu guri ransa babu daɗi.

Tsohuwa dai taƙi zuwa karɓo magani kuma likitan yaƙi kawowa ,Ramu tunda taji zancen aure ciwo ya warke.

Washe gari tsohuwa ta gyara gidanta tayi wanka ,tana fitowa ta shafa mai ta ɗauko ƙure adakanta tasa ta yafo gyalenta tare da ɗauko takalmin soson da bata sashi sai zata anguwa ,mudubi ta ɗauka tana kallon fuskarta tace "Ramumu nayi kyau kuwa ?Ramu dake ta ƙunshe baki tana son yin dariya tace "kinyi sosai Allah ya haɗaki da bazawari "turɓune fuska tsohuwa tayi kana tace "ke zanje nemowa saurayi ai garama ki nutsu ,ni zan tafi ki gyara shinkafa ko mai da yaji ki ɗora "to Ramu tace "tare da yiwa tsohuwa Allah ya tsare , tsohuwa na fita Ramu tai tsalle kai tsaye cikin ɗaki ta shige ta buɗe madara ta dinga hambaɗa tare da ɗibar suka , ta haye gado tana dariya sai kuma ta miƙe zaune tace "oh ni Ramatu idan nayi aure sau biyar zan dinga cin abinci a rana sai kuma tasa dariya har da shewa.

Kasancewar ba wata tafiya bane sosai yasa tsohuwa tafiya a ƙafa tana tafiya tana zancen zuci , tana isowa ƙofar gidan su likita ta gyara mayafinta tare dayin sallama , wata farar mata ce ta leƙo tace "sannu baba "bakinta na ɗauke da haƙorin makka wanda ya ƙara fito da kyawunta ,baba dake kiciniyar shiga ba tare data amsa sannun da ake mata ba yasa matae bata guri , sai da tsohuwa ta shige ta fara ƙwaɗa sallama ,sai da tayi sau biyu sanan taji muryar Alhajin gidan ya amsa , washe baki tsohuwa tayi kana tace "faɗi yazo dai-dai zama ayita ta ƙare "kallon rashin fahimta da hajiya da alhaji sukayi mata ,ita ko sai ɓaɓatun surutu take , ita bata shiga ɗaki ba ita bata nemi guri ta zauna ba sai magana take ,su kuma basu gane inda ta dosa ba , alhaji yace "tsohuwa bismillah sai yanzu na ganeki naga kin dawo ƴar caras ne "washe giɓib bakinta tsohuwa tayi kana ta kutsa kai zuwa cikin ɗakin Hajiya ma ta bita ,zama tsohuwa tayi a kan kujera tare da gaishe su ,bayan sun amsa tace "nazo akan maganar wanan ɗan naku likita waye ma sunansa ?tsohuwa ta fara kame-kame    sunansa "Zaiyyan" hajiya tace "a taƙaice , kuma washe baki tsohuwa tayi kana tace "dama nace "tunda yaga ƴar gurina wato jikata yace "yanaso sai ayi ƴar gida ai ko ?"cikin farinciki Hajiya tayi murmishi ta wuce kitchen ta ɗibowa tsohuwa dambun nama da lemun kwalba guda biyu ta ajiye gabanta , sai da tsohuwa ta gama shirya ƙarya da gaskiya sanan ta ɗauki kular da aka zuba mata    dambun nama ta riƙe ta kwashi lemon kwalba tace "Ramu zata kawo kayan "Alhaji ne yace "to hajiya kam sai binta da ido da tayi.

Tsohuwa na tafe tana sambatu tana cewa "dama ance idan arziƙi ya kiraka babu makawa sai ka samu ,yanzu gashi nayi samuwa dama Bashir ya daina ɗan siyomin gidan ma yamin yajin aiki ,tana tafe tana surutan ta har ta iso gida , sallama ta ƙwaɗa.  in kaji muryar tsohuwa sai ka rantse anyi mata bushara da aljannah ne , Ramu dake zaune a kan bishiyar gwaiba ta amsa tare da durowa ,kallon hannun tsohuwa tayi kana tace "sannu tsohuwa "yawwa ƴar albarka kinyi ƙoƙari gidan ya gyaru sosai gashi kinyi wanka kinyi fess kamar ba keba "murmishi Ramu tayi kana tace "ai saboda zan fara samari nayi " tsohuwa ta nemi guri ta zauna bayan ta ajiye kular hannunta da kwalaben lemu tace "yau fa samuwa mukayi "da sauri Ramu tazo ta buɗe kular , ganin dambun nama yasa ramu washe baki tace "wayo tsohuwa kin iya zuwa anguwa yasin ,nima barin kawo miki abin da na yi miki "tsohuwa dake hambuɗar dambun nama a baki tace "bari mu gama da wanan "tsohuwa da Ramu suka fara ci kamar kamun yunwa ,sai da suka cinye kowa ya ɗauki lemon kwalba ya kora .

Zuwa yamma abin da akaci ya zazzage tsohuwa tace "Ramumu mai kika dafa mana ? da sauri Ramu ta shiga kicin ta ɗauko kwano mai murfi ta shiga dashi ɗakin tare da direshi a gaban tsohuwa tace "gashi "bismillah tsohuwa tayi ta buɗe ,abin data gani ne yai matuƙar firgitata tace "....!

Afuwan fans ina matuƙar ƙaunarku daga grps grps ina ganin shar'inku insha Allah zanyi ƙoƙari inci gaba da faranta muku kamar yadda kuke kwararo min adu'a .

Pls kuyi following É—ina a wattpad momislam2020 sanan kumin vote a page sbda ganin cigaban labarin .

MOM ISLAM
[29/01, 10:11 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️
   
*NI DA   YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

Zainab Habib/Mom Islam

P 7-8
Chapter 6 · 0% Book details