← Book details Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mom na shiga ya miƙe ya nufi ɗayan dakin domin yin wankan tsarkin da bai samu ya yi ba tun ɗazu,dan ya ma manta shaf da maganar wanka tun lokacin da ya ga Siyama a wannan yana yin Sai yanzu abun ya faɗo masa.

Mom tana shiga ta tarar da Siyama kwance akan gado ,bacci har ta fara daukarta,ta ji shigowar mutun zumbur ta _tashi daga kwancen da take.

" Sannu ƴata ". Mom ta faɗi tana karasa baƙin gadon ta zauna ,

"Yauwa sannu Hajiya ".

Ni ma na faÉ—i cikin jin kunya,

*Bayan awa É—aya*

Bayan Mom ta gama yi min dinki ne ta miƙe ta nufi inda Asaf yake ajiye magungunan sa ta buɗe ta duba min paracetamol da ibuprofen ta kawo min da ruwa na sha,

Bayan na kammala sha ta karbi glass cup din ta ajiye sannan ta kalle ni ta ce "Yauwa ƴata Allah ya kara sauƙi ni zan tafi sai na dawo da safe mai kike so a faɗa miki ?".

Cikin jin kunya na ce "A'a Hajiya ni bana son komai,bai kamata a matsayinki na babba na saki girgi ba,ni ce ma ya kama a ce na yi miki girki ba ke ba ".

Ƴata ke nan ba ni ce zan yi ba wannan yarinyar da ta kai ku ɗakin bakin nan ne take yi,dan haka ki faɗi abunda kike so a dafa miki?".

Shiru na yi kamar ba zan ce komai ba.tuna wa da na yi da wannan girkin da na gani wata Æ´ar burni ta dafa a cikin film din da na gani rannan ne ya sa na É—ago da sauri ina cewa "Yauwa Hajiya akwai wani abinci da na ga wata Æ´ar burni ta yi a TV rannan shi nake so a dafa min ".

Dan murmusha wa Hajiya Rukayya ta yi kana ta matso kusa da ni ta ce"Toh ya sunan abincin Æ´ata?".

Jin Mom ta tambaye ni sunan abincin ne ya sa jikina yin sanyi,dan kuwa ko za'a kashe ni ba zan iya cewa ga sunan
abincin ba.

Fahimtar hakan da Mom ta yi ne ya sa ta cewa "É—an kwatanta min yan da aka faÉ—a abincin sai ayi miki ".

Jin abunda Mom ta kara faÉ—i ne , ya sa ni sakin murmushin jin dad'i har dimple dina ta lotsa,

Kallon ta Mom ta saya yi,dan ba karamin burgeta ta yi ba.komai nata abun burge wa ne,gashi cikin sanyi take yin komai.

ÆŠuk da a kauye ta fito amma in ba ta yi magana ba_ ba za ka taba cewa a kauye ta fito ba.

Saboda kwata_ kwata bata yi kama da su ba.

Kwantan ce na yiwa Mom tun kafin na karasa kwantacen ma ta gane jolof din shinkafa ce da kwaisilo da pepe ciki nake nufi .

Dan haka ta ce in sha Allah za'a dafa min,

Godiya na yi mata da kuma sai da safe ta juya ta bar É—akin.

Tana fita ta samu Asaf a palo yana gengeɗi sai da ta ɗan buga gafen kujeran sannan ya buɗe ido haɗe da miƙa wa ya ce "Mom kin gama ?".

"Eh na gama ".

"Saura ka kara yaga Æ´ar muta ne kaga abunda zan maka ". Tana kaiwa nan bata saya jiran mai zai ce ba ta bar É—akin .

Da kallo ya bita har ta bar palon,key ya je ya saka wa kofar sannan ya juya ya nufi bedroom,

Yana shiga ya tarar da ita tana addu'ar bacci karasowa ya yi ya z'auna ya kura mata ido yana kallon wannan É—an karamin bakin nan nata dake É—an motsa wa kaÉ—an_ kaÉ—an saboda karatun da take yi.

Har ta gama ta shafa.

Ta zame zata kwanta ya riƙo hannunta ya hana ta kwanciyar,

Baki sake nake kallon sa ina jiran in ji mai zai ce,dan in dai wannan abun yake so ya kara min yanzu zan fada mai ihu.

"Ni baki shafa min addu'an ba my heartbeat "?.

"Toh bacci zaka yi ne kai ma ?".

"Eh bacci zan yi bari ma ki ga ni ".Ya yi maganar haÉ—e da zame wa ya kwant gadon ya ja pillow ya É—ora kansa akai.

Ban ce mai komai ba,na fara addu'a bayan na gama na shafa masa na,na zira kafafuna da niyar sauka daga kan gado sai ya juya da sauri ya kalle ni, ya shiga tambayata ina zan je ?

"Zan je na kwanta kan kujera ne".

Na ba shi amsa ina koƙarin sauka,

Hannuna ya ja na faÉ—a kansa na kwanta,ina
faÉ—in washhhhh!

"Ya dai meye faru".

"Dinki na mana ka ja ni da karfi fa ".

Na faÉ—a a shogobe

Abun ba karamin burge Asaf ya yi ba,

Kara rungumeta ya yi ya ce"Sorry ki yi hakuri toh kin ji?".

Kai na_ nageda na yi kamar zan mike ya maida ni na kwanta,
A haka dai na hakura na kwanta har bacci ya dauke mu daga ni har shi ba tare da mun sani ba.

*Washe gari*

Kamar yanda É—abiyarsa yake in zai yi tafiya ba ya iya cin abinci haka yau ma ta ka san ce,dan ba abunda ya ci,ya yi mun sallama akan cewa zai koma wajan Malam Shuaibu ya faÉ—a masa abunda yake faruwa,

Da na ji kauyen mu zai je sai na ji kamar na bi shi saboda a iya kwana É—aya da na yi sai na ji gaba É—aya ina kewar Babana,

Bayan mugana sallama ya je wajan iyayensa ma ya yi mu su sallama ya hau mota ya wuce kauye,dan wannan karon shi ƙad'ai ya tafi bai tafi da kowa ba.

*Kauyen masanawa*

Ba karamin mamaki Malam Iliyasu ya yi ba da yaga Asaf a gidan sa yau,

Amma ya shanye mamakin sa ya yi mai sannu da zuwa,

Bayan sun gaisa Baban Siyama ya kawo masa fura ya dan sha ne, yake faÉ—a mai dalilin zuwan sa yau,da kuma abunda ya faru da kwalba,

Shiru Malam Iliyasu ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Cikin sanyin murya Asaf ya shiga tambarsa Lafiya ya yi shiru ko akwai matsala ne ?

Gyara zama Malam Iliyasu ya yi kana ya ce "ÆŠana ka yi hakuri da abunda zan gaya maka.......

Toh masu karatu mai Malam Iliyasu (mahaufin Siyama)zai gayawa Asaf 🤔kar fa ace akwai matsala 😱

Mu haÉ—u a sabon group,dan jin ya zata kasan ce Kuma me ya faru?

*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*

Comments and share fisabilillah 👏 mutanan amana 🥰
[04/10, 17:28] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹💫

Story and Written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)

________________________________________________

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ

________________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________________________________

*Diamond 💎Star 🌟 Ladies* 🧝‍♀️
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

Paid Book ₦500

Free page9️⃣

Bismillahi rahmani rahim

ÆŠuk fito wa suka yi har da ni, ni kam ba karamin tashin hankali na shiga ba da jin wannan maganar Aljanar.

*Bayan mintuna 9*

Zaune suke a gaban wani Babban Malamin garin da É—uk garin ba bu kamar sa dan shi yake tire mu su irin su Aljanu da É—uk abunda ya shafi jinnu.

Tunda su Malam Iliyasu suka zo yake kallon Asaf ko giftawa ba ya yi.

Ɓangaren Asaf kuwa ba karamin haushi kallon da Malam yake masa ya ba shi ba.dan shi mutun ne da ya tsani kallo a rayuwarsa

Sai da ya kalle shi sosai sannan ya ɗauke idonsa ya juya ya dubi Malam Iliyasu "Ya ce gaskiya kun kyauta da kuka zo akan lokaci,da ba ku zo yau ba.da shi ke nan ba zai taɓa yin aure ba har karshen rayuwarsa amma tun da kun zo in sha Allah yanzu zamu fara aiki "

Malam Shuaibu ya faÉ—a yana É—auko wata katuwar kwalba da wani jan kelle ya ajiye a gabansa.ya sake kallon Malam Iliyasu ya ce"Yauwa kowa ya nitsu zamu fara aiki ".

ÆŠuk nitsuwa suka yi, ya d'auko wata alkur'ani ya buÉ—e ya ajiye shi a gabansa ya buÉ—e wannan kwalbar da ya É—auko É—azu "ya kara kallon Malam ya ce"Tare da ita za'a daura mu su auren ko?.Kai Malam Iliyasu ya geÉ—a mishi alamar "Eh".

"Okay ku matso nan kusa da ni"

Matsowa Asaf da ni muka yi gaban Malam,hannun Asaf Malam ya kamo ya haÉ—a da na nawa ya haÉ—a hannayen waje É—aya sannan ya zare nashi hannun ya bar iya namu,

Wani yarrr! ÆŠuk muka ji,
Hanun namu da yake a haÉ—e Asaf ya matse sannan ya É—ago ya kalleta ni,
Yana kallonna muna haɗa ido na yi saurin k'auda nawa gefe kana na shiga zare hannunna daga cikin nasa amma na kasa dan ba karamin riƙo ya yi wa hannunna ba.

Wani zare ne Malam ya d'auko ya d'aura ma na a hannu,sannan ya ce "Kowa ya rufe ido kuma ko mai muka ji karmu kuskusa mu buÉ—e idanunmu"

Da "Toh muka amsa sannan É—ukan mu _mu biÆ´un muka rufe ido,amma banda Malam Iliyasu da Mus'ab, tunÉ—a su abun bai shafe su ba.

Addu'a Malam Shuaibu ya fara yi ya na yi ya na tofi a cikin kwalbar da ke gabansa,yana kiran sunan Aljanar Mazwara,

Bai fi mintuna biƴar da fara addu'ar ba ɗak'in ya fara ba da wani irin sauti mara dad'i, jikin Mus'ab ne ya d'auki ƙerma,
Haka ma bangaren mu ni da Asaf .

Malam Iliyasu kam ko a jikinsa,dan a bunda yafi wannan ma ya gani .
Tunda ya saba kawo mutane a wajan sa,

Sai da Aljanar Mazwara ta gama yin dariya kafin daga visani ta bayyana a gaban Malam Shuaibu.

Wani irin murmushi Malam Shuaibu da Malam Iliyasu suka yi mai sauti amma banda Mus'ab da ya tsorata sosai,dan zuwa wannan lokacin har ma da fisari ya yi,dan tu ni wandonsa ya gama jikewa da fisari.

Mikewa ya yi da zumbar barin wajan sai Malam Iliyasu ya gansa nuni ya yi masa da ido da ya koma ya zauna,ba bu shiri ya koma ya zauna.
ba tare da ransa ya so ba.
Ya yi ne ka wai saboda zaman lafiya,

Ni da Asaf kam jin shiru ba mu kara jin dariyar ba ne yasa hankalinmu ya kwanta
Chapter 13 · 0% Book details