← Book details Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Addu'ar da Malam yake d'azu ya ci gaba yana yi yana tofi a cikin kwalbar ne ya dawo tofa shi a jikin Mazwara

Ihu Aljanar Mazwara ta so ma yi tana dan kwanta wa a kasa kaÉ—an_ kaÉ—an har ta gama kwatar da duka jikinta akan tabarmar.

Sai da Malam Shuaib ya tabbatar ta kwanta rigingine sannan Malam ya yi anfani da wannan damar da ya samu ya kwantar da kwalban d'azu kan kwalbar na fuskantar kan Mazwara.

Sai ya ci gaba da addu'an da yake yi.

A hankali jikin Mazwara ta soma shigewa cikin kwalbar har ya zo ya shiga duka,

Sauri Malam Shuaibu ya yi ya dauƙo wannan jan Klellen ya sa ya d'aure bakin kwalbar da shi sosai ta yen da ba bu ta in da za ta samu damar fitowa.

ÆŠaga kwalbar ya yi yana hamdala.

Shi ma Malam Iliyasu Hamdalan ya yi,

Kallon su Asaf ya yi ya ce "Komai ya kammala yanzu za ku iya buÉ—e idanun ku".

BuÉ—ewa muka yi muna kallon Malam Shuaibu,

Asaf ne ya buÉ—e bakinsa ya ce "Malam tana ina ?"

Kwalbar da ke gefen sa ya nuna ma sa ya ce "Gata nan a cikin wannan kwalbar "

Kallon kwalbar Asaf ya yi sannan ya kalli Malam Shuaibu ya ce "Malam yanzu ba bu a bunda zai faru zan iya auren ?".

"Kwarai kuwa ÆŠana za ka iya auran ka ba tare da wata masa'ala ba"

Murmushi Asaf ya saƙi kana ya matse hannun Siyama da ke cikin nasa,

Ɗagowa ya yi ya kalle ni ya sakar min murmushi da tunda yake bai taɓa sakarwa wata Ƴa mace ba.bayan mahaifiyarsa da yen uwansa,

"Dan Allah yellow mutumin ka sakar min hannu "

Dariya Mus'ab da ke bayan su ya yi,

Juyowa Asaf ya yi ya kalli Mus'ab ya buÉ—e baki zai yi magana sai idonsa ya sauka akan fisarin da ya sula akan tabarma.

Ido Asaf ya zaro waje yana sakin murmushi,

Kallon in da Asaf yake kalla Mus'ab ya yi ya ga fisarin,ai ba shiri ya miƙe ya bar wajan.

Su Malam Iliyasu da Malam Shuaibu suka bisa da kallo su na sakin murmushi

KuÉ—aÉ—e masu yawa Asaf ya fito da shi daga cikin aljihun wandonsa ya ajiye a gaban Malam ya ce "Gashi Malam ayi sadaka da shi"

Kallon ƙuɗin Malam ya yi yana zare ido waje dan tunda yake bai taɓa ganin maƙodan ƙuɗi kamar wannan ba.

"A'a yaro wannan ya yi yawa ka rage"

"Eh gaskiya wannan ƙuɗin ya yi yawa Muhammad ka rage"Shima Malam Iliyasu ya yi maganar.

"A'a bai yi yawa ba,ba fa karamin taimako kuka yi min ba fa.da za ku ce wannan ƙuɗin ya yi yawa"

"Ni dai ayi sadaka da shi please "

Shi ke nan É—ana za'a yi kamar yanda ka ce."

Wata tsohuwar agogon da ya d'aura a hannunsa ya duba ya ga É—aya harda y'en mintuna

Dan haka ya kalle su ya ce"Ku tashi muje masallaci lokacin sallah ya yi "

Kai Asaf geɗa haɗe da miƙe suka yiwa Malam Shuaibu godiya suka bar gidan.

Umarni babana ya ba ni da na koma gida su bari su je sallah,na amsa da"Toh" Sannan na wuce gida

*Bayan awa biyar*

D'azu da aka idar da sallar la'asar ne aka d'aura auren Muhammad Zubairu tare da Siyama Iliyasu.

Zaune suke a cikin bukkan da aka s'auke su ya yi shiru,tun da aka d'aura auran jikinsa yake a sanyaye,ya resa murna yake ko kuma akasin haka.

Shi dai in an tambaye shi ba zai ce yana bakin cikin da auren ba.

Dafa sa ya ji anyi yana,ya É—ago ya ga Mus'ab ne

"Are you okay my friend?"

" I'm Okay "

"Me ka ga ni?"

"Ga ni nayi tun da muka dawo daga wajan d'aurin auren nan jikinka yake a sanyaye "

"Tunanin a bunda zan cewa Hajiya nake dan sauran in sun tambayeni na san amsar da zan ba su ".

" Karka damu na san in kayi wa Hajiya bayani za ta fahimce ka,tun da Na san Hajiya na da sauk'in kai sosai."

Da haka dai Mus'ab ya samu ya rarrashi Asaf suka ci gaba da hira kamar yanda suka sama in suna tare,

Banyan magriba mai gyaran mota ya dawo ya je ya duba mota ya ce shi bai ga in da motar ta samu masa'ala ba. asalima shi da ya kunna motar ya ga yana yi dan haka motar su ba ta lalace ba.

Mus'ab da Asaf ne suka fara mai masifa wai bai iya gyara ba shi ya sa ya ce motar su bai lalace ba.

Ganin ba fahimta za su yi bane ya sa Malam Iliyasu ya sallami mai gyaran mota ya tafi.

Kallon su ya yi ya ce su nitsu sosai zai mu su bayanin komai,

Shiru suka yi su na jiran su ji mai Malam Iliyasu zai gaya mu su

Bayani Malam Iliyasu ya fara mu su kamar haka "Ni ban yi mamakin da mai gyara ya ce motar ku bai lalace ba.saboda wannan Aljanar zai iya yi muku komai "

"Yanzu Baba kana nufin ita ce ta lalata mata mota ?".

Asaf ya tambaya

"Kwarai kuwa ita ce ta lala ta muku"

"Amma ba komai mu ta taimaka dan da a ce motar ku ba lala cewa tayi ba.da yanzu ba mu haÉ—u ba"

"Wannan gaskiya ne,da yanzu tana can a waje tana yiwa mutane abunda bai kamata ba"

Mus'ab ya yi maganar

Da haka dai suka wuce sallar i'sha, suna dawowa daga masallaci suka dan ci abinci,suka kwanta.

*Washe gari*

Tunda suka tashi da asubaha ba su koma ba.dan so suk'e kawai su gansu a gida.

Dan É—uk a takure suke anan,

*Bangaren Siyama*

Na haɗa komai na wa sannan mahaifina ya kira ƙanwarsa, watoh goggon na,akan cewa ta zo ta raka ni in ya so shi ya zo daga baya,ta amsa da toh.

Dan kuÉ—in da Malam yake da shi ne ya tattara duka ya bawa goggo Asabe ya ce in sun je can ta siyo min kafida da kwanuka da tukwane da zan dinga anfani da shi kafin ya karo min wasu ,ta karba ta amsa da "Toh ",

Ai Asaf na jin haka ya amshi ƙuɗin ya mayar wa Malam Iliyasu ya kara da cewa "Komai mu na da shi Baba ba sai ka siyo mata komai ba"

Baba ya buÉ—e baki zai yi magana Mus'ab ya karbi zancen da cewa "Da gaske kwai komai Baba karka samu damuwa".

"Shi ke nan Allah ya yi muku albarka ya kuma baku zaman lafiya" Suka amsa da "Ameen"

Har baƙin mota Malam Iliyasu ya raka su,

Muta nan Ƙauye ma ba'a barsu a baya ba,dan kuwa suma sun zo su ba wa idanun su abinci.

Rungume mahaifina na yi ina kuka.

Shafa kaina Baba ya yi cikin sanyin murya ya ce"Haba Siyama ba fa rabuwa muka yi ba.zan dinga zuwa ina kawo miki ziyara kema in an kwana ɓiyu za ki kawo min ziyara ".

Da haka dai Baba ya samu ya rarrashe ni na haƙura,

Bayan motar da Mus'ab ya buÉ—e mun ne na shiga ya rufe kuma dama ita goggo ta riga da ta shiga tun tuni,saboda goggo akwai ta da son mota Kamar me.

Tada motar Mus'ab ya yi suka ɗagowa Malam hannu ya ja suka bar Ƙauyen.

Karfe goma na safe suka isa kofar gidan su Asaf,

Home Mus'ab ya yi mai gadi ya wangele mu su gate ya cilla hancin motar cikin gidan.

Kallon kallo muka shiga yi, ni da goggo,har aka yi parking,

Shanye mamakin na nayi na fito daga cikin motar

Ita ma goggo fitowa ta yi tana zazzare ido.

Muje suka ji Asaf ya faÉ—a

Soma tafiya suka fara yi har suka karasa bakin kofar,

Danna kararawar ya yi ba bu jimawa aka zo aka buÉ—e kofar suka yi ido huÉ—u da.......

*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*

Comment's and share fisabilillah 👏
Chapter 14 · 0% Book details