← Book details Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata karasa magana ba ta ga dreve ya saƙi stearing mota kamar ana tura motar ya zo ya bugi wata katuwar bishiyar da ke gaban su ji ka ke dummm! Lokaci duni Aliya ta daɗe da suma,ihuu sosai Hanifa ta saki cikin tashin hankali ta shiga jijjiga Aliya amma shiru bata farfaɗo ba,cikin tashin hankali ta fita daga cikin motar tana sarce gumin dake siyayo mata akan goshi kamar wanda ya yi guɗu,sai data gama sarce gumin dake kan goshinta saf sannun ta gyara d'aurin dankwalin ture ka ga tsiya da ta ɗaura ya dawo gefe tukun kafin ta tire waya a jakarta ta dannawa Maman Aliya kira bugu biyu aka ɗ'auka,bata saya gaisheta kamar yan da ta saba in ta kira ta ba kawai kai saye ta ce "Mommy! Aliya Mommy! Aliya".Ta faɗa tana sakin kuka,cikin tashin hankali Maman Aliya ta shiga tambayarta a abun da ya samu Aliya "Me ya samu Aliyata Hanifa"."Mommy Aliya ta...ta..ta mutu"Haifa ta kare maganar ta na sakin kuka "Whatttt! Karki gaya min maganar banza Hanifa yanzu Aliyata tabar gidan nan taya zaki ce min ta rasu"Wallahi Mama da gaske nake Aljana ta kashe mana Aliya da dreve Mommy sai dana bawa Aliya shawara akan ta hakura da Asaf amma taƙi"."Kin ga Hanifa ki faɗa min yanzu kuna ina Aliyata ba za ta mutu ba,dan wallahi ba'a haifi Aljanan da zata kashe min ƴa ba".

Kwatance Hanifa tayi wa Maman Aliya, Maman Aliya bata karasa jin kwatancen ba ta kashe wayan cikin sauri ta É—auki mayafinta da key din motarta ta yi waje,cikin tashin hankali ta shiga mota dreve ya buÉ—e mata gate haÉ—e da yi mata Allah kiyaye amma ta yi ban za dashi ta ja motar a guje ta bar gidan,da kallon mamaki drave ya bi motar da shi

Tafiya da zai kaita a mintuna talatin ne ya kaita a yer mintuna da bai wuce goma sha biyar ba.

Tana karasa wajan ta hango mutane,bata saya dai _dai ta parking motarta ba ta fito daga ciki ta nufi wajan da mutanan suke saye,ta na zuwa ta chusa kanta cikin su wani irin ihu ta kurma da karfi a lokacin da idanuwanta suka sauka akan Æ´arta dake kwance a kasa ga mayafinta data yafa akan wuyarta Hanifa ce durkushe a gabanta ta na ku ka ta riko hannunta sai kiran sunanta take amma shiru bata motsa ba.

Kara sowa Maman Aliya ta yi cikin tashin hankali ta durkusa ita ma gefen Hanifa ta shiga jijjiga yar tata "My love ki tashi karki min haka amma still shiru Aliya bata motsa ba.

Wani irin ku ka mai suma zuciya ta saki ta daga kan Aliya ta dora kan cinyarta taci baga da kiran sunanta amma shiru

Daya daga cikin mutanan da suke zagaye a wajan ne ya yi magana "Hajiya ki yi haƙura Allah ya yi mata rasuwa ba za ta tashi"....Bai karasa magana ba yaji saukar mari a kan kuncinsa dafa wajan ya yi ya ɗago ya zubawa Maman Aliya idanu,ita ma Maman Aliya shi take kallo sai a lokacin ma taga ashe ma shi ɗin likita ne ma ashe

"Hajiya taya daga faÉ—ar gaskiya zaki mare ni"

Likita ya yi magana cikin ɓacin rai

"Taya zaka ce ƴata ta mutu bayan tana nan da ranta"daya daga cikin mutanan ne ya amshi zancen da cewa "Haba_haba Hajiya ina ki ka taba ganin likita ya yi karya akan mutuwa?in bata mutu ba taya zai ce ta mutu mai ta yi mana da zamu yi mata karyan mutuwa?a ina muka santa da har zamu yi mata karya"Maman Aliya bata ce komai ba ta juya ta sugun na ta ciccibo Aliya daƙer ta kalli Hanifa tace zo muje mu kaita a sibiti bata mutu ba suma ta yi"hawaye Hanifa ta share ta na murmushi haɗe da cewa"da gaske bata mutu ba Mommy?".Mtsiiii Maman Aliya ta ja tsaki kana ta ce"Ban sani ba karki zo mu tafi ki zauna"ta na kaiwa nan ta rasa ta cikin mutanan ta bar wajan,bin bayanta Hanifa ta yi da sauri,ta na zuwa wajan mota ta buɗe mata murfin motar Maman Aliya ta saka Aliya a bayan mota ta rufe,ta koma gaban mota ta shiga mazaunin dreva Hanifa kuma ta shiga dayan site din ta fisgi motarta karfi suka bar wurin

*Gidan su Asaf*

Sun zauna sun jira Aliya shiru bata zo ba har Asaf ya fita ya koma wajan aiki,da farko dai sun hana shi sai daga baya da suka ga lokaci na tafiya ba su ga Aliya ba gashi kuma sun kikkira wayan Aliya bata dauka ba,ya sa suka bar shi ya tafi

Kallon Zahra Hajiya Zainab ta yi kana ta ce "Zahra kara gwada number din mugani ko Allah zai sa a daga wayan".Da"Toh"Zahra ta amsa sannun ta kara dannawa Aliya kira amma shiru ba'a dauka ba sai a kiran ta biyu aka dauka

"Hello"Hanifa ta furta da dishashiyar muryarta data gama dishewa da kuka

Cikin sauri Zahra ta ce "Aliya lafiya na ga har yan zu baku zo ba?" "Ba ita bace ba Hanifa ce.
Ikon Allah!toh ina take Hanifa?"Kamar Hanifa zata yi shiru sai kuma wani abu ta ce mata yi magana Hanifa

"Allah ya yi mata rasuwa Aljanar jikin danku ta kashe min kawata da nafi so a duniya hankalinku ya kwanta bu....bata karasa maganar da na ke yi ba aka fusgi wayan da ke hannunta dago wa ta yi taga Maman Aliya ce saye gabanta idonta ya yi jajur saboda kukan data sha.

"Hello yauwa bari ku ji wallahi idan Æ´ata ta mutu sai na yi sharia da ku ta na kaiwa nan kitt ta katse kiran,

"Mommy! Ya jikin Aliyan? Ta farfaɗo ne ?" Hanifa ta tambaya,baki Maman Aliya ta buɗe da niyar bawa Hanifa amsa sai suka ji muryar likita a bayan su,duk juyo wa suka yi suka buɗe baki a tare suka shiga tambayar likitan "Likita ta farfaɗo ne ? Shiru likita ya yi na ɗan wani lokaci kana ya ce "Ku yi haƙuri Hajiya tun da na shiga na ɗubata na tarar Allah ya yi mata rasuwa kuma da dukkan alamun sun nuna cewa ta sha wahala sosai kafin ta rasu kuma ku san minti talatin ta yi da rasuwa dan ba yanzu ta rasu ba".

Wani irin ihu Maman Aliya ta kurma kana ta ce"Wallahi Karya ne wallahi basu isa ba wallahi ba zan yedda ba sai sun dawo min da Æ´ata dan su ne silar komai su suka kashe min Æ´ata"ta na kaiwa nan fuuu tabar wajan kamar za ta tashi sama ta yi bakin kofar fita a sibitin sai data kai bakin kofar sannun ta juya ta kalli Hanifa da jajayen idanunta ta ce "Hanifa ki zauna da ita bari na je na dawo"Ta na kaiwa nan bata saya jiran mai Hanifa zata ce ba ta karasa fita.

Kai kwai likita ya girgiza sannan ya juya ya bar wajan ya wuce offince dinsa,ita kuma Hanifa ta wuce dakin da Aliya take.

Cikin tsoro na ke guɗu ƙare na bina a baya ban saya ko ina ba sai a gaban wani dan karamin kofa turo kofar na yi da sauri naci karo da wani dattijo da alama fita zai yi da guɗu na karasa na buya a bayansa ina ɗan leko da kaina kaɗan dan gani in karen"Siyama laifiya kika shigo mana gida ba bu ko sallama?".Ba tare data yi magana ba ta nuna mai karen da ke gabansa da hannunta,sai a lokacin Babban ya lura da karen da ke gaban nashi kansa ya girgiza yana murmushi kana ya ce "Haba Diyana wai yaushe zaki yi girma ne ?" Mai ma kon ta bawa Baban amsa sai ma kara riƙe shi data yi,ba tare da Baban ya yi magana ba ya shiga koran karen,babu jimawa karen ya tafi sai a lokacin yar buduwar ta fito daga bayan mahaifinta...

Kuyi haƙuri da wannan jiya na dawo na gaji

Comments and share fisabilillah 👏😍

*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*
[22/08, 16:23] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫 MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹 💫

Story and written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)

__________________________________________________

Suivre la chaîne Sakeena Isma'il Cameroon Hausa Novel's 📚✍️ WhatsApp Channel sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029VaklQ3uLNSa36AqAX01V

__________________________________________________

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ

__________________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

__________________________________________________

*Diamond💎 Star⭐ Ladies🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

Paid Book₦500

Free page 3️⃣

Bismillahi rahmani rahim

Ba bu jimawa karen ya tafi sai a lokacin 'yar buduwar da a shekaru ba za ta haura 16 ba. fitowa ta yi da ga bayan mahaifin na ta,sai a lokacin na kare mata kallo sosai, kyakkyawa ce ajin karshe,ta na da dogon fuska da kuma dogon hanci sai dan karamin bakinta dake d'auke da Pink din lips sai zara zaran gashin ido da kuma ta gira,ba ta da wani haske sosai,dan kuwa ba za'a kira ta da fara ba.ba za kuma a kira ta da baƙa ba.irin kalan farar nan nata ne ake kira da wankan tarwaɗa.

Siririya ce amma ba sosai ba ,ta na da books da kuma hips sosai,idan aka ganta zaka d'auka ta yi shekara 20 nan kuwa 16 ne kawai saboda har tsayi ma ta na da ita ma sha Allah!

Kallon mahaifina na yi ina murmushi haÉ—e da turo baki gaba kana ganin yanda nake yi kaga yarinta a tattare da ni

"Siyama ina ruwan da ka ɗebo?".Ware manya _manyan idanuna na yi waje dan sai a lokacin na tuna da abun ɗiba ruwa na dana yer a hanya saboda karen daya biyo ni,bakina na buɗe na ce "Laa!wallahi Baba ruwan ya ɓare a hanya"."Toh da ki ka barar da ruwan ina botiƙin ya ke?"Wallahi harda shi na bari a hanya na dawo gida saboda wannan karen"."Wai ni Siyama yau ki ka fara ganin kare ne?"."A'a Baba ni fah bana tsoron kare kawai dai idon karen ne ya bani tsoro saboda tunda na ke ban taɓa ganin idon kare green ba sai yau ga kuma wani irin kallo da ya ke min shi ya sa na ji tsoro na guɗu shi kuma ya biyo ni ".
Chapter 2 · 0% Book details