← Book details Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan busar da iska Asaf ya yi daga cikin bakinsa kafin ya buɗe baki ya fara magana kamar haka "Wallahi Mom jiya ne da muka yi tafiya ko isowa in da zamu je ma ba mu yi ba motar mu ta lalace a wani Ƙauye...."

Kwashe komai ya yi ya gaya mu su daga haɗuwar su da Malam Iliyasu har da taimak'on Siyama da ya yi a lokacin da take son faɗuwan har da irin maganganun da 'ƴan Ƙauyen suka dinga yi,da kuma wanda Baba Siyama ya gaya mai,har da zuwan su wajan Malam Shuaibu da kuma irin wahalan da ya sha kafin ya rufe Aljanar Mazwara cikin kwalba.

Duk sai da ya gaya musu ba bu abunda ya boye mu su.

Bayan ya gama yi mu su ba ya nin komai ne ya É—ago ya dubi mahaifiyarsa ya ce "Mom kin ji dalilin da ya sa aka d'aura auren ba tare da an faÉ—a muku ba ke nan ",

"Ba dan komai ya sa na bari aka d'aura wannan auren jiya ba.sai dan irin son ganin na yi auren da kuke yi ",

Da a ce jiyan nan ba'a d'aura wannan auren ba. da tuni aljanar nan ta aure ni,kuma in ta aure ni _ni da aure har abadan ha ka Malam Shuaibu ya ce min ".

Ajiyar zuciya É—uk mutan palon suka s'auke

Hajiya ce ta yi magana kamar haka"Gaskiya abunda ka yi shi ne daidai,da a ce ba ka yi ha kan ba. da ba zan taɓa yafe maka ba Asaf ".

Lumsh ido Asaf ya yi ya buɗe ya dora su akan ƴaƴansa kuda ɓiyu

Su ma kai suka geÉ—a alamar sun gamsu sosai da maganarsa.

Kallon yayan mahaifinsa ma ya yi wa toh goggonsa ke nan,ita ma geÉ—a masa kai ta yi tana murmushi sannan ta ce "yarona abunda ka yi.ya yi daidai ".

Miƙewa ya yi ya je kusa da Auntynsa Zahra matar yayansa Mu'azzam ya zauna kusa da ita kana ya ce " Mom karama ke fa ?".

Murmushi ta sakar masa sannan ta É—ora hannunta samar kansa cewa "Haba Boy ai ni ko kowa bai amince ba ni zan amince saboda nafi kowa son ganin matarka kuma Alhamdulillah! na gani kuma na ji dad'i É—uk da ba haka na so auren ya kasan ce ba amma ba bu komai tun da lafiya aka d'aura an kuma raba ka da wannan muguwar Aljanar lafiya "

Tsaki duk suka ji an yi su na juyowa suka ga Aunty Jamilah ce ta yi,kafin su yi magana ta miƙe ta bar palon ta wuce bangarenta,suka bita da kallon mamaki.

Miƙewa ya yi ya je gaban akwatinsa ya kwantar da akwatin a hankali ya buɗe ya d'auƙo kwalbar da aka rufe Aljanar Mazwara a cikin wanda Malam Shuaibu ya kawo masa da daddare ya ce in ya koma gida ya samu wajen da ba wanda yake shiga a cikin sai family dinsu kawai ya samu waje mai kyau a ciki ya boye kwalbar .

Ya ce wa Malam Shuaibu mai zai hana shi ya ajiye kwanbar a wajan shi.ya ce a'a shi ba shi da wani mahalli mai kyau da zai ajiye mai a cikin dan in har ya ajiye zai samu yaran da za su buÉ—e kwalbar ku ma in an buÉ—e aiki zai dawo baya,

Juyowa ya yi ya kalle su ɗaya bayan ɗaya ya ce " " Kunganta gata nan ɗuk suka miƙe suka taho in da yake ido huɗu suka yi da Aljanar Mazwara cikin kwalba sai mutsu _mutsu take tana zazzare ido,cikin tsoro Mom ta kalli Asaf ta ce "Kaga Asaf ta shi ka je ka ɓoye ta a ɗak'in ma ajin kaya na musamman "." Da toh "Asaf ya amsa sannan ya maida kwalbar cikin akwatin ya rufe ya yi musu sallama ya wuce cikin.

Ya na barin wajan bai saya ko ina ba sai cikin É—ak'in ajiye kaya na musamman.

Waje na musamman ya nemo ya tire kwalbar daga cikin akwatin ya ɓoye.

Sannan ya juya ya fita daga cikin É—ak'in ya sa key ya kulle É—ak'in sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa.....

*Fulanin of Jajirtattu ce✍️*

Comments and share fisabilillah 👏
[20/09, 23:15] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫

Story and Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)

________________________________________________

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ

________________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________

*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

Paid Book ₦500

Free page1️⃣1️⃣

Bismillahi rahmani rahim

Sannan ya juya ya fita da ga cikin É—akin , ya sa key ya kulle É—akin, sannan ya ja akwatinsa ya bar wajan ya nufi part dinsa,

Yana zuwa part dinsa bai saya palo ba ya wuce É—aki darek,

Yana shiga ya ajiye akwatin gefen wardrobe d'insa ya shiga rage ƙananan kayan da ke jikinsa.

Bayan ya kammala rage kayan ne ya d'auki tawol ya d'aura ya wuce toilet,

Sai a lokacin na karewa É—akin kallo.

Komai na ɗak'in fari da gwalɗin ne,kama daga bed, wardrobe, dressing mirror, carpet ɗin da ke sakiyar dakin har ma da kujerar mai zaman mutun biƴun da ya saka a can gefe,ɗuk fari da gwalɗin ne,sai lamulayen ne ƙad'ai mai kala gwalɗin.

ÆŠakin ya haÉ—u iya haÉ—uwa,dan ita wardrobe din sakiyar sa ma glass ne.

Bayan na karewa ɗakin kallo na fita na ja masa ƙofa na wuce wajan su Siyama dan ganin me suke yi a cikin ɗakin baƙin da aka ba su😂

*Bangaren su Siyama da Goggo*

Bayan Sa'ade ta kai su wani haÉ—É—an wani É—akin baki mai masifar kyau ne ta nuna mu su komai har da toilet ta fita ta bar su.

Ɗakin d'auke yake da ƙananun gaɗo guda ɓiyu sai dan karamin wardrobe a sakiya

ÆŠakin ya yi kyau ba bu laifi,

Goggo ce tun da ta shigo É—akin take nuna k'auyenci,

Ta taɓa wannan ta taɓa wancan

Ni kam sai kawai nake girgiza wa.

Ɗuk da kuwa ni ma ina so na yi kallon amma in na yi za su raina ni tun yanzu shi ya sa na dage na haƙura

Baki na buÉ—e na ce "Haba Goggo mai haka dan Allah ki dena nuna wannan k'auyenci karki zubar min da mutunci tun yanzu,yanzu ma kina ganin ko kallo bamu ishi wa su ba.ba dan yellow na da kirki ba ma da tuni mun daÉ—e da barin gidan nan"

Na ƙare magana ina mai miƙawa daga kan gadon da nake zaune,na wuce toilet domin yin alwala dan Allah ma ya sani ba zan yi wanka yanzu ba.tun da ban daɗe da yi ba.

Har na buÉ—e kofar toilet zan shiga sai na ji Goggo na cewa" Mara kunya in ba ki yi haka ba ma baza'a gane Zainabu ce uwar....".Goggo ba ta karasa magana ba ta ji ina cewa"Goggo yi sauri ki zo ki ga wani abu ".Yana yin yan da na yi maganar ne ya sa Goggo saurin karasa in da nake kafin Goggo ta buÉ—e baki ta yi magana idonta ya sauka in da nake kallo.

Toilet ne mai kyau hadda su mirror da bahon wanka da dai sauran su.

Toilet din ya yi kyau ba laifi,

Goggo ce ta kalli Siyama ta ce "Wai Siyama anya wannan bayan gida ne kuwa ?"."Eh Goggo bayan gida ne,saboda na taɓa gani a wani film ni da Indo lokacin da mu ka je wannan gidan kallon ta unguwar mu ".

"Ki na nufin gidan kallon na Ado ?".

"Eh can nake nufi Goggo".

" Rannar zagayowa ranar haihuwata ce Baba ya ba ni É—ari biyar shine na d'auki Indo muka tafi gidan kallo aka saka mana film mai dad'i , a cikin film din ne aka nuno wata yarinya ta shiga toilet É—in ta hau wancan abun ".Ta faÉ—a tana nuna wa Goggo mats'ai

Kallon wajan Goggo ta yi ta ce " Ikon Allah !yanzu Siyama ki na nufin a nan zan hau in ina jin kashi?"."Kwarai kuwa Goggo tsaya ma ki ga na nuna miki".

Na faÉ—i ina shiga cikin toilet É—in,

Zama na yi akan mas'ai É—in.

Ina washe baƙi ,na ce " Goggo ha ka zaki dinga yi kin ga in kin gama sai ki ta shi ki ɗanna anan ".

Na faɗi ina saƙin ihu kamar mara hankali,

Saboda yana yin yan da na ji wannan abun da yake kore kashin dana taɓa yana ɗan yin kara.

Dariya Goggo ta saƙi tana tafa hannu,

"Yauwa Siyama fita toh da ma kashin nake ji "

"Kai Goggo wai ke ko kunya ma bakya ji ne ? Zaki din ga wani cewa kashi_ kashi dan Allah in wani ya shigo fah "

Goggo ba ta ce komai ba ta karasa cikin toilet din,ci kanta ban ce ba. na juya zan fita ban san ya aka yi hannuna ya taɓa wajan kunna famfon saman nan ba. kawai saukara na yi a kaina.

Goggo na ganin haka ta fashe da dariyan mugunta.

Ƙ'ok'arin kashe famfon nake amma na ƙasa,

Da yake ina da cutar limoniya ne ya sa bana son ruwa san yi ya taɓa mun jiki ko ka ɗan ballanta na a kai,

Shi ya sa ko a gida in na je wajan É—ibar ruwa da zarar na ga haÉ—ari a gari nake yin saurin komawa gida.

Numfashi na ne ya din ga yin sama da kasa.

Ya fito daga wanka kenan sai ya tuna da su,

"Kai shaf na manta wallahi ban gaya wa Sa'ade ta nuna musu yan da za su yi anfani da kayan toilet din ba.bari na yi sauri na saka jallabiya na je na nuna musu kafin na zo na É—an kwanta na wuta ".

Ya faɗa sannan ya yi saurin zuwa gaban wardrobe dinsa ya buɗe ya tiro milk din jallabiya mara n'auyi sosai ya riza ko wando bai saya sakawa ba ya yi bakin kofa ya bar dakin nasa ya wuce ɗak'in su baƙi,

Da yake dakin baƙin ba bu nesa yana kallon part d'insa shi ya sa bai wani jima ba ya karasa ɗak'in.
Chapter 8 · 0% Book details